Sashe 90
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Na lura zayn baka son daddy, baka ƙaunar shi, kafi son mommy, sai kace bashi bane ya haife ka, na tabbata da ace mommyne ta baka atm dinta jiki na rawa zaka kar6a ka yi amfani da kuɗin amma da yake na daddy ne shine kake neman yi mashi ƙazafi, wallahi kaji tsoron Allah zayn, mahaifin mu babu abunda yake aikatawa da guminsa Ya tara kuɗin shi, wata’kil dama can me arzikine Ya dai 6oyene don baison agani, amma nidai ina kyautata mashi zato, kuma atm daya bamu don yaga muna buƙara kuɗine Yana so ne Ya faranta mana” Zayn ya natsu yana kallon dan uwan nashi ya haƙiƙance Yana yi mashi magana, sai da yakai ƙarshen Aya tukunna zayn yace”baka amfani da ƙwaƙwalwa, ta inda muka banbanta kenan, Zaid ka faɗa min wani ubane zai ɗauki maƙudan kuɗi irin wadannan yaba ƴa’ƴanshi don suyi sharholiya? Ba tare daya tambayi me zasu yi da kuɗin ba? uba na gari bazai ta6a aikata hakan ba, Ni bani ke bansan daddy ba, shine baison mu zaid! Saboda tun da muke dashi bai ta6a zaunar damu a matsayin shi na mahaifinmu yayi mana nasiha akan rayuwar duniya ba, ko lahirarmu, komai mu ka yi dai dai ne a wurin shi, Mommy ce kaɗai take tsawatar mana idan mu ka yi ba dai dai ba......”
Tun da Zayn ya fara magana muryarshi a kausashe, idanuwanshi sun kaɗa sun ciko da ƙwalla, zaid dake sauraron shi, Yayi shiru yana kallon shi, Jikin shi ya fara yin sanyi, dakatawa ya ɗanyi yana faman fitar da huci, kafin ya ɗaura da cewa”idan har dagaske kuɗin shi ne meyasa be yi amfani da su ya gina mana gida na kanmu ba? bayan yasan duk irin gorin da ake yi mashi, hmmm kawai baison asan Yana da kudin ne don yasan za’a tuhume shi ina ya same su, shine kawai,” shiru su kayi ɗakin Yayi tsit na ɗan wani lokaci,
“Kaina harya fara ciwo, Inaso in kwanta In huta” Zaid ne ya ambaci hakan tare da miƙewa Ya nufi closet din Kayansu dake acan cikin ɗakin,
Kwantawa zayn yai saman mattress yayin da idanuwanshi suke fuskantar ceilling, abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yake yi ba, Yana matuƙar jin ɗacin irin rayuwar da mahaifinsu yake yi.
*Hajiya Saratu ❤*
A tsaye take gaban mirror, jikinta sanye da Jallabiya, babu mayafi akanta, hakan ya bayyana kitson zanan dake akanta, hannunta ruƙe da wayarta ta karata a kunnanta, fuskarta da fara’a, ga dukkan alamu magana take yi da wani awaya.
“Nayi mamakin ganin kiranki, Allah dai yasa lafiya, don nasan hakanan baki nema na, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba”
On the other hand matar da suke yin waya ta soma magana, Daga jin muyarta babbar macace mai ji da qasaita.
“Oh, saboda kada na fara yi maki ƙorafin baki kirana shine kika rigani yin magana”?
Hajiya saratu na dariya tace”wallahi ba haka bane Hajiyata, abubuwane suka yi min yawa, amma duk da haka ai ina ƙoƙarin tura maki saƙon barka da juma’a, ke dai ce baki nemana, amma nayi maki uziri saboda hidindimun al’umma da kuke fama da su, nasan sune suka sanyaki busy”
“Hakane, amma kada ki damu, dama dalilin dayasa na kira ki, game da zuwanmu gidane, Naga saƙon ankon da kika tura mini nagode, so abunda nikeson kiyi mini, Inaso ki fada min me baba yafi so”? murmushi saratu tasaki, Har cikin ranta taji dadin tambayar da tayi mata.
“Gift ne zaki shirya mashi na birthday dinshi”?
“Eh, na tambayi yayanki akan ya faɗa min me yafi so, kinsan halin shi, cewa yai shi baisani ba, Duk abunda yayi mini in siya mashi, Ni kuma nafi son abun zai burge shi sosai”
Dariya hajiya saratu tayi tana fadin” Gaskiya baba ni kaina bazan Iya cewa ga abunda yafi so ba, amma kwanakin baya naji yana magana da abokinshi akan yana son suturar su na al’adar inyamurai, tun lokacin dai banji sun ƙara magana ba, kuma ba akawo kayan ba, idan har kika shirya mashi su a matsayin gift dinsa, Nasan zai yi farin ciki sosai kuma zaiyi mamaki”
“Okey, Send me his measurements through WhatsApp, and please don’t let anyone know. I want to surprise him.” ta amsa mata da toh nima agaida mun da yayan nawa, ko na kira shi sai yaga dama yake ɗagawa, Ina nan ina jiran shi zamu haɗu ne” sautin dariyar hajiyarne ya cika kunnanta da ba’a tace”Ai kin fi kowa sanin yayan naki, sai dai ki ba wani labari” Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama, Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin zama gefen gadonta, Muryar Hajjaty ta katse mata hanzarinta, tayi mamakin jin sallamarta, don koda gigin wasa bata ta6a tako ƙafarta zuwa ɗakinta ba, Jim ta ɗanyi kafin ta furta”Wacece” ta fada tamkar bata gane me magana ba”
“Hajjaty ce” jinjina kai Hajiya saratu tayi tuni mood din fuskarta Ya canza, jim ta ɗanyi kafin tace”zaki Iya shigowa”
A hankali ta turo ƙofa ta shigo ɗakin, tun daga ƙasa hajiya saratu ta soma binta da wani matsiyacin kallo, pakistan ne ajikinta farare, ta ca6a uban ado, sai dai babu ƙamshin turaren nan, sai ka matsa kusa tukunna zaka Iya jin shi, hannunta biyu ruƙe da wooden tray, kayan abincine shaƙe asaman shi.
Lamarin ya ɗaurewa Hajiya saratu kai, tayi sototo tana kallon ta
Muryarta na ɗan rawa ta furta”Ina wuni” yamutsa fuska tai”da ban wani ba kin ganni, shin wai ma me ya akawo ki room dina? Makuwa ki kayi ne”? Fuska adaure ta mata maganar.
Duk tasha jinin jikinta, adabarbarce ta furfa”am..umm...dama abincine na kawo maki, Ni na girka shi da kaina abincin ƙasar mu ne...” daƙyar ta ƙare maganar a tsananin tsoroce.
Murmushin yaƙe hajiya saratu ta sakar mata”dama ke ce kike kawo min abinci? Ina masu aikin gidan ne? Ko sunyi yaji ne”
“Suna a kitchen suna aiki, kawai nayi ra’ayin in kawo maki ne da kaina, nasan zaki ji daɗin girkin tun da baki saba cin kalar shi ba” hankalin ba akwance ba take yin maganar,
Ruƙe ha6a hajiya saratu tayi tana faman jinjina kai tace”To fa, sabon salo, tanan kika biyo? An gaya maki bani da hankali ne da zanci abincin da kika girka da hannun ki? Wato bokan ki ya haɗo ki da maganin barbaɗe kin zuba min aciki shine ki kawo mun don inci in mutu saboda kinsan abinci ne lago na ko”?
Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, cikin sanyin murya tace”Allah shine shaidata, tun da nake arayuwata ban ta6a takawa naje wurin boka ba, kuma ni banzo da niyar in cutar dake ba, abincine kawai na kawo maki, dan Allah ki kar6a ki ci......” Kafin ta ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dakata mata tsawar data firgitar da ita, jikinta ya kama kakarwa, nuna mata hanyar fita tayi daga ɗakin”Fuce min daga ɗaki tunkafin Inyi ƙwallo da tray din hannun ki, Ƴar rainin wayau, wallahi na fi ƙarfinki ba za ki ta6a cin galaba akaina ba, tunda can baki ta6a girka abinci kin kawo min don inci ba sai yau da kika shirya kashe Ni”?
Tuni idanuwan Hajjaty sun cicciko tab da ƙwalla, cikin shessheƙar kuka tace”meyasa kika tsaneni? Laifin me nayi maki? Duk cikin masu aikin gidan nan ni kaɗaice ke bakiso, idan laifi nayi maki ki faɗa min sai in gyara”
A tsawace Hajiya saratu tace”wai ke baki da hankali Ne? Kin manta wacece ni acikin gidan nan? Ko kin fara shaye shaye ne? Ni narasa gane wani tsautsayin ne ya kawo ki cikin ɗakina, I don’t know where you get the nerve to talk to me face to face, ke ga ta6ararra dallah fuce ki ban wuri”
Juyawa Hajjaty tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, Kamar zatayi tuntu6e, gutun tsoki Hajiya saratu taja tare da samun wuri ta zauna gefen gado, tana mai mamakin ƙarfin hali irin na Hajjaty.
_~*✊💋BossLadiesWriters💋✊*~_
~The return of Benazir~
سجن القدر❤🤍❤
Bayan fitar Hajjaty daga ɗakin Hajiya saratu, zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta, taji ɗacin maganganun da saratu ta faɗa mata, ita har ga Allah bada nufin komai taje kai mata abincin ba, dama Pravin ne ya bata shawarar ta rinƙa kyautata mata, wata’ƙil ta fara ƙaunarta, saboda ta faɗa mashi tana son su dinga shiri da matarshi.
Kafin tabar ƙofar ɗakin sai da ta ajiye tray din ƙasa, ta share ƙwallar fuskarta, tukunna ta ɗauka ta nufi ɗakin twins da niyar ta kai masu abincin wata’kil su ci.
A lokacin Zayn yana zaune saman gado Ya tasa laptop dinsa agaba Yana operating dinta, zaid kuma Yana a kwance gefenshi hannun shi ruƙe da Wayar shi Yana daddanna ta.
Sallamar hajjaty ce ta janyo hankulan su ga duban ƙofar ɗakin.
Zayn tamkar bai ji ba yai shiru yaƙi amsawa sai zaid Ne ya amsa mata tare da bata Iznin shigowa ciki, A hankali ta shigo da tray muryarta asanyaya tace”barkan ku da hutawa, fatan kun wuni lafiya” da fara’a akan fuskar zaid ya ce”lafiya lou auntyn mu, yau ke ce da kan ki ki ka zo kawo mana abinci”? Ya yi maganar tare da ajiye wayar shi ya sauko daga saman gadon Ya nufe ta, zayn ko kallo bata ishe shi ba, baiwar Allah taji daɗin sakar fuska da zaid ya yi har cikin ranta taji ta ƙara ƙaunar shi.
“Abincin ƙasar mu ne, ni na girka shi da kaina, na kawo maku ne don ku ɗanɗana” hannu biyu zaid yasa ya kar6i tray din Daga hannunta yana fadin”gaskiya kina ji da ƴa’ƴan nan naki, wallahi munji daɗi, kamar kinsan kuwa yunwa muke ji, Yanzu nake shirin kira akawo mana abinci mu ci”
Asaman table ya ɗaura tray din, sai faman sakin murmushi take Yi yayin da take kallon fuskar zaid, buɗe warmer ya fara yi, ƙamshin Abincin ya daki hancinsa, Jinjina kai yai tare da ɗago da ido Ya kalle ta”Aunty, Ya sunan wannan haɗin”?
“Chicken tikka masala” ta faɗa still da murmushi kan face dinta.
“Daga jin ƙamshin abincin zai yi daɗi, balle ma daya kasance hannu mai albarkane Ya girka sa” ya fada yana nade hannun rigarsa.
“Zaid! Kada ka kuskura ka ci abincin nan! Kai baka da hankaline”? Ras taji gabanta ya fadi jin abun da zayn yace.