← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 152

Sashe 92

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Aneelerh ce ta ratsa kunnanta”Yar uwata rabin raina, tun safe baki ci komai ba, Ga abinci na kawo maki” Shafa tafin hannunta tayi saman fuskarta, Rai amatuƙar 6ace ta yunƙura ta mike haɗi da fuskantar Aneelerh, dake tunkarota, hannunta ruƙe da madaidaicin tray, mai ɗauke da plate din shinkara da ƙaramar warmer ta miya, tare da lemu mai sanyi.

Kafin ta ƙaraso zahra ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Aunty Aneeleeh idan kin kawo abincin nan domin in ci ne to ki maida shi kitchen! Bana buƙata” a faɗace ta furta.

“Haba zahra, kashe kanki ki ke so Ki yi ne? Tun safe baki ci komai ba, Ni kaɗai na damu dake, dan Allah ki kar6a ki ci”

Harara zahra ta wurga mata cikin 6acin rai tace”Ai ni kingama zubda girmanki a idona, tun da har kika iya bani shawarar In amince wurin aikata sa6on Allah, Kin ban mamaki aunty aneelerh, bansan haka kike ba” tana magana tana jan majina.

Jinjina kai Aneelerh tayi”Laifina ne zahra, Ni da na damu dake shiyasa kike gaya min magana son ranki, daga taimako? Daga yau ka da ki kuma tsammanin zan ƙara baki shawara idan har baki kar6i abincin nan ba” wani ɗan iskan kallo Zahra ta watsa mata, har saida ta dasa aya amaganarta tukunna zahra ta ruƙe qugu kamar ana tunzurata tace”Idan har kin damu dani, meyasa ba zaki taimaka mu nemi mafita atare? Saima ƙoƙarin da ki ka yi don ganin kin sanya ni a gur6atacciyar hanyar da zan lalata duniyata da lahirata, ke ba mai ƙaunata bace aunty Aneeleeh, bana sonki kuma bana son ganin ki!, Yakamata ki nisanta kan ki dani, Idan ba haka ba zan yi maki rashin mutuncin da baki ta6a tsammani ba!!”

A kausashe Ta furta maganar tana nuna Aneelerh da cazbahar hannunta kamar zata rufe ta da bugu.

Gyaɗa kai Aneelerh tayi tama rasa bakin magana, kalaman zahra sun bata mamaki, bata ta6a tunanin zahra zata Ya furta mata su ba.

Juyawa ta yi da sauri ta nufi ƙofar fita, adai dai lokacin Mahboob yana ƙoƙarin shigowa ɗakin suka ci karo da Aneelerh, har gaishe ta ya yi amma ko kallon shi ba ta yi ba, hakan yasa shi tsammanin ko wani abu Ya faru ne.

Zahra na jin sallamar shi da sauri ta sanya hannu biyu ta share hawayen dake akan fuskarta, komawa tayi daga gefen gadonta ta zauna tana dubanshi.

Riga da wandon shadda ne ajikinshi, hannun shi ruƙe da key din motar shi.

“Zahra Lafiya ki ke yi mini kiran talauci? Ina akan hanyar dawowa gida naga miss calls dinki, Allah dai yasa lafiya”

Cikin sanyin murya tace da shi”ka zauna mahboob mu yi magana” zama yai da ɗan mamaki akan face dinsa yace”meyasa ki kuka? Naga idanuwanki sun kumbura wanene Ya ta6a ki? Ko ke da aunty Aneelerh ne”?

A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faɗin”bakomai, banajin daɗi ne kaina ke ciwo”

“Kin sha magani” cikin kulawa yake yi mata magana, ɗaga mashi kai tayi alamar eh ta ƙara da cewa”Aunty Aneelerh ce ta bani maganin”

Gyaɗa kai yai”okey, Allah ya sawaƙe sister yanzu dai faɗamin me kike buƙata ne Kin dai san ban da ko sisi”

Murmushin takaici tasa kar mashi jin abinda yace

“Mahboob ba kuɗi zan roƙe ka ba, taimako nakeso kayi min dan Allah, bana son ka tambayeni dalili kawai ka yi abun da nace maka, kuma bana son kowa Ya sani daga ni sai kai”

“Kada ki damu, Ina jin ki” a ƙagare Ya furta mata hakan
“Inason zan siyar da motata ne da wayata, saboda ina buƙatar kuɗi ko akwai wanda ka sani da zai Iya siya a yau din nan’? Ta jefa mashi tambayar tana duban fuskarshi.

Mamakine ƙarara akan fuskarshi, Har saida Yaɗan saki baki da ido Yana dubanta Kafin yace”ke kuwa me zai ja ki siyar da motarki da wayarki? Runtse ido ta dan yi hawaye na ƙoƙarin cin ƙarfinta tace dashi”Mahboob banason tambaya! Kawai ka taimaka mun in zaka Iya in kuma ba za ka yi ba to ka tashi ka tafi kaban wuri”

“Shikenan Naji, nayi shirun, amma dai kinsan kowa zai saye su sai kin faɗi ko? Ba lallai asamu wanda zai siya da mutunci ba”

Ɗaga mashi kai tayi”Ni wannan ba damuwata bace, indai kuɗin zasu kai 4m Ya wadatar”

“Okey, amma ni shawarar da zan baki mai zai hana ki bada motar da wayar taki jingina? Idan kika samu halin biyan kuɗin sai ki Kar6o Kayan ki, zahra kinsan babu mai siya maki su idan kika rasa na hannunki kuma ni bazan juri ara maki motata ba” Ya faɗa Yana yamutsa fuskarsa, Harara ta watsa mashi da rinannun idanuwanta”kai fa banza ne wlh, Ni ina ruwana da motarka? Koda zan rasa abun hawa mahboob bazan ta6a aron kayanka ba”

Murmushi ya ɗan saki tare da miƙewa yace”to Aunty zahra, Ni zan tafi, in sha Allah zan samu wanda zai siya, amma ki sani zamu kasa kuɗin gida uku, Ki kwashi kaso biyu ni kuma ɗaya....”

Tunkan ya ƙare maganar zahra ta rarumi pillow aguje tabi shi da gudu ya fuce daga ɗakin Yana tiƙar dariya muryarta ashaƙe take fadin”wallahi mahboob ka fita idona, Ni ba tsarar wasanka bace, kuɗin nan da gumina na tarasu bada gumin wani ba’ rai a6ace take yin maganar, bayan ta gama zazzaga mashi masifar ta juya ta koma cikin ɗakinta tana faman tallabe cikinta dake yi mata kukan yunwa.

Safa da marwa ta soma Yi A tsakar dakin duk ta ƙagara da jiran kiran mahboob, Fatanta Allah yasa asamu wanda zai sayi motar.

Wuraren ƙarfe 8 na dare, Kiran mahboob Ya shigo wayarta jiki na rawa ta ɗaga ta kara a kunnanta, Anan yake sanar da ita cewa abokinsa Ya ce yana so harma sunyi cinikin motar akan miliyan uku da rabi zai siyeta, ita kuma wayar zai siyeta dubu ɗari biyar idan ta bari ahakan zuwa gobe da safe zai kai mashi Motar da wayar, daga nan zai tura mashi kuɗin, tsabar farin Ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, duk da tayi asara ba kaɗan, saboda an karya kuɗin motar da wayar, amma hakan bai dameta, burinta ta sauke nauyin dake akanta, Bayan sun gama wayar, ta zuƙunna takai goshi ƙasa tana godiya da Allah, daga bisani ta mike tana tiƙar rawa, da gudu ta fito daga ɗaki ta nufi kitchen, ta ciko plate da abinci, ta buɗe frigde ta dauko lemu mai sanyi kafin ta dawo ɗakinta, ita kadai ta zauna tsakiyar gado tana ci tana sakin murmushi, baƙin cikinta ɗaya ta rasa damar da take da ita na zuwa Obie estate, tunawa da wannan yasata rushewa da kuka ga abinci cike abakinta.

*JOS CITY*

Dare ya tsala sosai, Gari yayi duhu, a lokacin da kowani mahaluƙi yake a makwancinsa domin runtsawa, baka jin sautin komai saina kukan tsuntsaye dana karnukan Layi dake Hargowa.

A hankali take tafiya Hannunta ruƙe da trolley, doguwa ce a halitta, siririya bata da ƙiba sai dai tana da hips, doguwar jallabiyace a jikinta, ta sanya niƙab ta rufe fuskarta, abun da zai baka mamaki ita kaɗai take Bin santar babu alamun tsoro atattare da ita, da taimakon street light ta ke samun damar ganin ko’ina, Har Allah Ya nuna mata gidan da take nema, Katafaren Villa ne Mai gingirimeman gate.

da sassarfa ta nufi gate din, tana zuwa gabanshi, Takai hannu ta soma ƙwanƙwasa ƙofar, tun tana yi a hankali har takai ga tsunto dutse ta cigaba da bugun ƙofar da shi kamar zata 6alle gate din’

Security officers din dake tsaron gidan guda Biyu ne cikin kakinsu suka fito daga ɗakunansu jiki na rawa suka ƙara so gaban gate din, da alamun mamaki akan fuskokinsu suka haɗa bakin wurin furta Wanene ke buga mana ƙofa a dai dai irin wannan lokacin”! Da fargaba suka furta maganar.

Cikin shessheƙar kuka da muryarta mai tsiwa ta furta”BENAZIR CE”

kallon Juna Officers din suka Yi, ɗaya yace”Wanene kuma haka? Mutun ko aljan? Wa ki ka zo nema agidan ko dai kin yi 6atan Hanya ne”

Tamkar zata fashe da kuka tace”dan Allah ku buɗe mun gate in shigo, ni ce benazir ɗiyar Alhaji ubaid”!

Ba ƙaramin ɗaure masu kai lamarin yayi ba, kasancewar su tsoffin masu gadin gidan, sunsan wacece benazir Yarinyar uban gidansu data 6ace tsawon shekara goma sha shidda, kokwanto suka soma Yi anya kuwa itace?

Officer mai gemu yace”kai, Da wuya ya zama gaskiya yarinyar da babu tabbacin tana araye kota mutu”!

Ɗayan kuma yace”Ai ni banma yarda ba gaskiya, Kusan shekara goma sha shidda da 6atanta sai Yau ƙarfe sha biyu na dare zata dawo! anya kuwa ba tarko bane aka ɗana mana”?

Mai gemu yace”amma kuma muryarta sak kalarta hajiya layla, Har tsiwar iri ɗaya da tayi maganar”

Jin sunƙi buɗe mata kofa yasa ta rushe masu da kuka mai sautin gaske a faɗa ce ta ke fadin”wai baza ku buɗe mun gate ba, na gaji da tsayuwa wallahi idan baku buɗe ba na shigo cikin gidan saina Sa an kore ku”

Yawu suka haɗiya atare mai gemu yace”Ke baiwar Allah, ba yadda za’ai mu buɗe maki gate ba tare da mun sanar da masu gidan ba, dan haka ki ƙara haƙuri mu faɗa masu”

Kafin suyi yunƙurin zuwa cikin gidan su sanar masu, ba zato ba tsammani suka ji ta bangaje ƙofar jikin gate din dake a kulle, nan take ƙofar ta buɗe, hankalin su ba ƙaramin tashi Yai ba, A firgice suke dubanta yayin da take shigowa ciki da akwatinta, Ko kallo basu isheta ba, da sauri ta nufi cikin gidan.

Kasa motsi suka yi Kamar an dasa masu Aya, tuni zufa ta wanke fuskokinsu, Mamakin su Taya akai ta Iya bugun ƙofa da ƙarfi Har jamlock mai ƙarko Ya zame kanshi! Tabbas suna hasashen ba mutun bace aljana ce, tuni suka sha jinin jikinsu.

Tana tafiya tana bin ko’ina na gidan da kallo, abubuwa da dama sun canza mata ba kamar yadda ta tafi tabarshi ba.
Chapter 92 · 0% Book details