← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 152

Sashe 10

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ban faɗi hakan don na fama maki ciwon da ke acikin zuciyarki ba, Nasan kina yi ne duk don ki cece rayuwan ƴan uwan ki, don kuma ki cika mana alƙawarin da ki ka ɗaukar mana, sai dai kash gaggawar da ki ka yi ta yi silar jefa rayukan mu cikin haɗari, Zai yi wuya mu tsira sai dai bazan bari Ki rasa ran ki ba, Zan yi maku ƙoƙari Ayau ɗin nan ku fuce daga cikin kurkukun nan kafin Hankalin Matsafan ya dawo kanku, Mun ci sa’a shuwagabannin kurkukun basu aciki, Sauran da suka rage Giant ne masu haɗarin gaske, Ni kaina da na ke da sihiri a jikina bazan Iya ja dasu ba, A yanzu haka da nake Yin magana da ke nayi ƙoƙarin Sarrafa ɗakin Da ke ɗauke da madubin tsafin su shiyasa ba zasu Iya ganin mu ba, Nan da Awa ɗaya Zamu Aiwatar da komai Idan har lokacin nan ya cika kuna acikin kurkukun nan mu dukan mu zamu Mutu bayan azabtarwa da zasu Mana.”

Baiwar Allah duk da raɗaɗin da bakinta ke yi mata ahaka ta daure ta cije ta soma Yi mashi magana muryarta araunace daƙyar sautin ma yake fita

“Sun cire min uniform ɗina, Ruwan zamzam din Yana a cikin aljihun wandona bansan Ya zanyi ba” cikin ƙunar rai ta ambaci hakan

“Zanje na ɗauko maki Uniform ɗin ki, cikin minti ɗaya” Yana ambaton hakan ya 6ace ma ganinta.

Yunƙurawa ta yi daƙyar ta miƙe zaune, Ƙarnin Jinin jikinta ya addabi hancinta, bargon da ke shimfiɗe saman gadon ta janyo ta yafa ma jikinta, Zuciyarta acunkushe take da damuwar halin da ƴan uwanta su ke a ciki, Ita ba ta damu da kanta ba, sune damuwarta. Fatanta Allah yasa tsohuwa zafreen bata cutar dasu ba kamar yarda ta faɗa mata.

Durowa Cikin ɗakin salsabeel Yayi hannu shi ruƙe da uniform ɗinta, Jar vest ɗinta da wandon ta Ya miƙa mata su, yatsun hannayen ta na kerma ta kar6e su, Agaban shi ta zura kayan bayan ta kammala sanya su ta zaro ƴar ƙaramar robar zamzam daga cikin aljihun wandonta, Idanuwanta acike tab da ƙwala ta kalle shi tare da cewa”Ta ya ya zan Iya ganin Danish har in bashi ruwan zam zam ɗin”?

“Bamu da isasshen lokaci, A saman bayana zan goya ki in kai ki inda Ya ke kuma zan taimaka maki mu bashi ruwan, ya kai ƙarshen maganar tare da Juya mata baya ya zuƙunna daga bakin gadon, matsowa ta yi tare da kama bayan shi ta haye, Ya yunƙura Ya miƙe, Daga inda ya ke goye da ita Ya 6ace 6att....

Ba su dura a ko’ina ba sai A wani katafaren Ɗaki mai tsawo da faɗi komai na cikin shi launin Ja ne, hatta dogayen labulayen da ke a kewaye dashi red colour ne. wani irin sanyi ne ke ratsa sassan Jiki acikin ɗaki kamar sanyin A.c, daga gani special room ne na kurkukun ƙaddara, Tsadaddun furniture ɗin da ke a cikin ɗakin kaɗai abun kallo ne.

Jin shiru bata motsa daga saman bayan shi ba yasa shi yi mata magana muryarshi cikin raɗa ya furta” Mun ƙaraso, Ki tashi ki ga ɗan uwanki” yanayin yadda ya yi mata maganar ne yasa taji gabanta Faɗuwa shi kanshi Salsabeel ɗin A tsorace Ya ke da abunda zai Biyo baya balle ita kuma da ta ke Ƴar ƙwaruwa wadda bata taka kara ta karya ba. Tsoro ya hana ta ɗago ta kalli inda Danish ɗin Ya ke duk irin kewar shi da ta yi, Sosai ta runtse idanuwanta Hannayenta ƙanƙame da Salsabeel.

“Na faɗa maki bamu da isasshen lokaci ki sauka mana” yai maganar tare da zuƙunnawa don ta sauka, Kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai jiki na kerma ta sauko daga saman bayanshi, sai lokacin ta samu damar Ware idanuwanta sosai Tana ƙarewa ɗakin kallo tun daga kan labulayen dake a cikin shi har zuwa kan shimfiɗaɗen Carpet ɗin dake a ƙasa Ga wani ƙayataccen table mai ɗauke da Dinner set, plate ta gani na tangaran mai ɗauke da kayan marmari, ga wani apple da aka datsi saman shi, hada sawun haƙoran mutun, Ga wani glass cup mai ɗauke da wani abu acikinsa ruwane amma launin shi yayi bright red kamar an surkashi da wani abu. Duk fa wannan kalle kalle da ta ke yi ba ta yi tozali da shi ba, saboda ta hana idonta kaiwa gare shi, Har sai da Sabsabeel yai mata gyaran murya tukunna ta soma Juyar da ƙwayar idanuwanta a hankali ta ɗaura su kan katafaren king sized bed ɗin da ke kafe a cikin ɗakin, Gado ne irin na sarakuna launin shi Golden Colour an shimfiɗe shi da lallausan Bedsheet launin Ja, slowly ta sauke idonta akan dogayen ƙafafuwanshi wa’iya zubilla tsabar ruɗu yasa ta dabarbarce saboda ta kasa yadda cewa shine, Halittar Jikin shi gaba ɗaya ta canza, Ya zama jibgegen ƙato, Samun Namiji mai irin ƙirar ƙarfin shi zaiyi wuya, ƙira ce mai matuƙar tsoratarwa, rikitarwa da kuma jan hankali, Ga dukkan alamu bacci ya ke yi a giant ɗin ma bai bar halin shi na yin bacci ba, Dogon wandone Baƙi A jikin shi, Sai Jar t shirt ta matse jikin shi, ta bayyana ainihin surar shi, musamman damtsen hannayen shi tamkar zasu fasa rigar saboda tsabar ƙarfi.

Sun canza shi sosai Farar fatar wuyan shi hada zanen tattoo launin baƙi da Ja wanda ya kasance Tambarin kurkukun ƙaddara ne duk wani Giant yana da Zanan a wuyan shi, sun rage mashi tsayin sumar kanshi, Anyi mashi kitson zane guda shida, wutsiyar kitson ta sauka har saman Broad-shoulders ɗin shi, Ya koma kamar ƴan iskan turawan nan, waɗanda tun daga suffarsu zaka shaida cewa, ba bu Ɗigon Imani A zuciyar su.

Zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta a yayin da ta ke ƙare mashi kallo, Ta gaza yarda da abunda idanuwanta su ke Nuna mata, Wai Danish ɗinta ne Ya koma haka? Hankalin shi kwance ya ke sharar bacci babu alamun damuwa atattare da shi, duk irin kewar shi da ta yi shi baisan ma da zaman ta ba balle sauran ƴan uwan shi, saboda zalunci na mutanan nan sun rabasu da ɗan uwansu.

Cikin shessheƙar Kuka Ta furta Sunan shi”Da..Nish..” walking nervously ta nufi bakin gadon ta zauna daga gefe tana ƙare mashi kallo, Ya yi wani irin haske mai kyan gaske, tsabar kyan fuskarshi tamkar zai kashe mata ido, la66ansa sun yi jawur dasu kamar na Jinjiri, Dogon hancin shi ya tafi tsaye ba lanƙwasa, kwarin idon shi ta zuba ma ido, dogayen eye lashes dinshi masu kyau da tsari.

“Don’t waste Our time! Mintuna kaɗan suka rage mana,” Muryar Salsabeel ce ta fargar da ita, Ji ta ke kamar ta faɗa mashi ta rungume shi a jikinta ko ta samu sassauci a cikin zuciyarta.

Matsawa kusa da ita sabsabeel yai “Ki buɗe murfin robar, Ni zan hau saman gadon In ruƙe shi gudun kada ya farka ya ham6are ki, naushin giant yana da haɗari sosai Bugu ɗaya su ke Yiwa mutun ya mutu In ba wani iko na Allah ba’ Wannan maganar da ya yi ta ɗaga mata hankali, ta ƙara jin tsoron shi.

Yatsun hannunta na kerma ta soma ƙoƙarin buɗe murfin, tana dab da zata Ƙarasa cire shi, Kamar An ce ta kalli fuskarshi taga ƙwayar idon shi na motsi ta saman kwarin idon shi, da ƙarfi ta furta”Ya farka”

Sautin miryarta ne ya daki dodon kunnanshi, Aiko kamar an zungure shi Ya ware manyan idanuwanshi launin russet brown akan fuskarta, wani irin ƙwar jini yai mata a furguce Ta miƙe daga gefen gadon Tana ja da baya, idanuwanta azazzare, Salsabeel da ke yunƙurin ruƙe kafaɗun shi don Ya hana shi miƙewa A zafafe Yai wurgi dashi tun daga saman gadon Ya ƙundumo ƙasa Ji ka ke tummm, Hankalin Angel fa ya ƙara tashi ganin yarda ya jefar da babban mutun kamar Salsabeel yadda kasan kallon tamola haka ya jefar dashi wanda a haife salsabeel zai Iya haifarshi, Durowa yai daga saman gadon Yana huci Kamar mayunwacin zaki, breast ɗin shi har motsi su Ke yi, Wani matsiyacin kallo da taga yana binta dashi yasa ta haɗiyi yawu mai zafin gaske, kallon da Danish ke yi mata kamar ma baisan wace ce ita ba, Tunkararta Ya soma yi Yana gurnani har wani jijjiga jikin shi ya ke yi, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada Ya rikiɗa Ya canza halitta don ta fahimci abinda ya ke shirin Yi kenan, Juyawa ta yi da gudu tana neman inda zata 6oye kanta don kada ya cimmata, saida ta gama shan wahalar kewaye ɗakin Kwatsam taga Ya bayyana agabanta. Ɗagowa ta yi a tsananin tsorace ta ke kallon shi tana girgiza mashi kai haɗi da marairaice mashi fuska don Yaji tausayin ta amma ina ai ko kallo arziƙi bata ishe shi ba, Muryar Salsabeel ce ta karaɗe kunnuwanta a kausasace ya ke bata Umarnin ta gudu daga gabanshi kada ta bari ya Damƙe ta.

kafin ta yi yunƙurin Canza hanya Cikin rashin sa’a ta ji Ya damƙi qugunta Kamar ɗiyar roba Ya ɗaga ta sama Muddin kuwa Ya bugata da kasa sai qugunta Ya 6alle saboda ƙarfin dake gare shi bana Mutun bane na baƙin shaiɗanin aljani ne, Yana ƙoƙari makata Da ƙasa Salsabeel ya cimma shi Gaba ɗaya yai wurgi da ita ƙasa ta kife robar zamzam ɗin da ke a hannunta tuni ta gangara ƙarƙashin table ɗin da ke a ɗakin gashi murfinta ya fara zamewa zai cire saboda buɗeshin da ta fara Yi, ruwan da bai wuce Kur6a ɗaya ba Ya kare idan ya zube shikenan sun rasa damar da su ke da ita.
Chapter 10 · 0% Book details