← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 152

Sashe 111

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wuraren ƙarfe huɗu da rabi Estate din Ya cika maƙil da mutane babu masaka tsinke, manya mutane masu faɗa aji duk sun hallara, kama daga Ƴa’ƴan jam’iyarsu ta Action progressive party ministoci, sanatoci, gomnoni, da sauransu, Kowannansu Ya ɗauki wankan expensive shadda ta kece raini na shiga tsara, jikokin Obinna Na ƙasa nigeria da wadanda ma basa ƙasar saboda shagalin nan sun dawo Nigeria A yau din nan, daga cikinsu akwai ya’yan sir mubarak mazauna kasar canada, zaratan samari Zaki shine babban ɗanshi mai bi mashi Ibad, bayansu sai ƴa’ƴan His excellency abdul razak, babban danshi Yasir, tare da ƙanwarshi Yusra, sunzo ne tare da mahaifiyarsu Her excellency hajiya muhibbat, bayan su sai Ya’yan his excellency Deen, babban ɗanshi Justice Nadeem mai bi mashi Dr. nawaz tare da mahaifiyarsu suka zo Her excellency hajiya Jamila, bayansu kuma sai ƴar gidan mai girma sharafudden Hindu ƙanwar Chief Owais, tare da matayanshi suka zo Hajiya Malikat sarauta uwar gidanshi da kishiyarta Hajiya laurat, da kuma ƴar wurin Lateef zulaihat kanwar ziyad, gaba ɗayansu dai kowa Ya hallara ga yan matan hateem Nazli and Yazrin, gaba ɗaya matan sun ɗauki wankan Swiss cord lace yayi bala’en Yi masu kyau, A babban hall din dake acikin gidan aka gudanar da shagalin, An ƙawata cikinsa da kayan alatu, ko’ina ka kalla furannine da ƙyalƙyalin sparkling chandeliers, ga Banquet chairs da aka tanada domin baki su zauna, kowani table saman shi an ɗaura bouquet of flowers, tare da Crystal glasses and silverware, da sauransu, floor din hall din kuwa an shimfiɗe shi da ƙayataccen red carpet, daga can gaban hall din Gingirimeman Cake stand ne an ƙawata shi sosai, Mawaƙa da makaɗa hada maroƙa sun hallara, domin suma su kwashi rabonsu, an shirya kayan abinci saman zungureran table kala daban daban, sai mutun Ya za6a ya darje, duk haɗuwar taron nan mutun ɗayane bai hallaraba, Hakan ba ƙaramin ta6a zuciyar obie yai na, Yaci buri akan zuwanshi amma shiru babu shi babu alamarshi, mutane sai tambayar shi suke Yi, ya akai basu ganshi ba? Iyayenshi sun rasa amsar dazasu basu, sai dai suka dinga cewa bai kaiga zuwa ƙasar ba, farin jini gare shi shiyasa duk wanda yazo sai ya tambayi ina owais Yake, Taro Yayi albarka, Anci ansha anyi kullu wash rabu hani’an, Anyi harka ta arziƙi ta kece raini, daruruwan mutanan dasuka kawo mashi kyauta taban mamaki basu ƙirgiwa, baba obie Ya mori lokacin shi, Yayi farin cikin dabazai Iya misalta shi ba, Ƴan uwa da abokanan arziƙi sun faranta mashi rai, sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, Sun taka rawar girma, sai dai muce Alhamdulillah taro Ya tashi Lafiya, gab da magrib baƙi suka ragu waɗanda suka rage ƴan uwane na jini, da kuma mutanan Hateem.

*WAIWAYE ADON TAFIYA💫*

(Abunda ya faru bayan zahra ta faɗa ma Aneelerh halin da take aciki, Na kuɗi da hajiya falmata take binta bashi, bayan ta koma ɗaki damuwa ta isheta, tayi ƙarfin haline kawai wurin bata shawara akan ta amince da buƙatar hajiya falmata saboda tana son ta jaraba zahra ne don taga idan tana da hankali, tunani ta soma yi ta wace hanya zata Iya taimakonta? Nan take zuciyarta ta bata shawarar tayi amfani da sauran kuɗin nan da jami’an sirri suka bata, har yau bata ƙarar dasu ba, tamkar tana jin tsoron ta6a su, tun dai data siya ma baby junaid kayan wasa bata ƙara cirar ko naira biyar ba.

Ba tare da sanin kowa ba Aneelerh ta tuntu6i mahboob, a ɗakin shi ta same shi, ta tambaye shi koya san gidan hajiya falmata mahaifiyar ƙawar zahra? Yace mata eh yasan gidan, sun ta6a zuwa tare da zahran ma, tace toh so nake ka rakani gidan, da mamaki akan fuskarshi yace amma me zakiyi acan din kinsan ta ne? girgiza mashi kai tay alamar a’a, kawai inaso ka rakani muje, idan mun fita zan faɗa maka komai, amma kafin muje gidan zaka fara rakani banki, akwai wasu kuɗi da nakeson in cira, Jin ta ambaci kuɗi yasa mahboob saurin amincewa zai kaita gidan, a cikin motarshi ya dauki aneeleeh saida suka fara biyawa banki ta ciri kuɗin kafin suka nufi gidan hajiya falmata.

Lokacin da suka karasa gidan, A parking space mahboob Ya tsayar da motar, Aneelerh tace dashi ya jirata anan, ya amsa mata da toh, da sallama abakinta ta shiga palourn gidan, adai dai lokacin mai aikin gidan ta fito daga kitchen ta yi arba da aneelerh, fuskarta da fara’a suka gaisa tace mata wurin hajiya falmata tazo, Allah yasa tana nan, Mai aikin tace bata jima da dawowa daga office ba, ki zauna bari naje in sanar da ita, da sauri mai aikin taje ta fado mata, jim kadan ta dawo ta sanar da aneelerh sakon hajiya tace ta jirata gata nan zuwa, aneelerh ta amsa mata da toh, kusan mintuna biyar Aneelerh tana a tsaye ta ruƙe qugu tana jiran fitowarta, cikin jin fargabar ganin matar, sai faman bin palourn take yi da kallo.

Sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin Aneeleerh ga kallonta, A hankali take saukowa down stair, ta ɗauki wankan tsadaddan leshi, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali, ta manna farin glass a idonta, Babbar macace tana da jiki, tana tafiya tsokokin jikinta na motsawa, Fatar jikinta tasha hutu har ta gaji, daga ganin fuskarta masifaffiyace, idanuwanta mitsi mitsi da su kamar na mutanan Yankin china, hancinta kuwa abaje yake, ga big mouth dinta yasha man baki.

Ta6e baki Aneeleerh tayi aranta ta furta jibarta dan Allah, ƙatuwar banza da ita kamar buhun masara, a haka take lalata rayuwar matasan ƴan mata, Allah dai ya shirya, wasu mutanan sunyi asarar rayuwarsu.

Lokacin da hajiya falmata ta ƙarasa saukowa daga saman benan, idanuwanta suka Yi mata tozali da kyakkyawar fuskar Aneelerh nan take taji ta burgeta, tayi mamakin ganin baƙuwar fuska agidanta, bakomai yafi tafiya da imaninta ba face Kyawun surar Aneelerh.

Ganin Yadda Ta tsareta da idone Yasa Aneelerh tayi saurin gyara mayafinta ta rurrufe jikinta, Aranta ta furta A’uzubillahi minasshaidanirrajin, Aniyarki ta biki baƙar mayya”
Saman sofa din dake fuskantar Aneelerh Hajiya ta zauna, tana dubanta da wani irin mayataccen kallo.

Yamutsa fuska Aneelerh tayi fuskarta ba wasa tace”barka da Yamma”
Hajiya falmata ta amsa mata da”barka dai, bismillah ki zauna mana”

Ɗaure fuska Aneela tayi”bana zama agidan da ake aikata sa6on Allah, saboda ni tsarkakakkiya ce, bai kamata in goga ma jikina najasa ba”!! Mamakine Ya kama hajiya falmata, a hankali ta sauke glass din dake saman fuskarta don ta samu damar ƙarewa Aneelerh kallo.

“Bansan wacece ke ba, sai dai na fahimci haukan talauci ne ke damunki shiyasa kika kwaso ƙafa kika zo gidana don in taimaka maki”

Dariyar rainin wayau Aneelarh Tayi kafin tace”ki kalleni daga ƙasa har sama, kema kinsan nafi ƙarfin ki kira ni da talauci, Ni banzo don nayi cece kuce dake ba saboda bani da lokacinki, Maganar kudin zahra da kike bin ta bashi ne”
Shu’umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar Hajiya falmata da shaƙiyanci ta furta”oh, kinzo ne ki fanshe ta, shiyasa kika kawo min kanki? Donni banga alamun zaki Iya biyan kuɗin ba”
Girgiza kai Aneelerh tayi ranta a6ace tace”wato shi dai jaki duk yadda akai dashi sai yaci kara, idan kina tunanin na kawo maki kaina ne don in fanshi zarah to ki daina, domin kuwa nafi ƙarfin ƙasƙantacciyar mace ballagaza jahila kuma daƙiƙiya irinki, Mace mara tsoron Allah, me yin amfani da dukiyarta don lalata rayuwar matasan ƴan mata masu neman nakansu, Wlh kinji haushin rayuwar......” gigitacciyar tsawa Hajiya falmata ta daka ma Aneelerh, tamkar damusa ta yunƙura ta miƙe tsaye tana duban Aneelerh da mummunar fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin ta nuna mata Hanyar fita da yatsan hannunta”Ke Fuce kibar min gidana, tunkafin ranki Ya 6aci, matsiyaciyar banza masu ƙashin tsiya”
Chapter 111 · 0% Book details