Sashe 25
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsastsaye su ke a Cikin Katafaren Kitchen ɗin gidan mai girman gaske, A shaƙe ya ke da kayan Amfani, ko’ina a tsaftacensa ya ke tamkar ba amfani su ke yi da shi ba, aiki su ke yi tuƙuri babu kama hannun yaro, Matasan Ƴan mata da manyan su, wasu suna aikin wanke nama wasu suna yanke yanken kayan lambu agaban cutting board, yayin da wasu su ke agaban manyan gass cooker suna kula da girkin da suka ɗaura, akwai waɗanda ke a tsaye in front of kitchen microwave suna aiki.
Ƙamshin girkinsu ya karaɗe ko’ina tun daga cikin kitchen ɗin har izuwa Babban falon gidan.
Babbar macace ta shigo kitchen ɗin domin duba masu aikin don ganin yadda komai ke gudana, A ƙalla za ta kai shekara 40 a duniya, Ta kasance ɗaya daga cikin Masu yi masu hidima a gidan, ita ce head maids shugaban ma’aikatan Cikin gidan, Macace mai yawan fara’a ga son mutane, ma’abociya son Shigar fararen Kaya, A yanzu haka pakistan ne a jikinta riga da wando farare ƙal anyi masu adon duwatsu launi daban daban, ƙafarta na sanye cikin flat shoes, bakowa bace wannan face *DIVYA* ba’indiyace amma sunfi kiranta da *HAJJATY* tun da ta shigo kitchen ɗin masu aikin suka fahimci itace tazo dubasu nan fa suka ƙara dage damtse suna aiki duk don su ku6uta daga faɗanta.
A hankali ta ke zagaye Kitchen ɗin, Hannayenta a goye saman ƙirjinta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, na ɗan wani lokaci kafin tayi masu gyaran murya, kusan atare su ka ɗago suna kallonta, Hannu ta tafa masu
“Aikin ku yana kyau, You ladies Are doing a fantastic job, everything smells delious, i’m sure ɗanɗanon girkin zaiyi daɗi kamar yadda ƙamshinsa ya ke da daɗin shaƙa, Ina ƙara jinjina ma ku,” ta ƙarasa yi masu maganar tare da ɗaga masu babban yatsan hannunta na dama alamar Jinjina.
Murmushi ne Ya bayyana akan fuskokin su, ba ƙaramin daɗi suke ji ba, Idan hajjati ta yabe su, suna matuƙar sonta kuma suna girmamata saboda kyawun halayanta da ɗabi’unta.
“Dame dame aka kammala ne”? ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu, Abla ce ta soma Yi mata jawabi
“Kebab with chips, Beef shawarma, burger and pancakes,...” kusan abu goma ta lissafa mata, Jinjina kai Hajjaty ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa”Kada na katse maku aikin ku, lokaci Yana ƙurewa, Ku hanzata ku kammala, “
“An aikawa Hajiya saratu Breakfast ɗinta!”? da sauri Safa tace”yanzu nake shirin zuwa in kai mata, Nice nike duty part ɗinta” Gyaɗa kai Hajjaty ta yi.
“Okey, shirya min fresh fruit ki haɗa min da kakkauran tea,” Wadda aka kira da Sarah ta amsa mata da toh, ba tare da 6ara lokaci ba ta shirya mata kayan marmari a cikin ƙayataccen wooden tray, tare da cup of tea, ta miƙa mata hannu biyu tasa ta kar6i tray din tare da juyawa ta fuce.
Bayan fitarta, Fira ta 6arke a tsakaninsu
“Safa ashe ke ce kike duty a part ɗin Aunty jarabatu zaki sha Masifa, “ Abla ce tai mata maganar, murmushi suka saki, sophia tace”Ai hajiya saratu ba daga baya ba, In dai wurin Iya masifane, Last time fa da naje kai mata abinci cewa ta yi wai na gutsiri ƙafar kaza, hada cewa ita bata yarda damu ba, wama ya sani ko mun saka mata guba acikin abinci donta ci ta mutu,” dariya suka saka
“Tana da wuyar sha’ani bata yarda da kowa ba, In ba wannan Mijin nata ba, Uban son banza suruki da zaman gidan surukai Ko kunya babu” sophia ce tai maganar, Safa tace”Ai koni na samu wurin zama agidan nan abunda zanyi kenan, waman taraka bati siddan, shiyasa a kullum nake roƙon Allah ya bani bugun zuciyar family ɗin, Wlh idan na Aure shi nadaina sakin baki ina bacci, nafilfili zanta yi akan Allah ya dawwamar da auran mu don nasan maƙiya da mahassada ba zasu bar mu mu zauna lafiya ba, Musamman Mahaifiyarshi uwar Ji da izza, kinga matar nan bata ɗaukar raini batason Mu’amala da bare....” tun da ta fara zuba suke binta da kallon rainin wayau saida takai aya tukunna Abla tace”you don’t ave sense, Dama najima da zargin kwakwalwarki ba dai dai take aiki ba, Ko Jazz da muka raina wlh yafi ƙarfinki, Ni kaina ba zance bana son Owais ba, amma ance abunda yafi ƙarfinka ka haɗa shi da baka so” kwa6e fuska Safa tai”kiyi min fatan alkhairi kawai, Nima a hausa novels ni ke jin irin hakan na faruwa, mafi yawanci zaki ga ƴar aiki ta auri ɗan masu gida, wani sa’in ma mai gidan ta ke aurewa....” sautin dariyarsu ne Ya hana ta ƙarasa maganar, suna fira suna aiki,
“Safa kina atare da wahala, in dai ko zaki cigaba da tunanin zaki samu abunda ki ke so kamar yarda ki ke karantawa ahausa novels, Ni Bance baya faruwa ba amma Allah a zamanin da mu ke ciki zaiyi wuya, mai kuɗi sai ƴar mai kuɗi, talaka sai ɗan talaka, Ina jiye maki tsoron heart attack ya kama ki silar son wanda bai son Kina yi ba, a ƙarshe ki ƙare a emergency room”
Dariya suka saki gaba ɗayan su, kwata kwata firar da suke yi bata ɗauke masu hankali daga yin aikin su ba, manyan cikin su ne kadai basa magana sai dai idan sun faɗi abunda ya basu dariya su ɗan murmusa.
“Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa, duk irin tarin dukiyar nan ace Iya mutun goma sha biyar ne ke da gadonsu” Abla ce tai maganar.
Abla tace”Nikaina abun na damu na, Yana yi mun ciwo a zuciya, na rasa gane meyasa basa son haihuwa, daga mai ƴa’ƴa biyu sai mai ƴa’ƴa uku, Allah ya hore masu wadatar arziƙi sai ƴa’ƴa ne zasu gagare su? Abun na ƙona mun rai, komai nasu na rayuwar turai, Mu da zasu taimaka su Aure mu, duk bayan ƴan watanni zamu dinga sakar masu ƴa’ƴa tuni zamu cika famiy ɗin”
Maganar Abla ba ƙaramin dariya ta basu ba, Sofiya tace”Sannu kaza suma ai suna son ƴa’ƴan, sannan bada son ransu bane ba su haihuwa, Ƙaddarar su ce ta zo masu ahaka, naji labari a bakin Hajjaty saboda tafi mu daɗewa a gidan, Suna haihuwa amma ƴa’ƴan basu zuwa da rai, A mace ake haihuwarsu yawanci da zarar sun yi haihuwar fari da ta biyu zaiyi wuya kiga sauran sun rayu a matattu su ke haihuwarsu, Allah ni tausayi suke bani, Musamman prime minister Hateem shifa Bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, shi da matarshi Gimbiya mujeedat, ƴa’ƴa biyu duka mata, rashin haihuwarsu ba ƙaramin gi6i yai masu ba arayuwarsu, Ki duba fa hateem shine yafi kowa arziƙi a family ɗinsu daga shi sai sharafudeen,” mamakine akan fuskar Wasu daga cikinsu waɗanda basu daɗe da fara aiki ba
“Abun da ɗaure kai, Kuma an duba lafiyarsu? Ko dai wata lalurar ce da suka gada tun kaka da kakanni”?
“Ko ɗaya, Tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje an bincika lafiyar kowan nan su, Ba su da wata matsala da ta shafi ƙwayoyin haihuwarsu, lafiyar su ƙalau, har manyan malaman addini saida kakansu ya sanya don su bincika mashi meke faruwa a zuri’arshi, Sakamakon ɗaya ne dana asibiti, basu da wata lalura,”
Jikin su duk yai sanyi, Basu ta6a sanin zancen haihuwar da matansu keyi yara suna zuwa ba rai ba sai yau da sophia ta sanar da su.
“Allah mun tuba ka yafe mana, shiyasa akace zato zunibi koda ya kasance gaskiya, Gulma ba ta yi rana ba, Mune kullum tsegumin mu akan suna yin irin rayuwar turai ba su son haihuwa ashe ba laifin su bane, jarabtace daga Allah” murya asanyaye Safa Tayi maganar.
Abla tace “Na tausaya masu, kuma In sha Allah zamu ta ya su da addu’a, akan Allah ya yaye masu lalurar da ke damun su” shiru suka ɗanyi Na wani lokaci, daga bisani Safa ta shirya Kayan breakfast ɗin Hajiya saratu A Babban tray ta jera mata su, Bayan fitarta daga Cikin kitchen ɗin su ka ɗaura da wata firar, sam basa gajiya da firar Familyn Obinna.
“Muna fa da gagarumin bikin ranar zagayowar Haihuwar Obie, Nasan za’ae shagali na kece raini, za’a yi 6arin Dollar da pounds, Aranar zamu ga Zaratan ƴa’ƴan Obinna da Jikokinshi waɗanda basa a ƙasar, Ina da tabbacin Owais ma zai halarta”
Fuskar Sophia ɗauke da farin Ciki tayi maganar, Abla tace”Anya ko Owais zai zo? Kinsan fa halinshi, samun lokacin shi abune mai wuya”
“ai ko baiyi niya ba sai obinna Ya matsa mashi akan ya zo, Kinsan fa kaf cikin jikokinsa yafi ƙaunar Owais, kowa yasan da wannan zancen, Kinga ko ba zai so ayi shagalin nan ba tare da Owais Ya halatta ba,” acewar Abla
Murmushi Sopy tayi “Can’t wait to see Allah Ya nuna mana Lokacin, Dole naje ayi min wankin ido, don na samu damar ƙare Mashi kallo”
“Da rabon kisha mari, Owais baya son Kallo Idan Yana magana mutun bai isa Ya ɗaga ido ya kalle shi ba, Sannan ba’a katse shi, Sauƙin shi ɗaya Idan har kika karanci halayanshi da ɗabi’unsa tsaf zaku zauna lafiya, mutunne mai sauƙin kai baida girman kai, Yana da tausayi ga taimakon na ƙasa dashi.....” tun da ta fara jera masu Kyawawan halayanshi bata tsagaita ba har saida Landline ɗin dake a bakin ƙofar fita kitchen ɗin ta yi ringing tukunna ta dakata da yin magana, da sauri Sophia ta fuce ta je ta ɗauki landline ɗin Ta ɗaga kiran daya shigo, Cikin girmamawa tayi sallama, Jikinta sai 6ari yake yi.
“Cofee....” Iya abunda Taji an furta mata acikin wayar, jin yayi rejecting yasa ta zame ta daga saman kunnanta ta ajiyeta saman table, Dawowa Cikin kitchren ɗin Tayi Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta.
Har suna haɗa baki wurin tambayar ta “Wanene Ya kira” kwa6e fuska tayi tare da cewa”Nakasa gane muryar wanene acikinsu, Zaid ne ko Zayn, Coffee su ke buƙata, wa zai kai masu”? Ta yi tambayar tana kallon sauran. Shiru babu wanda yace zai kai, saboda Mugun tsoron shiga part ɗinsu suke Yi, saboda masifarsu,”