← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 152

Sashe 133

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, haƙiƙa yayi babban rashin da bazai ta6a samun mai maye mashi gurbinshi ba”
A hankali Ya furta”Allah Yajiƙanka aminina”
“Boss mu tafi” muryar unaisa ce fargar da shi ga kallonta, Harta zura hijabin ajikinta launin milk, Iya gwiwa ta tsaya mata, hannunta a ruƙe da prayer mat.
Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, dama ranta babu daɗi, dauriya kawai take Yi,
“Meyasa kika 6ata fuska”?
Zumbura mashi baki tai kafin tace”kaine mana, kaƙi jin maganata ni nasan baccine ke addabarka, amma kaƙi zuwa ka kwanta, kalli idanuwanta har sun canza launi sun yi jawur da su...” cikin kulawa tayi maganar
In a cool voice ya furta”karki damu dani, babu bacci atare dani, idona ne keyi min ciwo, kafin na fito daga gida saida na ɗiga magani”
Unaisa sarkin tausayi, duk sai taji ba dadi, jin baida lafiya.
“Allah yabaka lafiya boss, amma dan Allah kaje ka kwanta kayi bacci”
Bakomai ya tuna ba face maganarta lokacin da tana yarintarta, Idan baida lafiya ya kwanta don yai bacci, saman jikinshi take hayewa tana fadin ai wallahi bazan bari kayi bacci ba, ka jira sai lokacin da nima zanyi sai muyi atare, idan ta fadi hakan to bai isa yai bacci ba, dole yajira har zuwa time da zata gama wahalar dashi tukunna suyi bacci, yayi zurfi acikin tunanin shi muryarta ta dawo dashi
“Ka ƙura min ido kana kallona, ko nayi maka kama da wanine”? mamaki take bashi idan tana magana.
Adabarbarce ya furta”um...bakomai mu tafi kawai”
Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Suka nufi ƙofar fita daga dakin.

Kafin dawowarsu dakin danish, Tuni Big guy ya kawo mashi fresh fruit, a faffadan tray ya ajiye mashi saman mattress, abunka ga maciji, ɗai ɗai yake ɗauka da baki Yana lunkuma shi, Cikin ƙanƙanin lokaci Ya shanye kayan marmarin, bayan Ya kammala ci, Big guy ya tambayi Salsabeel Ina Unaisah take? Yaga babu ita adakin salsabeel Yace ta fita dauko hijabin sallah ne, amsa mashi yai da okey, kafin Ya dauki tray din Ya juya yabar dakin.

Adai dai lokacin daya sauko down hannunshi ruƙe da tray, Unaisah da Boss man suna kokarin nufar benan,
Da mamaki big guy ya furta”wa nake gani kamar Boss namu? Me ye hana ka runtsawa”?
Fuska asake Boss Ya nufe shi yana fadin”abunda ya hanaka runtsawa nima shi yahana in runtsa”

Dariya big ya saki”kai dai fadi gaskiya mutumina, nasan me ya hanaka yin bacci, damuwace ta isheka da fargabar kada maciji ya sari ƴarka, koba haka ba”? Ya faɗa yana ɗage mashi gira da zolaya.
“Baka da dama Big guy, ai dole na damu, ita kaɗaice fa ƙwallin ƙwal, bugun zuciyar,”ya fada idanuwanshi akan unaisah wadda tuni Ta haura saman bene don ta isa ga dakin danish
“Na fahimci ba ƙaramin so ka ke yi ma yarinyarnan taka ba, nima kuma inasonta, me zai hana ka bani auranta?da zolaya yai maganar
Harara Boss Ya watsa mashi shima da zolayar yace”ka dai bi a hankali, kada mamallakinta Yaji ka, kaima kasan me zai biyo baya,”
Da sauri Big guy ya toshe baki yana fadin”au namanta, ashefa ka bayar da ita, balle ma nasan koda baka bada ita ba da wuya ka bani ita, don na fahimci kafison inda zata huta” dariya boss yasaki yana fadin”kamar ka sani, kaima din ai ba daga baya ba, sai dai kayi mata tsufa, ina laifin ka nemi ummi mana zata dace dakai.....” tunkan ya ƙare maganar, Big guy ya galla mashi harara”Allah Ya kiyaye, in rasa wazan nema sai karuwa”
Boss yace”abar dai kaza cikin gashinta, kaima din ai tubabbe ne, nima labari naji”
“Ina ganin girmanka man, mu bar maganar, bana son tuna baya, Ni bansan ma wani munafukinne yabaka labari ba, wallahi da zan sani saina takaita jin dadinsa”
Dariya Boss yai ganin yadda ya 6ata fuska.

“Sorry mutumina, zolayatace kawai, ni bansan komai ba, kaine ka kama kanka,”

“Next time idan ka ƙara min wannan wasan, A jikin ƴarka zaka gani” Ya fada tare da bi ta gefen Boss Ya wuce yana dariya, shima Boss din dariyar yakeyi
“Ai kai ƙaramin ɗan iskane, sai dai ka cika baki indai akan Angel dinane, don kuwa kasan ko kallon banza kayi mata a jikinka zaka gani,”
Big guy bai juyo ya dube shi ba, Yai tafiyarshi.

Bayan komawar Unaisah dakin, a kishingiɗe ta samu salsabeel harya gaji da zama, macijin yana nannaɗe gefenshi.

Tayi tunanin bacci yake yi hakan yasa ta soma yin sanɗa tana tafiya duk don kada ta farkar dashi, shimfida dardumar hannunta tayi, kafin ta daidaita natsuwarta, ta kabbara sallah.

Boss na kokarin shigowa dakin aka fara kiraye kirayen sallar asuba, daga bakin kofar ya tsaya yai gyaran murya, salsabeel daya lumshe idanuwanshi jin gyaran muryar da Boss yai mashine yasashi bude idanuwanshi
“Sannu da kokari, Mun hana ka bacci,” yamutsa fuska salsabeel Yai, bacci yana neman yaci ƙarfin shi
“Baku kuka hanani bacci ba, ni na hana kaina saboda ɗan uwana” ya fada yana duban macijin.
Kallon shi Boss Yai, gwanin ban tausayi ya langwa6e kansa, bawan Allah takaicin duniya ya ishe shi.
Shiga cikin ɗakin Boss Yai, a bakin gadon ya dakata da yin tafiyar yana kallon Giant snake din
“Bacci yake yi”? Ya jefa ma salsabeel tambayar
“Bazai Iya runtsawaba, idan har ba Ƴar uwarshi tana atare da shi ba, sai kuma idan ya dawo ainihin halittarsa”
Cikin tausayawa boss yace”kayi hakuri, wata rana sai labari, In sha Allah ƙarshen wahalarka ne Yazo, wadanda suka yi silar ƙuntata rayuwarka, bi’iznillahi ajalin su ne yazo, zasu ɗanɗani kuɗarsu har sai sunji dama ba a halitto su a duniyar nan ba, sai sunyi danasanin rayuwarsu.....” kalamai masu dadi da kwantar da hankali Boss yake fada ma giant snake din, yayi lamo yana sauraronshi.

“Naji an fara kiran sallar asuba, Bari nashiga toilet inyi alwala, idan na fito kaima saika shiga ka yi mu tafi masallaci,” yai magabar yana duban salsabeel.
Batare da 6ara lokaci ba, Boss ya shiga toilet ya dauro alwala, bayan ya futo salsabeel Ya shiga shima yai alwalar,, sallama sukayi ma Unaisah dake zaune saman darduma, kafin suka tafi.

Kamar jira take Yi, subar ɗakin, jiki na 6ari ta miƙe ta nufi gadon ta haye gefen shi tana kallonshi, ta fahimci bacci yake ji, hakan yasa ta janyo bargo ta lullu6asu don ta taimaka mashi yai bacci.

*EX-PRISONERS❤*

Lokacin da Batul ta farka daga bacci, jikinta duk ba daɗi, tamkar mai fama da zazza6i, mura tayi mata mugun kamu, muryarta daƙyar take fita, fitowa tayi daga cikin bargon idanuwanta sunyi luhu luhu, ƙoƙari take tabar dakin duk don kada ta ƙara haɗa ido da ummi, tayi tsammanin zata ganta asaman gadon sai ganinta tay kwance saman carpet, ta lullu6e half body dinta da bargo, tafi ƙarfin ta haɗa shimfiɗa da su shine ta dawo kan carpet ta kwanta.
Muryar batul kasa kasa ta ke ambaton sunan parveen,
Daƙyar ta samu parveen ta farka daga bacci, tana faman yin miƙa haɗi da yin hamma, juyawa tayi 6angaren su Jemimah ta soma tada su daga bacci ɗaya bayan ɗaya suka farka suna faman mutsustsuke idonsu.

Cikin muryar rada take yi masu magana”ku tashi mu tafi ɗaki, lokacin sallar asuba yayi,” ruƙo hannun jemimah tayi ta sauko da ita daga saman gadon, Parveen ta ruƙo hannun Azeeza suka sauko.

“Bana so ta farka ta ganmu, kada ku yi surutu mu lalla6a mu bar mata ɗakinta” ta faɗa tana dubansu, Jinjina mata kai su ka yi alamar toh.

Cikin takun sanɗa suka nufi ƙofar fita dakin, sai da suka fita Batul ta tuna da kayan ummi dake a jikinta, dafe kai tayi da hannu ɗaya”nashiga uku ashe ban cire mata kayanta ba, Parveen ki ruƙe hannun Aziza dana jemimah ku tafi ɗakin mu zan biyo ku daga baya”

Maƙe kafada jemimah tayi”ni tsoro nake ji, idan abun nan ya ganmu fa”?
“Kada ki damu, babu shi ai, waɗannan mutanan sun kashe shi” daƙyar batul take Yi masu magana
“Batul baki lafiya? Idanuwanki sun kumbura jawur, muryar ki kamar ba’aji sosai” Azeeza ce tayi magnar.

Kafin batul ta bata amsa parveen tace”sanyine ya kamata, sai da na hana ta kar6i rigata amma ta kar6a tasaka”

“Amma ai aunty ummi ta bani kaya na saka, Kawai bana jin daɗine bawani abu ke damuna ba, Ku tafi ɗaki zan biyoki” Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin.

A tsananin tsoroce suke tafiya suna tunkarar benan, parveen tana aruƙe da hannun azeeza dana jemimah, har yanzu basu daina jin fargabar macijin ba.

Bayan batul ta koma dakin Ummi cikin sanda take tafiya, harta ƙarasa gaban gadonta, ta cire mata kayanta, ta ɗauki doguwar rigar parveen data jefar ƙasa, ta zura a jikinta, Juyawar da zatai keda wuya, taji sautin datse kofar ɗaki, rass taji gabanta ya fadi ganin ummi atsaye bakin kofar ta goya hannayenta kan ƙirjinta, fuskarta a murtuke babu annuri, idanuwanta sun ƙanƙance.

Hankalin batul ya tashi matuƙa, agigice ta furta”aunty ummi ina kwana”
Harara ta galla mata”daban kwana ba kin ganni atsaye? Kilbabba uwar iyayi”

Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Ai na cire maki kayanki, gasunan kan gado, Ni dakinmu zan tafi, wajen unaisah”

“Idan kinga na ƙyale ki kin fita daga dakin nan, to kuwa kin gyara sautin muryarki ne, wallahi baki isa kija min bala’e ba, Har kayan sanyi na baki, na kuma kashe sanyin a.c, saboda baƙin hali irin naki saida kika bari mura tayi maki mugun kamu duk don kija min masifa ko”?

Hawayene suka soma wanke fuskar batul, muryarta na rawa tace”ba haka bane aunty ummi, nima bayin kaina bane, bansan mura ta kamani har haka ba, dan Allah kibarni in koma cikin ƴan uwana”

Shu’umin murmushi ummi tayi mata,
“Zan barki ki tafi, amma kafin nan saina fara kawar maki da murar nan, don haka mu shiga toilet inyi maki wanka da ruwan zafi”

Zazzare ido batul tayi hadi da girgiza kanta”dan Allah aunty ummi ki ƙyaleni, ai ni ba yarinya bace, da zaki min wanka, ni kawai ki rabu dani nayi maki alƙawarin babu wanda zaisan ina yin mura”

Ɗaure mata fuska ummi tayi zaki wuce mu shiga toilet ko saina 6ata maki rai”?
Chapter 133 · 0% Book details