Sashe 82
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shafa sumar kanta dr Laura tayi”Kada ki damu yana daga cikin aikin mu!, Yanzu ki shiga kiyi wanka, Mintuna ƙalilan suka rage maku,” amsa mata tayi da toh, Bayan fitar dr Laura, Angel ta nufi Jakar Kayan, zuciyarta a hautsine ta girgiza da jin wacece matar da aka damƙa ma amanarsu, ita babban abunda ta ke jima fargaba garkuwarsu, tunawa da lokacin da aka kawo masu unaiza a kurkuku, yarinyar ta ruɗe shi da big boobs dinta, balle kuma matar da taji ance tana tafiya da imanin namiji saboda dirin jikinta, tashin hankalin da ba’a sanya mashi date. (🤣)
Har ta fara Imagining abun da zai faru, a gidan da zasu zaune atare da ita, tayi tunanin sun samu sauƙine komawarsu Nigeria ashe akwai sauran rina akaba.
A hankali ta ruko hannun jakar Kayan, ta zaro kayan dake acikinta, wata haɗaɗɗiyar A-line gown ce launin red colour mai round neck ƴar ubansu awurin haɗuwa, Rigar tayi mata kyau a ido, sai faman jujjuyata take yi, aranta tana ayyana yau wata rana zata sanya kaya na mutunci wanda ba uniform din prison ba, wannan abun farin ciki ne agare ta.
Bayan ta gama kallon rigar, ta ɗaurata saman mattress, ta zaro kwalin takalman dake a cikin jakar tare da kwalin sabuwar wayar da dr laura ta siya mata, ƙirar iphone 15 pro, Takalman kuma Ankle strap ne masu tsini launin black, hada face mask da mayafi aka basu wanda bakowa bane Ya tsara hakan face chief na Isod, Lokacin da dr laura ta bukaci zata siya masu kaya Sai da aka nemi izininshi, yace ya amince bisa sharaɗin idan zasu sanya kayan a haɗa masu da Niƙab ko face mask da zasu rufe fuskokinsu, a ƙalla ta shafe tsawon mintuna biyar tana kallon kayan, bakomai yafi burgeta ba face wayar da aka bata kyauta, tunawa da lokaci yasa tayi saurin nufar toilet ta shige ciki, shaf shaf tayi wanka kafin fitowarta, Nurse jessica ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da gift kit ƙaramin akwati na kayan shafa, ta ɗaura shi gefen gadon Angel, ta zauna saman kujera tana Jiran fiowarta, bayan ta fito daga wankan, suka gaisa da nurse din cikin girmamawa, daga bisani tayi mata bayani game da care kit din data kawo mata donta gyara jikinta, godiya Angel tayi mata bayan ta ɗauki kayan shafar da rigar ta juya ta nufi toilet dasu saboda jin kunyar kada aganta tana sanya kaya, murmushi nurse jessica tayi yayin da take binta da kallo.
Bayan ta shafe ko’ina na jikinta da body oil mai tsadar gaske, skin dinta har glowing take yi, rigar tayi bala’en yi mata kyau, duk da bata da jiki tana da tsawo, white in red abun ba’a magana, lokacin da ta fito daga cikin toilet ɗin, ita kanta nurse din sai santin kyan Angel take Yi, daga saman rigar ta tsuke daga ƙasanta bazace daga ta jujjuya rigar take bubbuɗewa kamar ana hura mata iska, bayan ta kammala shiryawa nurse ta feshe mata jikinta da turaren desired destiny, fragrance din turaren mai daɗin shaƙa a hanci.
Face mask din da ta sanya black colour ne launin takalmanta, har saman karan hancinta mask din ya haura, Gray eyes dinta ne kaɗai suka Bayyana.
Ɗaura Mayafin rigar tayi asaman kanta tayi rolling dinsa, gyalen yana da tsayi ba laifi, Har saman gwiwar hannayenta yakai mata, shima launin takalmanta ne.
“Kin yi kyau masoyiya Angel, sai ki ka yi mini kama da Cinderella saboda rashin ƙibarki,” Ƙayataccen murmushine kwance saman fuskarta,
“Na lura kin ƙosa ki bar ƙasar nan, Ni kuma gashi bana son ki tafi, saboda na saba da ke masoyiya Angel,” cikin sanyin murya Nurse jessy tayi maganar tana duban fuskarta.
“Dr. laura ta bani kyautar waya, kuma ta faɗa min akwai phone numbers din ku aciki, zan dinga kiranku akai akai muna gaisawa saboda ni kaina bana son mu rabu don ya zamar mana dole ne mu tafi” Sai da tayi maganar Nurse jessica ta wurga eye balls dinta kan kwalin wayar, zaro ido ta ɗanyi haɗi da cewa”wow, gaskiya dr. Laura tana Ji da ke shalelenta, wannan waya haka mai kyau da tsada, Ina taya ki murna masoyiya Angel, Kuma naji dadi da ta baki wayar, Kinga zamu dinga kiran juna muna gaisawa, harma muyi video call” fuskarta dauke da matsanancin farin ciki, ta nufi gefen gadon ta ɗauki kwalin wayar a hannunta, tana ƙare mashi kallo, Angel dai sai murmushi take saki, bakinta yaƙi rufuwa kamar ta fasa ihu Haka take ji tsabar murnar yau zasu Bar america zuwa ƙasarta ta gado.
“Yakamata mu tafi masoyiya Angel, Ƴan uwanki suna Jiranki a waje” cike da ƙagara Angel ta amsa mata da toh, shaf shaf ta zura takalman a ƙafarta masha Allah, wankan Angel yabi jiki.
A hannu ta ruƙe wayar bayan ta curo ta daga kwalin, atare suka fito daga ɗakin.
Tun kafin ta ɗago da idonta, Muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta”Genie gamu nan ki dube mu da kyau, mun yi kyau” Da sauri ta wurga idonta kansu, masha Allah har saida gabanta Ya faɗi tsabar kiɗima da ganin Kyawun da suka Yi acikin sabbin kayansu, jemimah da azeeza launin gown dinsu Royal blue ne, hannah da parveen launin punch pink, Ita kuma Batul launi ɗayane dana Angel, red colour, kowaccensu akwai Face mask a fuskarta, Anyi masu rolling Veil a saman kawunansu, takalman kafarsu flat ne ba kalar nata ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallon mamakin Kyawun da suka Yi, mutun ɗaya ne ke babu a cikinsu, Mazan su huɗune, kowannansu ya kimtsa cikin shiga ta mutunci ta kece raini wato shigar hadaddun Slim fit suit, sun manna mask a fuskokinsu, kwantacciyar sumar kawunansu ta kwanta luf, ƙafafuwansu na sanye cikin tsadaddun takalman fata, ta ko’ina ƙamshin turarensu ne ya karaɗe ward din da suke.
Ganin tayi tsaye tana kallonsu bata motsa ba, yasa kowan nan su sanya hannu a lokaci ɗaya suka Zame mask din dake a saman fuskokin su, sai faman washe mata baki suke yi, wani irin farin ciki ne Mara misaltuwa ya kamata, tun daga kan yadda suke shaƙar iskar ƴan ci zaka tabbatar da kwanciyar hankali da natsuwa atattare da su, su kansu sun yaba da kyawunsu, sai faman shafa kayan jikinsu suke Kamar zasu lashesu.
Jemimah ce ta ruƙo hannun Azeeza suka watso da gudu zuwa gabanta, Atare suka fada saman jikinta, Hugging dinta su ka yi suna tiƙar dariyar murna, tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, ko a mafarki bata ta6a tsammanin zata ga wannan ranar ba, yau gata ga ƴan uwanta cikin shiga ta alfarma ba uniform din kurkuku ƙaddara ba.
A hankali Batul da sauran ƴan uwan nasu suka nufo wurin Angel, ɗaya bayan daya take rungumo su saman chest dinta, suna matuƙar ƙaunar junansu, nurses da likitocin dake tsaitsaye cirko curko sai kallonsu suke yi gwanin ban sha’awa.
“Angel, Kinga yadda ki kayi kyau? Rigar nan tayi maki kyau, wlh duk munyi kyau,” Batul ce tayi maganar tana shafa gaban rigarta da hannunta.
“Nayi tunanin abinci kaɗaine abu mafi kyau a duniyar nan, ashe sutura ma abu ne mai ƙayatarwa, gaskiya bazan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Daɗi Nake ji kamar In buga tsalle sama in dira ƙasa,” Parveen ce tayi maganar, sautin dariyarsu yacika ko’ina, kasancewar suna Yin firar cikin harshen hausa babu wanda ya fahimci abunda suke tattaunawa a tsakaninsu, sai dai Abi la66ansu da kallo.
“Ban ta6a ganin kalar kayan nan ba, Mun saba da Uniform kala daya na prison, Yau sai gashi mun tsinci kanmu acikin sutura mai kyan gaske, godiya ta tabbata ga Allah, domin kuwa shine silar komai, dama kin ta6a fada mana cewa mahaƙurci mawadaci, sannan duk tsanani Yana tare da sauƙi, kuma babu yanayi na rayuwa da yake kasancewa Na dundundun, Yau mun shaida hakan Angel” tun da Haris Ya fara magana Suka natsu suna kallonshi, tamkar ba mara lafiyan nan ba, Jikinshi Yayi kyau ɗan black beauty da shi, Kalamanshi sun tunama Angel deeja, Yarinyar akwai tawakkali duk da bata da zurfin ilmin addinin musulci tayi imani da Allah, fiye da wani musulmin daya taso acikin musulunci, tunawa da deeja ne yasa ƙwallar idonta suka soma gangarowa saman kuncinta, a fakaice ta sanya hannu ta share su, haƙiƙa taji zafin mutuwarsu, ga salsabeel daya tsaya mata aranta, bawan Allah ko awani hali yake ayanzu? Ya rayu ko ya mutu? Allah masani!.
“Angel, Ina fata Yanzu hankalinki ya kwanta, babu sauran damuwa tun da yau zamu koma Nigeria” Gabriel ne yai mata maganar Haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bata ba, Javed yace”ni fa duk atakure nake jin kaina, mutanan nan sai kallon mu suke Yi,”
Naufal Yace”ka gode ma Allah tun da ba Giants din kurkukun ƙaddara bane suke kallon ka,” gaba daya suka sanya dariya cikin nishaɗi.
Gabriel yace “kyau suke kallo, wankan da muka ɗauka ne Ya burgesu, mu kanmu mun burge kanmu balle kuma su”
Hanna tace”Wannan abun da aka sanya mana a fuska yafi komai 6ata min rai, Duk ya toshe mun ƙofofin hancina, wai ba yadda za’ai mu tafi batare da mun sanya shi ba”? Tana faman yamutsa fuska tayi tambayar tana kallon Fuskar Angel.
Kafin tayi yunƙurin bata amsa Gabriel ya riga ta cewa”saboda tsaro, shiyasa aka bamu shi don mu sanya, sunanshi face mask,” Javed Yace”ai na gane shi, kalar wanda tsohuwa zafreen take sanyawa ne” harara parveen ta ɗan jefa mashi”Ni bana so kuna maganar matar nan, na tsaneta kamar mutuwa ta”
“Ina danish yake ne? Shi bai fito ba ne”? Angel tayi tambayar tana leƙen ƙofar room dinsa.
Haris yace”Suna can ɗakin shi suna ta fama dashi akan ya sanya kayanshi yaƙiya, kinsan mutumin da taurin kai kamar ƙashin nama, bansan Ya suka ƙare da shi ba, Har lalla6a shi nayi na nuna mashi kayan dake a jikina amma yasa kafiya akan bazai sanya ba”
Mai hali bazai ta6a canzawa ba, aranta ta ayyana hakan, Kallon su azeeza tayi”our twins ku sakar min rigata, zanje ɗakin danish”
Azeeza tace”toh, mu tafi atare zamu biki” Ruƙo hannayensu tayi a cikin nata, suka nufi ɗakin Danish, Su Haris ma suka bi Bayansu, har sun kusa shiga Muryar dr laura ta katse masu hanzarinsu.