← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 152

Sashe 79

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kiyi haƙuri, Nima matar aure ce kamar ke, kawai inason nasan ainihin wanene me wayar, ki taimaka min a ƙagare nake da son ji” da alama matashiyar Yarinyar Akwai ƙuruciya atattare da ita, tun daga kan kalamanta zaka shaida hakan.

“Nace maki ni ce me wayar,” atsawace ta furta hakan, Aneelerh tace”ba wayar ki bace, saboda ke da kanki ki ka ce irina ne masu bibiyar mazajan mutane don mu kwace masu miji, hakan na nufin ba wayarki bace wayar mijin ki ce” sautin dariyar matashiyar ne ya cika mata kunnuwanta, lamarin ya ɗaure ma Aneelerh kai, gashi duk ta ƙagara a matse take da son jin wanene.

“Ke dai zan faɗa maki gaskiya, tun da kin gano ni, ba wayata bace, wayar mijina ce, kuma baya nan Ya fita ni ka ɗai ce agidan”

“Okey, pls Ko zan Iya sanin sunan mijin naki”?

“A’a gaskiya, salon ki je ki kai ma boka sunan shi ayi maki asiri ki mallake shi” duk yadda Aneelerh ta kai ga jurewa saida ta fashe da dariya jin abun da Yarinyar tace, daƙyar ta sassauta da yin dariyar tace”wlh ni bana bin boka, Ko hanyar zuwa wurin shi bansani ba, Yar uwata ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ni bana ɗaya daga cikin matan dake zuwa wurin boka, saboda na dogara da Allah shi kadaine zai Iya biyamun buƙatuna”

matashiyar tace”Ni ban yarda dake ba, mata dayawa suna son ƙwace mini mijina saboda kyakkyawa ne kuma yana da ƙarfi”

Aneelerh tace”baiwar Allah na faɗa maki nima matar aurece, da mijina akan me zan nemi mijin ki”!

“Oho nima bansani ba, idan kin gama magana zan kashe wayar” amsar data ba aneelerh kenan” Shiru aneelerh ta ɗanyi tana tunanin hanyar da zata 6ullo mata, ta fahimci Yarinyar bata da cikakken Ilmi da wayau sai a hankali. Dabara ce ta faɗo mata.

Dariya ta fara saki, Matashiyar tace me kike yi ma dariya Aneeleh tace”Ai dole inyi dariya, ke yanzu baki gane muryata ba ne? Aneelerh fa ce matar abokin mijin ki Shu’aibu”

Da buɗar bakin budurwar sai cewa tayi”ƙarya kike yi aini mijina basu nan shi shu’aib ba, TAJ ne sunan shi, Kina son ki yi mini wayau ne”

Jin ta ambaci sunan Taj Yasa Aneelerh Tsayawa cak ta dakata da yin tafiya, yayin da bugun zuciyarta ya ƙaru, Muryarta na ɗan rawa ta furta”ƙarya kike yi, ba sunan mijin ki tajuddeen ba, so kike in yadda don kada ki faɗa min ainihin sunanshi, ai ni nasani Shu’aibu ne sunan shi”

Matashiyar budurwar tace”To kada Allah yasa ki yadda ma, kuma wlh ma ƙarya kike yi mini cewa wai ke matar abokinsa ne baki da gaskiya,” da alama ranta ya 6aci ta fara harzuƙa.

Sassauta murya Aneelerh tayi”Ki yi haƙuri, ba yadda ki ke tsammani bane, Dan Allah ki faɗamin ina mijin naki yake inason yin magana dashi”

Dogon tsoki matashiyar Taja, kafin ta furta”ba kin ce ke matar abokinsa bane? To ki ce ma shu’aibun Ya kawo ki gidan mu,” kafin Aneelerh ta furta wani abu, Matashiyar ta katse kiran!”

Hankalin ta Yaƙi kwanciya, Jiri ta soma gani acikin idanuwanta, a daddafe ta nufi gado, Ta haye ta kwanta, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta ta shiga ruɗani, tun da Matashiyar ta ambaci sunan tajuddeen, natsuwarta tabar jikinta, taso ace tayi waya da shi don ta tabbatar da abun da take hasashe.

Har ƙara jaraba kiran layin tayi amma matar taƙi ɗagawa.

Dubara ce ta faɗo mata aranta, da sauri ta rubuta mashi saƙo cikin harshen turanci.

_Idan ka karanta saƙona, dan Allah ka kira ni, Inason Yin magana da kai, saƙo daga Aneelerh muhammad falgore_

Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kammala rubuta mashi sakon, Ta ɗaura wayar saman side drawer, A gogon ɗakin ta kalla ƙarfe Uku na rana, kwanciya tayi saman gadon tana jiran tsammanin Kiran me wayar.

❤ZEENATU❤

A 6angaren zeenatu kuwa tun da ta fito da gudu daga ɗakin Dr. Shureim ta koma ɗakinta, ta fada saman gado taci gaba dayin kuka tamkar ranta zai fita, cikin muryar kuka take fadin”yaya shureim ba sona yake yi ba, wata yake so daban, dama nasani babu namijin da zai yarda yaso ni saboda rashin natsuwata,”

Idanuwanta sun kaɗa jawur, miƙewa tayi zaune ta soma cire lace jikinta a saman floor, ta watsar da kayan hada ribbon din da aka daure mata gashin kanta, iya undy ta bari a jikinta, ta jashi saman ƙirjinta, tana huci yayin hawaye ke cigaba da wanke mata fuskarta, saukowa tayi daga saman gadon ta nufi gaban dressing mirror dinta, cikin 6acin rai ta sanya hannu ta watsar da jerin turarurrukanta komai sai da ta wurgo shi ƙasa, bayan ta gama ta koma gaban wardrobe dinta, ɗaya bayan ɗaya sai da ta wurga da suturar saman floor, hankalinta bai kwanta ba har saida ta maida ɗakin kamar na mahaukata, tukunna ta koma saman gadon ta haye tare da jan bargo ta lullu6e zuciyarta na ta farfasa.

Bayan Dr. Shureim ya fito daga wankan, kimtsa kanshi yai ciki shiga ta larabawa Ya feshe jikinsa da turare,
Ya ruƙo wayar shi a hannun shi, tare da car key dinsa, walking quickly ya fito daga bedroom dinsa, Ya nufi ɗakin zeenatu, duk inda Ya gifta a paloun masu aiki ne suke Yin aikace aikacen su cikin girmamawa suke gaishe da shi.

“Yalla6ai barka da fitowa” muryar Tani ce ta katse mashi hanzarinsa, dakatawa yai da yin tafiyar ya juya ya dubeta

“Yawwa barkanki, Ya aiki” fuskarta da fara’a ta amsa mashi”Lafiyalou Alhamdulillah,”

Har zai wuce ta Ya kuma tsayawa ya kalle ta”Ɗakin zeenatu nake nema” Da rawar Jiki ta ce”Yana a second floor, muje in nuna maka ɗakin” ta faɗa tare da yin gaba Yabi bayanta, Yayi matuƙar ƙagara da son ganinta, duk don Ya lallasheta akan laifin da yayi mata.

Bayan sun hau elevator ta sauke su a second floor, Tani ta nuna mashi ƙofar ɗakinta.

“ki shiga ki faɗa mata inason magana da ita”
Tani ta amsa da toh, tana zura ƙafarta ɗakin zeenatu, gabanta Ya faɗi ganin irin 6arnar da tayi, hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, jiki na rawa ta nufi gefen gadonta.

“Zeenatu! Lafiya meke damunki ne? Meyasa kika hargitsa suturar ki”?

Shiru zeenatu bata tanka mata ba, saima ƙara ƙudundune kanta da take yi cikin bargo.

“Dan Allah zeenatu kiyi mini magana, nasan 6ata maki rai akayi ki fada mini wanene”

Jin tayi shiru ba ta yi mata magana ba yasa tace”ba zan takura maki ba, Yanzu ki tashi Yayan ki shureim Yana a ƙofar ɗakin ki, shine yace in yi maki magana yana son ganinki”

Kamar jira ta ke yi Tani ta ambaci sunan shureim, Cikin shessheƙar kuka tace”Tani, I don’t want to see him. Please tell him I won’t come. Yaya Shureim doesn’t love me wata yake so daban, tun jiya yayi min alƙawarin zamu fita yawo atare, yau kuma da kanshi yace min inje in shirya kafin in dawo zai yi wanka ya shirya, Tani da naje ɗakin shi babu abunda yayi, yana akwance saman gado yana kallon hoton girl friend dinsa a laptop....” daƙyar ta ƙare maganar.

Jikin Tani yai sanyi, duk sai taji ba daɗi, sai yanzu ta gane dalilin dayasa ta shiga halin da take aciki.

“Kiyi haƙuri zeenatu, ki tashi ki gyara jikinki, Yace yana son magana dake nasan yazo ne don ya baki haƙuri, kuma naga ya shirya hada key din mota a hannunshi....” Katse ta Zeenatu tayi”Na fasa zuwa ki faɗa mishi bazan je ba, tun da bayaso na”

Cikin muryar raɗa Tani tace”yana fa jin ki, bai kamata kina ɗaga murya ba, sannan ke in banda abunki waya fada maki budurwashi ce yake kallo awayar?

“Ai naga hoton da yake kallo, Yana a kwance saman gado ya rungumeta a kirjinsa” ta fada tana jan numfashi taƙi fitowa daga bargon.

“Zeenatu, kiyi mashi kyakkyawan zato, yaya shureim yana sonki fiye da yadda kike son shi, Ni shawarar da zan baki shine kada ki bari ya gane kina son shi, idan kika kwantar da hankalin ki da kan shi zai furta maki kalmar so”

Sassauta muryarta tayi”Tani, zan iya jure wannan amma bazan Iya jure kallon hoton budurwarshi da Yake Yi ba,”

Dafe kai Tani tayi da hannu ɗaya”zeenatu baki da tabbacin budurwashi ce, pls kibi komai a sannu zamu gano ainihin wacece Yake kallo awayarshi, Yanzu Ki tashi muje Yana awaje yana jiranki’

“Tani ki daina wahalar da kanki, Nifa ba inda zanje, Ki fada mashi bana Jin daɗi bacci Nike Yi”

Duk yadda Tani taso ta lallashe ta akan ta tashi ta je gare shi taƙiya, a dole ta ƙyaleta ta juya ta fuce daga ɗakin.

A tsaye ta same shi Ya jingina bayanshi jikin bango.

Harya fara Gajiya da tsayuwa
“Ka yi haƙuri, Zeenatu tayi fushi bansan meya haɗa ta dakai ba, nayi ƙoƙarin In lallasheta amma taƙi amincewa ta amsa kiran ka, ban ji daɗi ba shureim, duk da bansan meya haɗa ka da ita ba, amma bai kamata tun yanzu afara samun rashin jituwa a tsakaninka da ƙanwarka, zeenatu tana da haƙuri sai dai tana da zuciya idan aka 6ata mata rai’

Tun da ta fara magana Ya natsu yana sauraronta, sai da ta kai karshen maganar tukunna yace”Inaso zan shiga ciki”

bai jira amsar da Tani zata bashi ba yai saurin haura ƙafarshi cikin ɗakin zeenatu.

Dafe kai tayi da hannu ɗaya tunawa da 6arnar da zeenatu tayi a ɗakin, gashi kuma Ya shiga hake zai je ya same shi kamar bola, can kuma ta ayyana aranta cewa ɗan uwanta ne, daga haka ta ƙara gaba.

A tsanake Yake bin ko’ina na ɗakin da kallo, yayi mamakin ganin yadda ta hargitse komai, ta rikita mashi tunanin shi, Ya rasa gane fushin menene take yi da shi? Don shi a tunanin duk akan fitar da yace za su yi ne.

Sam bai lura da lace din data cire ta jefar saman floor, idanuwanshi na akan gadonta, bargon da ta lullu6e dashi sai kerma yake kamar wadda sanyi ya kama.

daddaɗan ƙamshin turarensa ne Ya daki hancinta, Nan take ta fahimci Ya shigo ɗakin nata.
Chapter 79 · 0% Book details