Sashe 86
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da jirgin Ya soma tafiya Yana bin hanya kafin Ya ɗaga sama, Hankalinsu Azeeza ba ƙaramin tashi yai ba, jami’an Sunyi ƙoƙarin kwantar masu da hankali, ganin yadda su ka ruɗe jikin su ya hau yin kerma, sun fahimci mugun tsoro ne da su, Angel ce ta tunasar dasu akan suyi addu’a, aiko atare suka hada baki suna karanta addu’o’in data koya masu.
Cikin ƙanƙanin lokacin jirgin Ya ɗaga sama Ya keta hazo can cikin sararin samaniya, Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke kamar an yaye masu tsoron da suke Ji, hankalin kowan nan su ya kwanta tun da aka kunna masu kallo a tv, ban da na Angel, Yanayin fuskarta ya canza, sakamakon maganganun da taji Danish yana furta mata acikin kunnanta, muryarshi arauna ce yake fadin baya son mutane, haushin su yake ji, yana ji kamar ya kashe su, jinin su yake sha” ƴan hanjin cikin ta ba ƙaramin kaɗawa su ka yi ba, sai faman zazzare ido take yi, babu wanda ya lura da halin da take a ciki, sauƙin ma acikin kunne yake yi mata raɗa, sautin muryar baya fita, kuma akwai tazara tsakanin seats dinsu dana sauran ƴan uwansu, ɗaya daga cikin jami’an isod ne Ya ɗauko mashi eye mask ya miƙa ma Angel don ta sanya mashi a tunanin shi hasken jirgin ke bayaso shiyasa ya cusa kanshi saman kafadar Angel may be ko yana son ya runtsa ne.
Tun da ta sanya mashi eye mask taji yayi shiru ya daina magana alamar bacci ya dauke shi, a ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirga, addu’o’i taci gaba da karanto mashi tana tottofa mashi saman sumar kanshi, fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane zai faru da shi, gashi ta manta bata nemi takardar dake ɗauke da address din gidansu salsabeel, duk da bata tunanin ma ko sunje zasu samu abunda suke so.
A Kishingiɗe yake saman shimfiɗeɗan full-sized bed dinsa dake acikin privet room na jirgin, ya ɗaura kansa saman tattausan pillow, Shin wanene wannan kyakkyawan matashin saurayin? A jin farko afagen kyau da ƙasaita, Namijin duniya, A halitta madai-dai ci ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, Vest din jikinsa tayi tighting dinsa, kana iya ganin zanen ƙirjinsa, Ko ɗan wrestling bazai nuna mashi ƙirar ƙarfi ba, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, mutun ne mai ji da ƙarfi, Allah yabasa kyawawan idanuwa farare tass ga su so sexy, masu ɗauke da launin ƙwayar ido reddish brown, har shining suke yi, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda Yana da yalwatacciyar suma, lallausar sumar kanshi tasha gyara anyi mashi Military haircut yayi bala’en yi mashi kyau, abun da yafi komai jan hankali a jikin shi tsadaddiyar launin fatar shi, chocolate colour, har wani glowing take yi, hutu ya zauna mashi, jikinshi ya wanku da dollar, duk inda namiji yakai to ya zarce nan, komai nashi na kece raini ne ba wasa a tattare dashi, kuma burin kowace ƴa mace ne shi, a 6angaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, su kan su kuɗin raina kansu suke yi agabanshi, duk da tarin dukiyarsa baida girman girka, mutum ne shi da bai ɗauki duniya da zafi ba, Allah ya bashi kaifin basira, Yana da ilmin addini dana zamani, ta ko’ina Allah ya hore mashi, yana matuƙar jin ƙan talaka, Yana da tausayi ga son taimako, shi sam abun hannunshi bai rufe mashi ido ba, kyawawan halayansa da ɗabi’unsa abun burgewa ne, shiyasa ya fita daban ko acikin jikokin family ɗinsu, ya shahara aduniya sosai, babu inda ba’a sanshi ba, mutane basa gajiya da yabon shi, burin kowane ya yi tozali da shi, babban abunda ya tsana a duniyar nan shi ne yaga mugun mutun mara imani acikin mutane Yana zalunci, In kuwa ya damƙi irin su, mai ƙwatar su sai Allah, shiyasa mutane masu irin halin suke mugun jin shakkar shi, dai dai da sunan shi aka fada sai gabansu ya fadi, don baya yi masu da kyau, ni nasan bazan Iya misalta ƙasaitaccen Namijin nan ba, Kaɗan ne na Iya faɗa maku sauran ku biyo ni acikin labarin, Yanzu ne wasan Ya fara.
Tun da ya ɗaura lumsassun idanuwanshi akan tsadaddar laptop din gabanshi ƙirar Apple macbook pro bai ƙyafta idon shi ba, Hannun shi na dama na sanye da wrist watch ƙirar Rolex submariner haɗaɗɗar gaske, ya tattara dukkan natsuwar shi akan abun da yake kallo, duk wani motsin prisoners dake acikin jirgin yana kallon su ta cikin laptop dinsa, Ƙayataccen table din dake agaban gadon shi ɗauke ya ke da Mug na cofee ga fresh fruit da aka ajiye mashi, daga gefen shi saman mattress, suit jacket dinsa ce daya cire launin Navy blue, trouser din ta ne a jikin shi, hankali a kwance bai da wata damuwa.
Awanni da suka ɗauka acikin jirgin ba ƙaramin daɗi suka ji ba, saboda an gatanta su, sunci abinci har sau biyu, sun yi bacci sun tashi, komai suke so yi masu ake yi, Danish ne kaɗai baici komai ba, tun da bacci ya ɗauke shi bai farka ba.
*💋ABBAN SOJOJI💋*
*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za’a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature*
*✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_
~Middle step~
سجن القدر❤🤍❤
_THE PRISONERS E26🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
Confusion of the heart💫
Tun da Aneelerh ta turawa numbar saƙo har yau ba’a tuntu6eta ba, abun ya dame ta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kullum ne sai ta ƙara jaraba kiran layin ko za’aci sa’a mamallakin wayar ya ɗaga amma wani iko na Allah a kashe take samun layin duk ta damu da son jin wanene.
Fitowa ta yi daga cikin ɗakinta hannunta ruƙe da wayarta, ɗakin zahra ta nufa da niyar ta faɗa mata halin da take ciki wata’kil ta bata shawara akan abun da ke damunta.
A bakin ƙofar ɗakin ta fara yin sallama, shiru ba’a amsa mata ba, kusan sau uku tana kwaɗa sallama zahra bata amsa ba, tunani ta soma yi ko dai ta koma wurin aiki ne? Ko kuwa baccin lalacin da ta saba yi ne, wata’ƙil kuma wanka ta shiga.
Haura ƙafa ta yi ta shiga ɗakin zahra, tun abakin ƙofar room din ta fara cin karo da takalmanta da jakarta da mayafin ta gaba ɗaya ta watso su saman floor, nan take hankalin Aneelerh ya tashi da sauri ta ɗago da ido tana kallon gadonta, duvet dinta da pillow dinta duk ta watso su ƙasa, Komai na ɗakin ta tarwatsa shi.
Aneelerh ta fahimci babu lafiya wani abu ya faru da ita, Zahra da ta sani Mai tsafta dagangan dai bazata ta6a barin ɗakinta a hargitse ba.
Cikin tashin hankali ta soma ƙwala mata kira”Zahra! zahra!!” shiru babu amsa, ranta ne Ya bata cewar ko dai bata agidan ne ko kuma ta shiga ɗakin ummi, da sauri Aneelerh ta fuce daga ɗakin, Har zata gifta ta falo ta wutsiyar ido ta hango Mami da ummi zaune suna fira, juyawa tayi da sauri ta nufe su, babu wanda Ya lura da ita acikinsu har saida ta furta”ummi mami Ina zahra” kusan atare suka ɗago suna kallonta, gaba daya sun fahimci babu kwanciyar hankali atattare da ita.
Ummi tace”kin duba ɗakinta baki ganta ba”?
Kafin ta bata amsa mami tace”Aneelerh wai lafiya? Ya akai naga kamar bakya acikin natsuwarki”
Muryarta na ɗan rawa ta furta”bakomai, na duba ɗakin zahra ne ban ganta ba”
Mami tace”shine duk kika ɗaga hankalin ki? Sai kace yau ta fara fita daga gidan, kema kinsan zahra idan har ba wurin aiki taje ba toh tana acikin gida”
Ummi tace”tun ɗazu fa ta dawo, ki kwantar da hankalin ki, bata wuce cikin ɗakinta, Ki koma ki sake dubawa”
Juyawa tayi da sauri ta nufi ɗakin donta ƙara dubawa.
Bayan tafiyarta ummi ta dubi mami”ƙawancen Aneelerh da zahra ba ƙaramin burgeni ya ke yi ba, har mamaki nake yi idan naga yadda Aneelerh take jan zahra a jiki, duk da ta girme ta”
Mami na murmushi tace”ai shi ƙawance ba a shekaru yake ba, indai mutum Ya mallaki hankalin shi ko da ya girme ka zaka Iya ƙawance da shi, Ni kaina ba ƙaramin burgeni suke Yi ba, Allah dai Ya bar zumunci”
Ummi tace Ameen ameen.
Daga haka su ka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.
Afujajen Aneelerh ta faɗo ɗakin zahra tana faman Yin haki, ta kware murya tana ambaton sunanta”Zahra! zahra! Nasan kina jina, Dan Allah kiyi mini magana”
Still babu alamar za’a tanka mata, ranta ne ya bata cewar wata’ƙil ta fita ne ba tare da sanin kowa ba, Har ta juya zata fuce daga ɗakin ba zato ba tsammani ta soma jin shessheƙar kukan zahra, da sauri Aneelerh taci burki, a sukwane Ta juya tana bin ko’ina na ɗakin da kallo, a ƙoƙarinta nata gano inda zahra ta 6uya, hankalinta yafi karkata akan toilet din ɗakin, da sauri ta ƙarasa bakin kofar ta kara kunnanta, sosai take jin kukan zahra mai matuƙar tsuma zuciya.
Muryarta na rawa ta furta”Zahra meya faru dake? Wanene ya ta6a min ke? Dan Allah ki faɗamin zahra, ashe kina jina shine kika ƙi tanka mun ko?” cikin shessheƙar kuka zahra tace”...Aunty Aneelerh babu abun da ke damuna, kawai bana son kowa ne a kusa dani”