← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 152

Sashe 21

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ni banga alamun hakan ba, pls idan munje mu tafo dashi, tunda ka ga bamu da wani ɗa da zamu dinga kallo muna jin daɗi” fuskarta amarairaice tayi mashi maganar, girgiza mata kai Uncle Abdallah yai”idan mukayi hakan bamuyiwa Mahaifiyarshi adalci ba, ta rasa mijinta yanzu kuma sai mu tada zancen zamu kar6i yaro daga gurinta”? Ɗaure fuska Hajiya adama tayi, ranta ya 6aci”Abdallah baka son farin cikina, Ni zan koma palour wurin mai zanan can” Ta ambaci hakan tare da juyawa a fusace zata tafi, Har takusa kaiwa bakin ƙofa muryarshi ta katse mata hanzarinta”ba zan ta6a manta irin wahalar da nasha kafin na mallake ki a matsayin matata, ta ya ya kike tunanin bana son farin cikin ki”? shiru bata Juyo ta kalle shi ba, idonshi na akan bayanta

“A yanzu haka da ni ke yi ma ki magana, na yi mana cuku cukun komawa can da zama, na samu aiki a babban companyn sharafudeen saboda ba zan Iya raba uwa da ɗanta ba, haka zalika bazan Iya raba kaka da jikanta ba, shiyasa na yanke shawarar komawarmu can, Nasan hankalin ki zaifi kwanciya idan kina ganin shi akai akai” idanuwanta ne suka cuko tab da ƙwallar farin ciki.

Fasa fita ta yi daga Cikin ɗakin, Jiki asanyaye ta nufe shi tare kwantar da kanta saman ƙirjinshi, Hannun shi Ya ɗaura saman bayanta yana cigaba da gayamata daɗaɗan kalamai masu kwantar mata da hankali, tsawon mintuna biyar kafin ta ɗago dakai Tana kallon shi

“Inaso zanyiwa Aneelerh kyautar zanan fuskar Angel da akayi min a south korea, Nasan za ta yi farin ciki saboda tana matuƙar ƙaunarta, kuma zatayi mamakin ganinta a shekarunta na yanzu don inada tabbacin idan har Allah yasa ta bayyana zamu iya ganinta da suffar da mai zanan ya zanata, kasan sun ƙware a iya zane” tana magana Hannunta ruƙe da gaban rigarshi kamar tana gyara mashi ma6allinta

“Idan ki ka bata zanan ke fa? Almost dala dubu ɗari akayi maki shi fa”

murmushi ta ɗan saki”saboda haka yasa nace ka kiramin wani mai zanan ni sai na ɗauke shi,” yace”mai zai hana ki bata sabon zanan da za’ayi ke sai ki ruƙe na koriyan? Girgiza kai ta yi alamar “a’a, Nafison nayi kyauta da abunda yafi kyau da tsada, Farin cikinta kawai nakeso,” yanayin fuskarshi ya nuna tamkar bayason taba Aneelerh zanan fuskar Angel da akayi mata aƙasar korea, ba ta kawo komai aranta ba saboda ta fahinci Son zanan ya ke yi ba don saboda tsadarshi ba.

“Hajiya an kammala” daga Cikin palour su ka jiyo sautin muryar me zanan, da sauri Hajiya adama ta nufi falon uncle abdallah yabi bayanta, tunkan su ƙarasa shiga Ciki idanuwansu suka soma hango masu Kyakkyawar fuskar Angel jikin allon zanan nashi, Tsabar mamakin yadda suffarta ya fito ne yasa su sakin baki, Kamanninta sak dana tajudden Hasken fatarne kaɗai na mahaifiyarta da kuma sumar kanta.

“Wow! Zanan sak kalar na south korewa nayi mamaki! Banbancin kawai tsadar kayan aikin da akayi amfani wurin yin wancan zanan amma wlh yayi kyau over” hajiya adamace take ta sambatun ganin zanan, Shi kanshi uncle abdallah Ya yi mamakin ganin zanan, Suffar Angel sak sai dai an ƙara mata girmanta, takai dai dai age ɗinta na yanzu 15 to 16 years,

Mai zanan yana atsaye yana kallonsu, sai sakin murmushi yake yi jin yadda suke yabon aikinsa

“Ina fata Angel ta bayyana kamar yadda muka ganta a zananta, in har hakan ta faru nayi maka alƙawarin zan ninka maka kuɗinka” fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar tana kallon mai zanan, washe baki yai yana faɗin”In sha Allah ranki ya daɗe ƴar ki zata bayyana kamar yadda na zana ta a hoton nan, kuma ina roƙon Allah yasa zanene ya zama silar ganinta” atare suka amsa mashi da ameen, Kafin tafiyar mai zanan saida suka haɗa mashi sha tara na arziƙi.

*EVIL FOREST*

*the Prisoners💔*

Kamar matattu haka su ka sha baccin su cikin kogon dutse, Allah kaɗai yasan awanni da su ka kwashe suna sharar bacci, Bawan Allah Danish A zaune ya ke bacci, Wutar da ya kunna masu tuni ta jima da mutuwa, Hasken rana ya kwalo daga sararin samaniya duhun dajin ya ɗan washe, A hankali ta soma mutsun mutsun buɗe idanuwanta a yayin da ta ke ambaton Sunan Allah, tsabar kumburan da idon nata yai daƙyar ta ke iya buɗe shi, ga uwar kwamtsa cunkushe da idon, kaɗan ta ke iya buɗe shi tana kallon Saman kogon dutsen, cikin rashin fahimtar ina ne? sam ta manta cewa sunbar kurkukun ƙaddara, wani irin tsorone ya kamata muryarta sam babu wadataccen sauti ahaka take ƙoƙarin ƙwalawa ƴan uwanta kira ɗaya bayan ɗaya, duk tabi ta furgice.

“Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai ji na ne”? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi da ƙarfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta, slowly ya ɗan ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a iya ƙirjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin sanyin murya ya furta sunanta”My Angel” jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin sambatun nata, ƙoƙari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin fuskarta yai mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana juna, kaɗan ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi”Da..Nish” fatanta Allah yasa ba mafarki bane.

Dogayen yatsun hannun shi ya ɗaura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta ɗaura nata hannun saman nashi dake akan face ɗinta, Sai yanzu ta samu damar motsa jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, Ɗago da ita yai zuwa saman ƙirjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta, sosai ya ƙanƙameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu dake harbawa da sauri da sauri,

“I can’t explain how much I miss you. I’m sorry for what happened, it’s all my fault. I’m sorry, Angel.”

Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shessheƙar kuka ta soma yi mashi magana”ba laifinka bane Danish, ka daina faɗin hakan, ni abunda yafi damuna rashin ƴan uwan mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu alƙawarin da na ɗaukar masu ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran ƴan uwan mu da mu ka rasa” daƙyar ta ƙarasa maganar, zafin jikin su duk ya ɗumamasu, Yanayin weather ɗin dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun dawa.

Ɗaura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi kaɗai yasan raɗaɗin da ya ke ji acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi ta ɗaura eye balls ɗinta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke ƙarewa juna kallo tsawon mintuna goma sha biyar, ‘

“Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun zai ƙara ta6a zuciyarsu, ka taimaka min Danish mu binne su kafin farkawarsu,” shiru bai tanka mata ba sai kallon ta ya ke yi kamar yau ya fara ganinta

“Danish! Am talking to u, bana jin daɗin jikina, maganar ma daƙyar nake iya furtata” Still bai motsa la66ansa ba’ ta rasa meyasa ya ke kallonta yana lumshe ido Ya ƙi tanka mata,” Gyaɗa kai tai”shikenan tun da bazaka taimaka min ba, Ni zan je na rufe su” tana ƙoƙarin miƙewa sexy voice ɗin shi ta ratsa kunnuwanta”Kin ta6a ganin an binne mutun da ranshi”!! ras taji gabanta ya faɗi a matuƙar ruɗe ta zazzaro idanuwanta waje tana kallon shi........

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E7🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

“ka na nufin ba su mutu ba suna a raye”? A ƙagare ta jefa mashi tambayar, jinjina mata kai yai ba tare da ya furta mata kalma ba, bugun zuciyarta ne ya qaru a sukwane ta juya baya don ta samu damar ƙare masu kallo, bargunan da ya lullu6e su da shi ya hana ta gan su da kyau, jikinta na 6ari ta ƙara sa gaban su ta zuƙunna tare da kai hannu ta ɗage saman bargon, duk wani motsin ta akan idon Danish.
Chapter 21 · 0% Book details