← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 152

Sashe 116

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tunda suka zauna Unaisah ta kasa samun sukuni, yanayinta tamkar na mara lafiya, sai faman jujjuya spoon take Yi acikin plate din gabanta, da ke shaƙe da abinci, damuwar duniya ta isheta, sam babu sukuni akan fuskarta, A hankali ta ɗago da ido tana duban fuskokin Ƴan uwanta, tun daga kan Sajeed dake fuskantar Azeeza, suna cin abinci suna kallon juna, har zuwa kan Haris dake fuskantar Hannah, kafin ta kawar da idonta daga kansu ta maida su kan fuskar Naufal da javed, sun natsu suna cin abincinsu, hasken musulunci ya fara shigarsu, komai nasu cikin natsuwa suke yin shi, mayar da idanuwanta tayi akan face din jamimah, bakinta duk ya 6aci da maiƙo, ta samu cinyar kaza saici take Yi kamar tsohuwar mayya, ta cinye tsokar naman, Ƙashin take gwaigwaya kamar babu sauran naman alhalin gashinan saman tray guda aka jera masu chicken legs, girgiza kai tayi kafin ta mayar da dubanta kan Batul dake gefenta, ita dai duniya babu abunda ke burgeta irin taliyar indomie, tun ranar farko data fara cinta, kullum ne in zasu ci abinci saita ci ta, sam bata gajiya, da hannu take nannaɗota kafin ta tura abaki, rantane ya raya mata ana kallonta, dai dai time dinda ta tura taliyar abaki ta ɗago da ido suka kalli juna ita da Angel, da sauri ta haɗiya taliyar, cikin muryar raɗa ta tambayeta lafiya take kallonta? Ko tayi ƙauyancine”? Girgiza kai Angel tayi babu komai kawai burgeni kikeyi idan kina cin noodles da hannu”
Gyaran murya ummi tayi masu atare suka ɗago suna kallonta.
“Unaisa tun ɗazu na lura kamar bakya jin daɗi, meke damunki ne”? Murmushin yaƙe ta sakar mata”babu komai aunty ummi, ko kinga wani abu ne” ɗaga mata gira tai”ƙwarai kuwa, tun da gashinan kin kasa cin abincinki”
Kafin unaisa ta ƙara furta wani abu, Muryar Haris ta katse su
“Kodai Danish bashi da lafiyane? Tun jiya da rana ban ƙara ganin ya leƙo waje ba, naso naje na duba shi sai dai karatu Ya mantar da nayi yin hakan”
Cikin nuna damuwa Sajeed yace”wallahi yana araina, tun ɗazu da muna awurin kar6ar karatu nake ta tunaninshi, bansan dalilin dayasa baya son zuwa cikin mu cin abinci ba, naga dazu da rana ke kika kai mashi lunch dinshi a dakin shi” ya faɗa yana nuna Unaisah da spoon din hannunshi.
Naufal Yace”to me zai hana mu tashi muje ɗakin nashi mu duba su? Ni abunda ke damuna da danish baya son sakewa cikin mutane” Yai maganar fuskarshi dauke da damuwa.
Javed yace”ai halinshine tun fil azal, kaima kasan Danish bai cika son zama cikin mutane ba, baison surutu kuma baison ana kallon shi”
Gyaran murya Ummi tai masu, Hankalinsu Ya dawo kanta sun natsu suna jiran jin me zatace
“Koda ace halinshi ne hakan bai kamata ku ƙyale shi ba, cos barinshi acikin ɗaki zai Iya haifar mashi da wata damuwar, duk da naga Unaisah tana ƙoƙarin dubashi, amma a ƙalla yakamata kuma kuna zuwa wurinshi kodan ku dinga ɗebe mashi kewa, kafin zuwa lokacin da zai saki jikinshi, nasan rashin sabone ke damun shi”
Jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da bayaninta, Sajeed yace”ku tashi muje dakinshi Inyaso sai mu tafi da kayan abincin mu ƙarasa ci acan” Yai maganar tare da miƙewa, da sauri Unaisa tace”a’a basai mun tafi mu duka ba, Ku zauna ni zanje in taho da shi” amsa mata sukayi da toh, da sauri ta miƙe ta nufi ƙofar fita daga dining room din
Miƙewa Batul tayi Ummi tace Ina zuwa? Cikin sanyin murya tace ina so zanbi Unaisah ne”
“Ki koma ki zauna, ai tace zasu dawo atare dashi ko”? Amsa mata tai da toh jiki asanyaye ta koma ta zauna.
Shiru suka ɗanyi, abincinma sun dakata da cin shi, hakanan suke jin zuciyoyinsu na bugawa, Jemimah kadaice ke cin abinci ta cika masu kunnuwa da sautin taunar abincinta, da gangan take yi duk don ayi mata magana.
Harara Azeeza ta watsa mata”dan Allah ya isa haka, ba zaki Iya ci a hankali bane”? Hanna tace”ki daina wahalar da bakinki, dagangan take yi duk don ayi mata magana” tuntsirewa tayi da dariya tana fadin”Eh din kuma gashi kunyi min maganar ba” girgiza kai ummi tayi fuskarta dauke da murmushi take dubanta, hankalinta kwance take yin magana. Kallon da naufal ya jefa matane yasa tai shiru tana ƴan ƙunƙuni.
“Kuna burgeni, gaba ɗayanku” ta fada tana nuna su da spoon din hannunta.
Batul tace”aunty ummi, kina nufin kina sonmu”? Jinjina mata kai tayi”haka nake nufi,” murmushi su naufal suka saki jin abunda tace,
Parveen na faman siɗar hannu tace”Aunty ummi ke baki haifi ƴa’ƴa bane, kamar yadda daddyn unaisah ya haife ta? Ko kuwa ita mace bata haihuwane sai maza”? Da mamaki Ummi ta dan zaro ido tana kallon parveen da tayi maganar, sam babu wasa akan fuskarta ita bilhakki take Yin maganarta.
“Amma baki da hankali parveen, Kin manta labarin da unaisa ta ta6a faɗa mana ne? Macace take haihuwa ba namiji ba, itama Mommyntane ta haifeta ta jefar da ita cikin wannan abun kalar na toilet din gidan nan, namanta sunanshi” Batul ce tai maganar,
Azeeza tace”eh kuwa hakane, Macace ta haifi unaisa ba namiji ba, to aunty ummi ke kin ta6a haihuwa”? tayi tambayar tana kallon ummin america wadda mamaki da al’ajabi suka cikata, sai kallonsu take Yi ɗaya bayan ɗaya, sajeed Ya duƙar da kanshi ƙasa sai faman sakin murmushi yake Yi jin wautar parveen.
“Aunty ummi kinyi shiru baki ce komai ba, kina ta kallonmu” Hanna ce ta jefa mata tambayar, ta ƙura masu ido tana binsu da kallon mamaki,
“wai kuna nufin bakusan komai ba, game da zamantakewar aure?
Atare suka haɗa baki wurin furta”Aure kuma”? Gudun kada suyi wata 6aran 6aramar yasa Sajeed yin saurin cewa”aunty Ummi, Yakamata mu maida hankali akan abunda muke Yi yanzu,” Ta6e baki taɗanyi kafin ta furta”okey, “ ta fahimci baison maganar dama ta lura yafi su hankali shida Unaisah, bata ta6a ƙagara da sonjin labarinsu ba sai yau, tabbas tana son tasan tarihin rayuwarsu! Ya akai har suka kai wannan shekarun basusan komai dangane da zamantakewar aure ba? batun Yauba ta lura da ƙarancin wayewarsu, kamar babu ƙwalwa akansu, basu iya komai ba, In banda cin abinci da kwanciya bacci sunfi ƙwarewa a 6angaren nan.

_(Ummin america batasan su wanene prisoners ba, Mutanan da suka juri rayuwar kulle tun suna jarirai, basu ta6a ganin hasken rana ba, dare da rana basu da abunyi daya wuce idan ankawo masu abinci sau ɗaya suci sai kuma idan lokacin baccin su Yayi su kwanta, badan Allah Ya ƙaddara zuwan unaisah kurkukun ƙaddara ba, da kuwa abunda zasu aikata sai yafi hakan saboda su din tamkar baƙine a duniyar mutane, basusan komai ba, unaisah itace ta wayar masu da kansu dangane da mutanan duniya da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan adam shiyasa ma har suke Iya sakin jiki suyi rayuwa acikinsu)_

Shin meya faru bayan Unaisah ta fita daga Dining room?

Cikin sauri ta nufi upstair, tunkafin ta ƙarasa ƙofar ɗakin danish ta dinga jin faɗuwar gaba, tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, jiki na rawa ta nufi ƙofar room dinshi, zura ƙafarta keda wuya cikin ɗakin, taga babu kowa wayam har saman gadonshi babu mutun, sai faman baza ido take Yi tana faman ambaton sunanshi tamkar makoshinta zai 6allo”Danish! danish! my Man! Kana ina”? Shiru babu alamun zai amsa mata, ƙofar toilet dinshi ta tunkara lokaci ɗaya taji sautin gurnaninshi mai matuƙar firgitarwa ya cika ɗakin, cikin jin faɗuwar gaba ta sanya hannayenta biyu da ƙarfi ta ingiza ƙofar ta buɗe, tun daga bakin ƙofar toilet din ta ci karo da singlet dinshi, A hankali take bin ko’ina da kallo har tayi nasarar cin karo dashi kwance acikin kwamin wanka, wanda ke akewaye da glass, ya ƙunshe kanshi cikin kwamin, jikinshi sai kerma yake yi, faɗawa cikin toilet din tayi, Cikin sanyin murya take fadin”My man meke damunka? Meyasa kake yin gurnani? Baka da lafiyane” idanuwanshi dake a lumshe ya buɗesu sun kaɗa jawur dasu tamkar an wanke ƙwayar a cikin jini, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata damu da yanayin da zata riske shi ba, Jiki amace ta shiga inda kwamin yake ta zuƙunna agabanshi tana dubanshi, fatarshi tayi wani irin haske naban mamaki, Ya cika kwamin da ruwa mai sanyi, amma saboda tsabar zafin jikinshi yasa ruwan ya koma na zafi.
Chapter 116 · 0% Book details