Sashe 3
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunnar dakai ƙasa Angel tayi a tsananin ruɗe Batul ta ɗaura da cewa"Ae tun lokacin da aka canza mana abinci zuwa ganye, Angel ta soma Fita hayyacinta, sam babu natsuwa atattare da ita, Hakanan zaki ga ta zauna tana sambatu ita kaɗai" ta ƙarasa maganar hada murmushinta,
(Yara sun zama ƴan wasan kwaikwayo)
"Eyyah Hakane ashe, " jinjina kai Angel tayi"dama ni tun ina agida idan na ci abincin da aka haɗa da ganye zaucewa nake yi, Bana son Cin ganye yana affecting ɗina" Fuskarta amarairace ta yi maganar.
Shiru tsohuwa zafreen ta yi a yayin da ta ke ƙare masu kallo kamar tana son gano wani abu da ke 6oye akan fuskokin su sai dai Allah bai bata ikon fahimtar komai ba, Abun da ya ɗaure mata kai yadda su ke yi mata magana ba tare da jin shakkarta ba.
"Da za ki bamu dama Yau na rana ɗaya kawai, Ki zauna muyi fira da ke, A matsayin ki na kakarmu....." gaba ɗaya sun ruɗar da ita, sai kallonsu take yi tana faman jinjina kai kamar ƴar ƙadangaruwa
Sun kashe mata bakin magana, A hanzarce ta juya ta nufi bene Giants dake take mata baya suka juyawa tare da bin bayanta, Suna jiyo sautin rufe ƙofar ɗakinsu, Gaba ɗaya suka daka uban tsalle tare da rungume junansu fuskokinsu ɗauke da farin Cikin nasarar da su ka yi akanta, yau sun kashe tsohuwa zafreen da mamaki
"Alhamdulillah Ya Allah, Mun gode da taimakon ka agare mu, " Angel ce ta furta hakan.
"Mun ji jiki yau Allah, ba kiji yadda gaba na ke faɗuwa ba, tun da ta shigo hankalina yaƙi kwanciya" acewar Yasmin, Hibba tace"Ae ba ke ka ɗai ba, ni kaina ƙiris ya rage in saki fitsari a wando, matar can bala'e ce' Kowa yana tofa albarkacin bakin shi
"Amma wai ya akai da ta shiga toilet din bata ga komai ba? Kuma har ta ga Tukunyar fulawar"? Naufal nai yai tambayar mamaki ya ishe shi
"Ae Allah muka roƙo shine ya makantar da ita, shiyasa bata ga komai ba" Deeja ce tai maganar,
"Pls kudaina maganar nan kada Suji mu tunda suna ganin mu, Inaso mu yi magana amma dole mu jira zuwa anjima idan marece Ya nutsa, sai mu shiga sashen toilet dinmu saboda idan su ka ga zaryar Tayi yawa zasu fahimci wani abu" Atare suka hada baki wurin furta mata "Toh"
"Yanzu kowa yaje ya kwanta, Inaso ku huta, kafin zuwa anjima " ɗaya bayan ɗaya suka nufi gadajen su tare da haye saman suka kwakkwanta, Mutun uku ya rage a tsaye, Zuciyoyin A cunkushe suke da tunanin taya zasu Iya 6alle murfin ƙofar nan? Taya zasu iya Gano Danish? Fatansu Allah yasa adawo masu da shi ba tare da sun sha wahala ba, A tunanin su Haris kenan su da basu san komai game da zamanshi giant ba.
Mutun uku da suka rage atsaye Gabriel ne sai Batul tare da Angel, Sunƙi tafiya ga dukkan alamu suna buƙatar jin wani bayani ne daga gare ta.
Kallon su ta ɗanyi kafin ta soma magana "Gabriel nasan me ka ke son ji, Ka ƙara haƙuri zan yi maka bayanin komai" amsa mata yai da toh tare da juyawa ya nufi gadon shi.
"bugun zuciyata me kike tunani ne"? Lumshe ido batul ta yi tare da ware su kan fuskar Angel"har yanzu ban fahimci komai ba, dangane da abunda ya faru da ɗan uwana Danish, hankalina bai kwanta da abunda kika faɗa mini ya faru dashi,"
Matsawa Angel tayi kusa da ita sosai har numfashinsu na kokawa dana juna
"Kin damu dashi"? Jinjina mata kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa"taya bazan damu dashi ba Angel, bakisan yadda nake jin shi acikin zuciyata ba, da ace ina da hanyar da zanbi inje gare shi nothing would stop me from going."
Angel ba ta yi mamakin jin abunda batul tace mata ba, saboda sanin irin shaƙuwar dake a tsakaninsu, Hakan yasa ma taƙi sanar da ita cewa Ya zama Giant, gudun kada ta sanya damuwa
Ruwan hawayen da ya taru acikin idonta ne yaci gaba da gangarowa
"Ki kwantar da hankalin ki bana son kina shedding tears din ki, Ko dan saboda farin Cikin ki zan yi ƙoƙari wurin ganin Danish ya dawo gare mu," kwantar da kanta tayi saman kafaɗar Angel taci gaba da yin shessheƙar kuka tana faɗin"Amma ai bashi da lafiya, An cire mashi ido ɗaya, bansan awani hali yake ciki ba, "
"Ki daina kuka batul so kike hankalinsu Ya ƙara tashi? Nace ma ki lafiyar shi ƙalau shi da kanshi Ya faɗa mini cewa babu abunda ya samu idonshi"
lallashinta Angel taci gaba dayi har saida ta samu ta lafa, Abun da yaɗaure ma Angel kai, zazza6in da taji a jikin batul lokacin da ta kwantar da kanta saman kafadarta, Jikinta zafi sosai.
Hannayenta biyu ta ɗaura saman shoulders ɗin batul, ta ɗago da kanta, Idanuwansu acikin na juna,
"Baki da lafiya ne?naji jikin ki da zafi"? Muryarta adisashe ta ce"Lafiyata qalou, idan ma bani da lafiya damuwar rashin Danish ne" shiru Angel tayi kamar an ɗauke mata sautin muryarta, ta rasa tunanin me za ta yi, Ruƙo hannun batul tayi acikin nata
Calmly tace "You need to take a bath, mu je in raka ki toilet, girgiza kai batul tayi"A'a bana iya wanka, nafi so na kwanta zuwa anjima idan na tashi zanyi,"
Gyaɗa kai Angel tayi"shikenan muje mu kwanta da anjima nima zanyi wankan"
Atare suka nufi gadajen su, tafiya su ke yi kamar waɗanda aka zarewa laka, babu kuzari a jikin kowaccensu, Ita dai Angel akwai wani abu dake damunta acan ƙasan zuciyarta, Fatan ta Allah yasa hasashenta karya zama gaskiya don kuwa ba ƙaramar matsala za'a samu ba.
Ta yi niyar ta kwanta asaman Gadon Danish ganin Jemimah kwance saman nata gadon, sai dai kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta batul ta riga ta kwanciya saman gadonshi, da ido ta bita da kallo ganin ta rungume pillow dinshi a ƙirjinta tare da lumshe idanuwanta, Jiri Angel ta gani acikin idanuwanta kamar zata faɗi kasa adaddafe ta nufi gadonta daƙyar ta haye gefen jemimah ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya, lokaci ɗaya ta ji yanayin jikinta ya canza zuwa zazza6i, hakan yasa ta soma ambaton sunan Allah, sama sama ta fara jin bacci yana fisgarta har ya ci nasara akanta sosai ta nutsa tana bacci...............
Ɗakin ya yi tsit babu mai magana a cikin su, kamar masu bacci alhalin kuwa likimo su ka yi, sai da marece ya nutsa Angel ta umarce su akan su je su yi wanka saboda wunin ranar jikin su baiga ruwa ba, ba tare da 6ata lokaci ba kowannansu Yayi wanka, ta ɗauko masu sababbin uniform ɗinsu kowa ya zura nashi a jikin shi, tsaffin kuma suka cire su Angel ta kar6esu ta ninke su ta ajiye saman table.
Lokacin da dare ya gabato, dubara su ka yi wurin kashe Floor lamps ɗin da ke a ƙasan ɗakin su, Duhu Ya mamaye idanuwansu, saboda sabon da su ka yi da ɗakin yasa su ke iya gane hanya ko a cikin duhu, Kamar yarda Angel ta tsara masu mutun Uku ne zasu Haɗa masu kayan su A cikin akwatin da zasu gudu da shi, Rai da burin sufa shirin matafiya su ke yi tun kafin su gano Makullin Buɗe ƙofa, Babu wanda yai bacci acikin su Hatta Jemimah idonta biyu tun ɗazu da marece da ta farka Angel tayi mata bayanin komai dangane da gano ƙofa da kuma shirin su na guduwa, abunda yasa tayi mata bayani don kada ta basu matsala, da ya ke yarinyar tana da wayau ta fahimce ta sosai, yanzu haka suna kwance saman gadon Angel ita da azeeza sun rungume juna sunata saƙa wasiƙar jaki game da rayuwar da za su yi agidan daddyn Genie ɗinta.
Sauran Ƴan uwan nasu duk suna a zaune gefen gadajen su, duk wani motsin su Angel akan kunnuwansu.
"Bamu san Girman ƙofar ba Angel Kada mu gaza wuce wa da akwatin kayan mu" Gabriel ne yai maganar, Cikin duhu suke magana, zurfin tunani ta yi acikin kwakwalwarta, A Labarin da Salsabeel ya bata Na mahaifin shi habibullah ya tabbatar mata da cewa Ƙofar sai da rarrafe mutun zai Iya giftawa ta cikinta, mutun zai Iya rarrafawa ko ya zauna, Amma babu zancen miƙewa tsaye, abun zai zo masu da sauƙi tun da basu da girman jiki, yawancinsu dogaye ne amma babu ƙiba, haris ɗin ma da ke da jiki yanzu ya zabge ya koma kamar su Javed.
"Ae akwatin zamu Iya kwantar dashi mu dinga tura shi ta cikin hanyar, Ni abunda nake Jiye mana kada mu kwasa mu tafi zai Iya kasancewa ƙurmin daji ne bamusan ya weather ɗin shi zai kasance ba, Zafi ko Sanyi, Zamu sha wahala akwai sanyin da ma zai Iya kisa Haka zafi ma, Ni nafi so mu tafi da bargunan mu saboda tsaro, shiyasa nake so mu ɗauki akwati ɗaya sai Backpack ɗin Unaiza dole mu tafi da ita saboda gadon mu ce.
Duk maganganun da suke tattaunawa cikin duhu akan kunnan ƴan uwansu da ke zaune gefen gado Sun natsu suna sauraron su.
"Mu fara ɗaukar uniform ɗin mu jera su ciki, " batul ce tai maganar, Angel tace"Ki je toilet ki ɗauko mana fitila ɗaya amma ki fara kashe ta tun acan dan kada su gan mu, a ɗakin tsohuwa tamira zamu aiwatar da komai" ta amsa mata da toh, kafin ta nufi hanyar sashen toilet ɗinsu cikin duhu har ta samu ta cimma ƙofar makewayin nasu, da hannu ta tura ƙofar ta kutsa kai ciki ta shiga ta ɗauko fitilar tare da kashe ta, Kafin ta dawo ɗakin tunkan ta ƙaraso tace dasu gata nan tafe, Ruƙo hannunta Angel tayi acikin nata ta kuma ruƙo hannun Gabriel da ɗayan hannun atare suka shige ɗakin tsohuwa tamira,