Sashe 65
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ci gaba da cewa”Shine silar komai dake faruwa arayuwarmu, Zaid Ina kishin mahaifiyata sosai, Ina jin takaici da ƙululun baƙin Cikin mutumin nan, wlh duk ranar da mommy taji labarin abunda Yake aikatawa tabbas zuciyarta zata Iya bugawa saboda tana da kishi kuma Tana son daddy, ni har kokwanto nakeyi anya daddy yana son mommy kuwa? Ko dai Abunda mutane suke hasashe akanshi gaskiya ne? ya aureta saboda dukiyar family dinmu’ yana magana hawaye naci gaba da taruwa acikin idanuwanshi.
Dafa kafaɗarshi Zaid Yai”duk abunda ka ke ji zayn nima inajin shi, Amma Ya zamuyi? Mu tamu ƙaddarar ahaka tazo mana, Muyi haƙuri wata rana sai labari Sannan Yakamata muna tayashi da addu’a akan Allah ya shirye shi, saboda shi mahaifinmu ne duk inda za’aje adawo mu jininsa ne kuma ba zamu so mutuncinsa ya zube a idon jama’a ba.
Lallashin junansu su ka yi, Hannunsu ruƙe cikin na juna suka Nufi Babban falon gidan, masu aikine keta kai komo.
Suna dab da zasu fuce daga falon, Kwatsam Pravin Ya faɗo Sai faman zumbula sauri Yake Yi, Jikinshi sanye da Suit dinsa light brown, ƙiris Ya rage su ban gaji juna da shi, duk da faɗin ƙofar kasancewar Kowan nan su Hankalinshi ba a kwance yake ba
Har zasu gifta shi, suka ci wani uban burki agabanshi, Tun daga Kan Yarda suke jefa mashi kallo yasa shi kame kanshi.
“Har kun dawo daga aikin”? Tambayar daya jefa masu kenan.
Zayn tamkar ya shaƙe baban nasu haka Yake ji, takaici Ya hana su yi magana.
“Lafiya? Baku ji ina magana ba”?
Saida suka taushi zuciyoyinsu tukunna suka Iya yi mashi magana,
Zaid yace”Sannu da dawowa daddy, Ya office din? Naga yau ka yi marece ko duk Aikin ne ya ruƙe ka”?
Basarwa Yai tare da cewa”Eh, “ daga haka bai ƙara tanka masu ba, Sai bi da yai ta gefen su Ya wuce, kamar sakarkaru haka suka Bi bayanshi da kallo, Sam baisan cewa sun san abunda yake aikatawa ba.
Kusan atare suka girgiza kawunan su.
“Zayn tunda Ya dawo mu koma ɗaki, dama Ni agajiye nake wlh, inaso na ɗan kwanta In huta”
Juyawa sukayi Atare suka nufi part dinsu.
Hajiya saratu na zaune gefe gadonta, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta Hannu biyu ta zabga uban tagumi, gabanta sai faɗuwa yake yi gani take yi kamar wani abunne Ya faru da mijinta, Kasa samun natsuwa tayi zumbur ta miƙe kamar an zungureta da sanda, safa da marwa taci gaba da yi acikin ɗakin tana ƙarewa agogon bango kallo.
Ba zato ba tsammani muryar Pravin ta ratsa kunnuwanta”Assalamu alaikum” tunkafin Ta juyo ta kalleshi ta soma sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tsabar farin ciki da sauri ta nufeshi, hannu biyu ya rungumeta a ƙirjinsa.
Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, yayin da take ƙara shaƙar ƙamashin turaren jikinsa.
“Am sorry My wife, nasan ban kyauta maki ba....”tunkan Ya ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dago da fuskarta, babu annuri ko misƙala zarratin tuni yasha jinin jikinshi.
Da kakkausar Murya ta furta”PRAVIN DAGA INA KAKE”!? Rass Yaji gabanshi Ya faɗi
“Na kira p.A dinka Awaya ya sanar dani cewa tun ƙarfe 12 kabar office, Inason Jin ya akai kabar office ina kuma kaje”? Rai a6ace take Yi mashi magana, Hannunta ruƙe da qugunta.
Ya tsareta da Ido batare daya furta kalma ba, hakan ba ƙaramin Ƙona mata rai ba, Tsawa ta daka mashi kamar mahaukaciya Ta cakumi Gaban rigarshi.
“Nace ka faɗamin Ina kaje pravin? Saboda ka maidani shashasha ban da amfani awurinka shine zaka kama Hanya kabar office tun ƙarfe sha Biyu baka kirani awaya ka sanar dani ba, Kasa duk nabi na tashin hankalina akanka, ni na ɗaukama wani abunne ya same ka sai gashi ka dawomun lafiyarka qalou”
Ƴan hanjin cikinsa tuni sun soma kaɗawa, Abunka ga shu’umin namijin wanda yasan takan mace, runtse idonshi yai tare da kai hannu ya dafe gefen cikinsa.
Nan take Hankalinta yai matuƙar tashi la66anta na rawa take faɗin”pr...pravin? Lafiya? Meke damunka”
Da wata irin kasalalliyar murya ya furta”My stomach, bana jin daɗi ai tun Jiya na faɗa maki,” ya ƙarasa maganar yana faman cizon la66ansa, lokaci ɗaya fushin fuskarta ya sassauto, tsananin tausayin shine Ya kamata, ganin yana tangal tangal kamar zai faɗi yasa tayi saurin talla6e waist ɗinsa, da taimakon ta suka ƙarasa gaban Gado Ya hau Ya kanta Yana fuskantar ceilling, daga gefen gadon ta zauna daga gefenshi tana kallon shi
“Pravin am sorry nayi maka faɗa bansan baka da lafiya ba, kaine kaƙi Yi min magana, why pravin kasan baka da lafiya meyasa baka kira awaya ka sanar dani ba? Cikin kulawa take yi mashi magana, har ta manta da zancen tambayarshi Ina yaje.
Wahalallan Yawu ya haɗiya, Cikin mawuyacin Hali Ya furta”wayar bata a hannuna ne a mota nabarta, Ina Cikin Yin draving zan dawo gida, Ciwon ciki Ya takura min, draving dinma na gagara Yi, shine na wuce gidan abokina dake anan kusa, to acan bacci ya kwashe ni,
“Pravin why baka je asibitin Gida ba? ai da komai yazo maka da sauki, yanzu ka tashi ka shirya In kaika asibiti da kaina inyaso sai in dubaka acan”
Tana Ƙoƙarin miƙewa yai saurin fusgo hannunta, gaba ɗaya ta faɗa saman jikinsa, Ƙanƙame ta yai da hannayenshi biyu
Yana faman cizon le6e ya furta”rashin lafiyata bata asibiti bace, My wife kece kike damuna saboda rashin bani haƙƙina da bakya yi akai akai, shiyasa nake fama da ciwon cikin nan, ko da yaushe Aikinki ne agabanki, idan dare yai nayi maki magana kina danna laptop sai kice min In jira ki kammala daga nan har bacci ya ɗauke ni baki gama ba......”
Pravin Ya kashe mata Jiki da kalamansa, ta yarda da abunda ya faɗa mata saboda tasan bata kyauta mashi ta 6angaren nan mafi yawan time idan Ya matsa mata tana Yin aiki bata kula shi saita kammala.
“Am sorry dear, indai nice zan gyara, kayi haƙuri nayi kuskure but bazan ƙara Ba, tun da abun Yana affecting dinka”. Lumshe ido Yai, har cikin zuciyarshi ba ƙaramin daɗi Yaji ba, ganin yai nasara akanta.
“Yanzu ka faɗamin me kakeso? Za ka yi wanka in taimaka? Ko zaka fara Cin abinci ne”
Yana faman sakin nishi Ya furta”nafi buƙatar wankan, amma idan kin amince muyi atare”
Murmushi tasakar mashi”is Okey, shine kaɗai abunda kakeso”? Ɗaga mata Gira yai alamar eh, A hankali ta ɗaura yatsun hannayenta saman coat din jikinsa Ta cire mashi ita, kafin ta zame mashi belt din wandonsa, yunƙura yai tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon Ya ƙarasa zame wandon ya rage daga shi sai short da singlet dinsa, Yaja hannunta suka nufi toilet, da gudu nabi bayansu sai dai kafin in ƙarasa Pravin Ya kulle ƙofa.
*EX-PRISONERS❤*
Idan muka koma 6angaren Prisoners, sai dai muce Alhamdulillah, tun bayan da Dr laura davis ta tattauna da Sojoji bata ƙara Ji daga gare su ba, An dai samu damar Kammala Yi masu injections ɗinsu kuma kullum sai sunsha magani na safe daban na rana daban na dare daban, injection ɗin duk mutun ɗaya uku suke Yi mashi arana, Likitoci sun ci kwakwa Wurin ma Matan allura, Musamman Azeeza da Jamimah, mugun tsoron Allura su ke ji, idan za’ayi masu sai an kira Angel ta ruƙesu, tukunna ake samun sauƙin yi masu allurar, Mazan dai da sauki basu tsoron Allura tamkar basu son ana tsira masu ita a jikinsu ba, cikin kwanaki huɗu da su ka Yi a Texas Rayuwarsu ta fara canzawa, saboda kyakkyawar kulawar da suke samu tarairayarsu ake Yi kamar new born babies, abinci sau uku ake basu, Breakfast, lunch and dinner, Lafiyayyan abinci mai gina jiki, sau ɗaya ake sanyasu yin wanka, su canza Kayan Jikin su, Su Angel an dage da yin sallah da addu’a, har tsakar dare tana tashi yin night prayers, yawanci addu’o’inta akan Danish ne, ta roƙi Allah da ya kare mata shi, idan farkawarshi Alkhairi ce Allah Yasa ya tashi cikin amince, idan kuma farkawarshi ba Alkhairi bace Allah yasa yaita sharar baccina har zuwa su koma Nigeria zaifi masu sauƙin su Yi control dinshi, duk da yanzu ta fara fargaban kada su zo Nigeria A nemi Ruwan zam zam arasa tabbas ba ƙaramar matsala za’a samu ba, damuwarta yanzu akan Sojojin ce shiru basu dawo ba, Kuma bata Ji daga bakin dr laura Ya ake ciki ba, Shin za’a maidasu ƙasarsu ne ko kuwa a’a, Ta dai zubawa sarautar Allah Ido 👀
Sam ta kasa runtsawa, tun wuraren ƙarfe tara na dare ta farka, saboda mugun bugun da ƙirjinta ke yi mata, tabbas tana ji aranta wani abun ne ke shirin faruwa.
Miƙewa Tayi zaune saman gadonta, ta jingina Bayanta Jikin pillow, idanuwanta suna a lumshe, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinta Yake yi wata irin kasala take Ji da matsanancin faɗuwae gaba.
“Masoyiya Angel, Lafiya kika farka daga bacci? Na lura kamar wani abu ke damunki”
Muryar Nurse Jessica ce ta fargar da ita, har saida ta ɗan zabura don bata yi tsammanin jin Muryar mutun a kusa da ita ba.
Slowly ta wurga eye balls ɗinta akan fuskar nurse ɗin, tana daga zaune saman chair ta kusa da gadonta, hannunta ruƙe da wayarta, fara ce sol, uniform ɗin jikinta light blue ne kalar nasu, ta ɗaure jar sumar kanta da ribbom.
Nauyayyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa”sister, nagode da kulawarki agareni, nakasa runtsawane saboda inason ganin yan uwana ko zaki Iya taimaka min”?
Smiling gently nurse jessica tace”Na lura kina son ƴan uwan nan naki, cos tun ranar dana fara kula da ke, sau uku kike zuwa room ɗinsu Kina duba su, faɗamin ko dai akwai damuwane? Ko tsoro kike ji kada mu sace maki su”? Da zolaya nurce jessica tayi mata maganar
Cikin jin kunya Angel takama ƴan kame kame tana faɗin”am.... Ba haka bane just inason su sosai, mun shaƙu da juna, shiyasa bana samun natsuwa idan ban gansu akai akai ba”