← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 152

Sashe 94

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dare Yayi yanzu, kada mu katse ma wani baccin shi, shawarar da zan bada shine a ɗebo ruwa a yayyafa mata in sha Allah zata farka, zuwa asuba sai a kira malamin da zai dubata” mai gemu ne Yayi maganar, muryar Alhaji ubaid a sanyaye yace”Inaso zan kira Dr shureim ne, saboda a irin wannan lokacin baya runtsawa Idonshi biyu Yana tashi domin Yin nafilfilin dare” ya ambaci hakan tare da Danna wayar hannunshi ya buga ma dr shureim Kira ta soma ringing.

Kallon zainab Hajiya layla tayi idanuwanta sun kaɗa jawur tace”ɗauko mun ruwa a fridge “ amsa mata zainab tayi da toh, da sauri ta nufi hanyar kitchen.

Dafe kai Hajiya layla tayi da hannu ɗaya, Sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, ta manta da yanayin jikinta, don ma babu wanda ke acikin natsuwar shi, hankalinsu na akan Benazir.

Bayan zainab ta dawo, hannunta ruƙe da bottle water me sanyi ta buɗe murfin ta miƙa ma Hajiya layla, Yayyafa mata tayi saman fuskarta, nan take ta sauke nannauyar ajiyar zuciyata muryarta da tsiwa take fadin”ina mahaifiyata Ina mahaifina! Ina mijina da ƴata Ina yayana shureim, suna ina ! Na shiga uku na bani na lalace Na rasa kowa nawa, wayyo Allahna na shiga Uku wallahi gida zan koma Nabar Yarinyata cikin Jini, tajuddeen kai na bama amanar ɗiyata nasan bazaka bari rayuwarta ta wulaƙanta ba. Dan Allah ka bani Ƴata ita nake son gani’

tunda ta fara sambatun nan zainab da hajiya layla suka fashe da kuka suna kallonta, ta runtse idanuwanta sai faman ciccije le6enta take Yi da haƙoranta tuni suka soma faffashewa, jini Ya soma tsastsafowa, dunƙule hannu tayi tana buge buge, da sauri zainab da hajiya layla suke rurruƙeta sosai suna ambaton sunanta

*DR.SHUREIM❤*

Lokacin da Kiran Alhaji Ubaid ya shigo wayarshi, Yana a zaune saman darduma cikin shiga ta larabawa, Yayi nisa acikin karatun qur’nin dayake yi Kiran Ya daki dodon kunnanshi, Hakanan yaji gabanshi Na faduwa, aranshi ya ayyana kowa ne ne ke kiranshi a tsakar daren na! ya salam, Sai da yakai ƙarshen Aya tukunna Ya zabura Ya miƙe Ya nufi wayar dake ajiye saman side drawer ya ɗauke ta yana duban Screen din, Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba ganin sunan Abie dinsa Ya bayyana, kafin Ya ɗaga kiran saida Ya fara kallon agogon bango ƙarfe ɗaya da rabi na dare, picking call ɗin ya yi muryarshi na rawa ya furta”Assalamu alaikum Daddy!!!” muryar Alhaji ubaid Babu natsuwa Ya furta mashi”shureim Ƴar uwarka ta dawo gida daren nan cikin mawuyacin hali”! Da alamun ruɗu akan fuskar dr shureim Yace”bangane wa kake nufi ba daddy” muryar shi da sauti mai ƙarfi Yace”BENAZIR!! nake nufi ta dawo gida cikin daren Nan, Gatanan kwance tana buge buge zufa duk ta wanke jikinta, mun rasa ya zamuyi da ita”

Zafafan Hawaye ne suka wanke fuskar dr. shureim, tsabar farin ciki baisan sa’adda Ya zube saman gwiwowinsa Yayi sujjada, sosai ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, Alhaji Ubaid Yana jiyo sautin kukan dr shureim Kamar ƙaramin Yaro.

“Shureim ba kuka yakamata kayi ba, dan Allah ka natsu muyi magana, hankalin mu ba’a kwance Yake ba, Ƴar uwarka bata acikin Hayyacinta, Mai gemu ya tabbatar min da cewa Kurciya ne akayi mata, saboda alamomin dake a jikinta na fitar sihirine”

Jin wannan maganar ta Mahaifin nasa ne yasa shi saurin ɗagowa daga sujjadar, arab turban dinsa tuni ya warware Yabar saman kanshi.

Manna wayar yai saman kunnanshi da alamun kiɗima ya furta”Sihiri kuma!!
Alhaji ubaid Yace”to haka dai mai gemu Ya faɗa mana, baka ga yadda jikinta ke fitar da gumi ba kamar wadda aka tsamo daga kogon ruwa, bari na kanga maka wayar kaji haukan da take Yi mana” on the other hand Alhaji Ubaid Ya matsa gaban benazir Ya saita wayar abakinta.

Muryarya ce ta ratsa kunnuwan dr shureim”Ni ku sake ni, Ku ƙyaleni ku daina ruƙe mun hannuna, wurin Mijina zanje nabar mashi ƴata a gida ita nake son gani, wallahi ku rabu dani dole in tafi” Jikin taƙaura yai la’asar, a sukwane Dr shureim ya miƙe tsaye da waya kare a kunnanshi.

Muryarshi na rawa Ya furta”daddy najima ina zargin hakan, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, wallahi da ina da halin da zan Iya zuwa Jos acikin daren nan da babu abun da zai hana inzo don in cece rayuwar ƴar uwata, amma duk da haka daga nan ɗin ma zan Iya taimakawa, Daddy Idan Aunty zainab tana akusa ka miƙa mata wayar!”

Jikin Alhaji ubaid na 6ari ya miƙa ma zainab Wayar yace ta kar6a dr shureim ne ke son Yin magana da ita, da sauri ta sanya hannu ta kar6i wayar tana fadin”dr shureim kaga wani ikon Allah ko? Tsawon shekara goma sha shidda Yau benazir ta dawo gida, wlh tsabar farin ciki bansan inda zan tsoma kaina ba, sai dai na damu da yanayin da take aciki”

Numfasawa dr shureim Yai tare da cewa a tsanake”Aunty zainab, yanzu bani da natsuwa, zuwa gobe da sassafe zan shigo Jos din, amma kafin nan ki duba ɗakina a cikin drawer chest na bedside drawer gida na uku, akwai robobin ruwan zam zam da wani malamin mu na ƙasar egyp ya bamu su don mu dinga yin amfani da su muna taimakon mutanan da suke fama da matsalar sihiri, ki ɗauki ɗaya Kije ki buɗe bakin benazir Ki matsa mata shi ki tabbar ta shanye shi duka in sha Allah, sauran sihirin dake ajikinta zai barta ne kafin goben mu ƙaraso” amsa mashi tayi da toh, yace ta miƙa ma mahaifiyarshi wayar da sauri ta miƙa mata, yatsun hannun layla na kerma ta kar6i wayar.

Cikin shessheƙar kuka tace”shureim benazir ɗinmu ta dawo gida, sai dai kamar bata acikin hayyacinta, duk ta faffasa la66anta da haƙoranta.

Cikin kwantar da murya dr shureim Yace”Ki sanya handsfree Inason daddy yaji maganar da zanyi” da sauri layla ta mayar da wayar handsfree, zainab tuni ta shige ɗakin dr shureim neman ruwan zam zam.

“Mommy daddy, dan Allah ku kwantar da hankalinku, wallahi Allah ne ya taimaki rayuwar baiwar Allah nan Ya Karya sihirin dake a jikinta, kuma ya dawo mana da ita da ranta, wani mugun aka samu mara imani mai zuciya irin ta kafuran farko Yai silar rabata da danginta tsawon shekara goma sha shidda, wallahi tun lokacin dana ji yanayin da benazir ta gudu tabar gida raina ya bani cewar wani abunne Ya faru da ita, haƙiƙa munyi sakaci wurin kula da ita, gaba ɗaya mun ɗaura mata lafin guduwarta babu wanda ya ta6a yi mata kyakkyawan zato akan meyasa ta gudu tabar jinjira acikin kwamin wanka, Kuma bata nemi kowa ba ta kama hanya tayi tafiyarta, anyi amfani da halayanta na rashin jin magana da rashin Kunya da take dashi anyi mata abun da yasa tabar mu saboda ansan kowa zai yi tsammanin ita ta gudu dakanta tunda dama bata jin magana, da ya ke Allah ba azzulumin bawansa bane sai gashi ya dawo mana da ita a lokacin da bamuyi tsammanin ganin ta ba” gaba ɗaya sun natsu suna sauraron muryar dr.shureim, hatta security officers din gidan duk suna sauraron shi ga dukkan alamu suna gamsuwa da bayananshi duba da yadda suke gyaɗa kawunansu.

“Banaso wani daga cikinku Ya tambayeta meyasa ta tafi, ko kuce zakuyi mata faɗa dan Allah kada kuyi mata hakan, Kuma kada ku faɗa mata abun da ya faru da mijinta da ƴarta, naji tana ambaton sunansu, ku sanar da ita cewa suna nan kuma zaku haɗata da su idan ta kwantar da hankalinta, idan ba haka ba zata Iya zaucewa idan taji cewa babu su”

Kamar malami da ɗalibansa haka shureim keyi masu magana suna amsa mashi da toh.

“Zuwa da safe kafin mu ƙaraso, a kira likitan gidanmu Ya duba lafiyarta,” suka amsa mashi da toh.

“Mommy idan zainab ta bata ruwan zam zam din, in dai bacci bai ɗauke ta ba, ki taimaka mata tayi wanka taci abinci, idan kuma tayi bacci ku ƙyale ta kada ku takura mata” layla ta amsa mashi da toh.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruƙe da robar zam zam ta ƙara so gaban sofa din da benazir ke akwance tana sambatu, muryarta harta disashe fuskarta ta kumbura suntum.

Zuƙunnawa tayi agaban sofa din, ta cizge murfin robar, da sauri Alhaji ubaid ya rurruƙe mata hannuwan Benazir, daƙyar ta Iya buɗe bakinta ta kafa mata ruwan zam zam din ya dinga shiga cikin ƙaramin bakinta, gaba ɗaya ta shanye ruwan, ko mintuna biyar ba’ayi ba da bata ruwan bacci mai nauyi ya ɗauketa, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zufar jikinta tuni ta soma daskarewa, addu’o’i zainab ta dinga karantowa cikin harshen larabci tana tottofa mata saman fuskarta da jikinta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma iyayenta ba, tuni layla tayi sallama da dr shureim ta miƙa ma Alhaji ubaid wayarshi ya sanya hannu Ya kar6a ya tura a aljihun jallabiyarshi, security office din dake atsaye bakin ƙofar falon suka yi masu sallama da niyar gobe da safe zasu dawo duba jikin benazir, Alhaji ubaid yai masu godiya kafin suka fice daga falon.

Hajiya layla ta dubi zainab kije ki kwanta mun gode sosai, dan Allah gobe da a suba ki shirya mata lafiyayyan breakfast din da zata ci” amsa mata tayi da toh, ta mike ta nufi room dinta, ya rage saura Alhaji ubaid da Hajiya layla a falon, kallon juna sukayi lamarin Ya girgiza su, abun daya ɗaure masu kai wanene yayi masu wannan muguwar aika aikar!!!
Atare suka ɗaura idanuwansu kan benazir tsantsar sonta da ƙaunarta ne Ya kamasu, Har cikin zuciyarsu basu ji daɗin ƙaddarar data afka mata ba, tayi matuƙar basu tausayi ganin irin mayuwacin halin da take aciki, fatansu Allah Ya toni asirin baƙin azzulim daya yi silar barinta gida!!! yadda suka ga Rana haka suka ga dare, babu wanda Ya runtsa acikin zukatan nan guda huɗu, Hajiya layla da Alhaji ubaid, Dr shureim da Zainab, akan kunnuwansu aka fara kiran sallar asubahi!!!!
Chapter 94 · 0% Book details