Sashe 88
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Nayi ƙoƙarin Na saida motata don na samu na biyata kuɗinta sai dai bansamu wanda zai siya ba, Jiya ina kwance saman gado na gama shan kuka na sai ga kiran fatima awaya, na ɗaga muka gaisa da ita, tace min mominta tana son Yin magana dani inzo in same ta agida, hankalina ya dan tashi don tunda muƙe nuƙu nuƙu akan yadda zamu biyata kudin bata ta6a yin maganar dani ba, tsakaninta ne da fatiman, nace mata zuwa gobe zanzo gidan nasu, jiya ko bacci banyi ba, da sassafe na shirya babu wanda ya san na fita daga gidan nan naja mota naje gidansu fatima babu kowa afalon gidan saida mai aikin gidan ta fito daga kitchen muka gaisa take ce min ai hajiya ta faɗa mata game da zuwana in shiga ɗaki tana jirana, da sauri na juya na nufi ɗakinta gabana na faɗuwa abakin kofar ɗakin nayi mata sallama, muryarta ƙasa ƙasa tace min wanene? nace mata zahra ce ƙawar fatima mai dimple, tace in shigo ciki.....” dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana faman ƙyafƙyafta ƙwayar idanuwanta.
Cikin ƙagara da sonjin ƙarashen zancen Aneelerh tace”naji kinyi shiru? Me tace maki ne”! Yawu zahra ta hadiya muryarta na ɗan rawa ta ɗaura da cewa”Ina shiga ɗakin na same ta kwance saman gado daga ita sai ɗan undy shara shara ajikinta, arude na juya zan fuce da sauri ta kira sunana zahra zonan, cak na tsaya ba tare dana juya na dube ta ba, ta sauko daga saman gadon ta nufo inda nake a tsaye ta tsaya daga bayana ta soma yi min magana .
Ya maganar kuɗina da zaku bani? Nayi magana da fatima tace min atare kuka kashe kudin meyasa zahra? Ban ta6a tunanin za ku yi mini haka ba, Na yadda daku na damƙa maku amana amma kuna nema kuyi mini wasa da dukiyata, ko dan ba ku san zafin nema bane”? faɗa sosai tayi mini bansan lokacin dana fashe mata da kuka ba ina roƙonta akan tayi hakuri nayi mata alƙawarin zan biyata kuɗin ta cikin satin nan, Aunty Aneelerh ba zato ba tsammani naji ta sanya hannu ta ruƙo hannuna, ta juyo dani ta rungumeni a ƙirjinta, ban ɗauka da wata manufa ba sai da naji tana matse ni a kirjinta gabana yaci gaba da faɗuwa, cikin dabara ta miƙa hannu ta bayana ta datse ƙofar ɗakinta da jamlock, ba tare da sanina ba....” ganin yadda Aneelerh ta zaro ido waje yasa zahra ta dakata da yin maganar la66anta na kerma.
Aneelerh tace”zahra ke nake sauraro uban me tayi maki” a kausashe Aneeleeh ta furta mata hakan, cikin ruɗu zahra tace”nayi ƙokarin raba jikina da nata amma saita ƙara tighting dina, ta zame mayafin dake akaina, ta sanya hannu tana shafa sumar kaina cikin raɗa take furta min”meyasa nake yi mata kuka? Ko dan saboda tayi mini faɗa akan kuɗinta ne, muryata na kerma nace mata ta yi haƙuri zan biyata kudinta, tace min in kwantar da hankalina ai ba dole saida kuɗi zan Iya biyanta ba, A jikina ma ina da abun da suka fi kuɗi daraja, idan na amince na bata haɗin kai zata yafe mana bashin harma ta yi mana order na kayan decoration din da muke so, cikin rashin fahimtar maganarta nace mata ni ban gane me kike nufi ba? Menene yafi kuɗi daraja a jikina? Kuma wani irin hadin kai kikeso in baki”? Har lokacin bata raba ni da jikinta ba, saima nishi da naji tana saki, tace min tana buƙatata jikina kawai takeso, zatayi amfani dani.
Saboda yarda da nayi da matar saina dauka wasa take yi mini, Cikin sanyin murya nace mata mommy amma dai zolayata kikeyi ko”? Na fada ina kokarin raba jikina daga nata saidai taƙi bari inyi hakan, kamar zata maidani cikinta.
Babu alamun wasa a kalamanta tace min” Zahra na ta6a yi miki wasa irin wannan? Nace mata a’a, tace min toh dagaske take, dama ta jima tana kwaɗayin son kasancewa tare dani bata samu damar yin hakan ba don ta lura kamun kaine dani kuma ni ba ƴar harka bace, shiyasa ta yi dabarar amincewa da buƙatarmu ta buɗe mata company kuma taƙi kar6ar kuɗin ribarta dake a hannun mu, Ashe maƙarƙashiya ta shirya mini saboda tasan zamu iya ta6a kuɗin, Ni ban ta6a tunanin matar zatayi mini haka ba.
Aunty Aneelerh data faɗamin hakan tsigar jikina ta tashi, na rasa uwar ubana, na soma kiciniyar ƙwace kaina daga ruƙon da tayi min ina fadin ni ki sake ni in tafi gida, wlh kin ban mamaki na dauke ki tamkar mahaifiyata saboda ƙaunar dake a tsakanina da fatima ashe nayi babban kuskure, Ni bazan ta6a baki haɗin kai don mu aikata sa6on Allah ba, kema inayi maki fatan Allah ya shiryeki,’ sai da nasha wahalar bangajeta, da gudu na damƙi ƙofa zan buɗe naji ta a garƙame kafin in zare jamlock din Naji ta damƙeni ta wurgar dani saman gado tana fadin”baki isa ki kubcemun ba zahra, dama nasan zakiyi min taurin kai shiyasa na biyo maki ta wannan hanyar, wlh idan har kika bijirema buƙatata zan saki dole ki biyani kuɗina a yau ɗin nan idan ba haka ba zan damƙa ku hannun lawyer dina, sannan zan rufe companynku,”
Ina kuka nace mata naji ta bani lokacin da take son kuɗinta In sha Allah zan biyata amma ni kada ta kuskura tace zata ta6a jikina, ta jira taga idan ban biyata ba sai ta yi mini duk abun da ta ga dama, tana faman sakin shu’umin murmushi tace min bataso inyi danasani, don tasan banda arziƙin da zan Iya biyanta, tasan wanene mahaifina karen ƴan siyasane sai yayi masu wahala suke watsa mashi hatsin da zai samu ya tsastsaga harma ya ɗan mana, raina ya 6acin sosai jin irin wulaƙancin da take yi mini nasan nina ja ma kaina, dama ance kwaɗayi mabuɗin wahala, sannan idan har kace zaka dogara da wani kana tare da wahala, sai dai ba yadda zanyi ne tun farko da nasan wacece ita wlh daban amince ta buɗe mana company ba, daƙyar na samu ta ƙyale ni abisa sharadin gobe da safe ƙarfe 7 tana jiran alert na kuɗinta, wlh idan daddy yaji maganar nan sai ya kusa kasheni, ni bansan ya zanyi ba”
Zuciyar Aneelerh tayi matuƙar karaya, tayi mamakin Hajiyarsu zahra me halin bunsuranci.
“har nawa ne kudin”?
Zahra na matsar ƙwalla tace”kusan fa miliyan shidda muka raba ni da fatima”
Zaro ido waje Aneelerh tayi tana mai jinjina kai tace”tabɗijancan, ashe da rabon zahra ki kwana a cell, don kuwa babu abunda zai hanaki zuwa gidan Yari, Ni har na hangoki cikin uniform dinsu” fashewa zahra tayi da kuka jin abunda aneeelerh take faɗi.
Cikin shessheƙar kuka tace”Aunty aneelerh kidaina banso, bakisan halin da nake aciki bane shiyasa kike zolayata, wlh saboda tashin hankalin da nake aciki tun safe ko ruwa ban sha ba”
Tsananin tausayinta ne Ya kama
Aneelerh, idanuwanta sunyi jawur dasu kamar an watsa mata barkono, muryarta na rawa tace”Aunty aneelerh ko zaki taimaka mini mu je mu nemo wanda zai sayi motata da wayata kafin lokacin Ya cika” Jikinta na kerma tayi magana.
“Lokacin da ku ka yi yarjejeniyar buɗe companyn kinyi shawara da wani? Ina nufin Uncle ko Ummi akwai wanda kika faɗa mawa”?!
Girgiza kai zahra tayi”Ni ban faɗa ma kowa ba, babu wanda ya sani, kawai dai na faɗa masu na samu aiki a company, sun tayani murna kuma sun yi min fatan akhairi, ummi ma ta ta6a tambayana ya akai companyn yaci sunana? Kamar nawa, sai nace mata banawa bane, Yarinyar me companyn ce takwarata shiyasa aka sanya mashi Sunan Zahra world of beauty”
Jinjina kai Aneelerh tayi”Kinyi babban kuskure Zahra, Matar nan Tayi maki wayau, Nafi ganin laifin ki, ke fa da kanki kikace kinsan halinta masifaffiyace amma ahaka kika biyewa fatima ku ka kashe kuɗi har miliyan shidda bayan kinsan ba gadon ɗan iya bane, Idan ita yarinyar bata da wayau ai ke da hankalin ki, kuma ita dukiyar mahaifiyarta ce, ke kuma fa? Baki haɗa komai da ita ba,Yanzu ai gashinan taja maki bala’e, ko dai ki biyata kuɗinta ko ta maka ki kotu, Ni dai shawarar da zan baki shine kije ki yi mata abun da take so!” hankali akwance aneeelerh tayi mata magana, tayi tsammanin zata taimaka mata ne donsu nemi mafita amma sai taji tana fadin hakan, zuciyarta ta karaya sosai, har batasan sa’adda ta fashe da kuka ba, ta sauko daga saman kujerar ta zube saman gwiwowinta Cikin shessheƙar kuka take fadin”Na shiga uku aunty aneelerh, amma dai wasa kikeyi mini ko? Ni nasan bazaki ta6a bani shawarar in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, wallahi ina tsoron Allah, Ina tsoron ranar da zan koma gare shi”
Ɗaure mata fuska Aneelerh tayi”Idan har baki amince mata ba zahra tayaya kike tunanin zaki Iya biyanta? Kinsan halin mahaifinki bazai ta6a biya maki kudin nan ba, Ummi kuma bata da kuɗi, zahra ƙwara ki bata haɗin kai, nayi maki alƙawarin babu wanda zai ji abunda ya faru, daga ni sai ke, kinga tace zata ƙara maku wasu kudin harma tasa ayi maku order na kayan da zaku yi amfani da su daga dubai, wallahi zahra ki amince mata idan ma don baki saba bane zaki saba a Hankali, Allah kuma gafurirrahim ne, zaki iya tuba ko daga baya ne in ta gama amfani dake”