← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 152

Sashe 122

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Tsautsayi da ƙaddara” acewar Tiger, Army ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar da Big guy, sai lokacin ya lura da jinin dr jazz daya daskare saman floor, ga kuma Dressing mirror da daya fashe ta silar buga kan jazz jikinshi, cikin matsanancin tashin hankali ya furta”Inna lillahi wa’inna ilaihirraji!”

Cikin sanyin murya Army Boy yace”sai haƙuri yalla6ai, rashin sanine, tabbas munyi kuskure, amma shima jazz din hada laifinshi, Yakamata ace komai zai yi ya sanar da Sir mubarak a matsayin shi na mahaifinshi bawai yayi gamon kanshi ba, kuma a yanayin yadda Sir mubarak yake riskarshi Yana yin waya ta sirri, kalaman da yake furtawa sun yi kamanceceniya dana masu safarar mutane”

Tiger ya ɗaura da cewa”yanzu haka sun tafi asibiti dashi, Muna jira muji daga gare su, In sha Allah zaiji sauƙi”
Numfasawa big guy yai, jikinshi duk yai sanyi kamar wanda aka zarewa laka, babban tashin hankalin shi halin da suka jefa jazz basu ta6a tsammanin abun zai jaza mashi matsala ba.

Tuni idanuwan big guy sun kaɗa jawur tamkar zai fashe da kuka Ya soma yin magana”ba laifin shi bane, laifinmu ne da muka hanashi yasanar ma kowa dangane da aikin da muka sanya shi, saboda bama son kowa ya sani”

komawa yai daga gefen gadon dakin Ya zauna, Yana duban Yaran dake raku6e jikin bango, idanuwansu sunyi luhu luhu.

Mai ta6in hankalin tuni tayi shiru, sai faman zazzare idanuwanta take Yi tana dubansu.

Tiger yace”shi kanshi Chief Owais bazai ji dadi ba, ranshi zai Iya 6aci amma nasan zai fahince mu”
Ganin yadda yaran suketa Yin hammar bacci, yasa Big guy yi masu magana”Kuje ku kwanta, Zuwa gobe idan Jazz Yaji sauƙi zamu dawo maku dashi”

Miƙewa su ka yi a jere suka nufi hanyar fita daga ɗakin jikinsu babu ƙwari, hankalinsu ba kwance yake ba saboda Jazz dinsu da babu lafiya.

Har sun kusa fita daga ɗakin, Big guy ya kwaɗawa ɗaya daga cikinsu Kira “Hawwa! zonan, matashiyar daya kira da hawwa ta juyo tana dubanshi, Ki ruƙe hannun khadeeja ku tafi da ita daki ta kwanta” ya fadi hakanne don yasan su kadaine zasu Iya control dinta har asamu tayi bacci.

Muryarta ashaƙe take fadin”ni bazan bisu ba, kuma bazan Yi baccin ba, wallahi sai kun dawo mun da jazz dina”

Lallashinta mutumin dake ruƙe da ita ya somayi”kinsan dai bazanyi maki ƙarya ba khadeejata, da kaina zan dawo maki dashi, Yanzu dai kije ki kwanta gobe zaki ganshi, amma idan har bakiyi bacci ba, toh bazan dawo maki dashi ba”
Kwa6e mashi fuska tayi”kayi alƙawari”?
Jinjina mata kai yai”in sha Allah” ta amsa mashi da toh, sakarni inje in kwanta” sakinta yai, tafiyarta sam babu natsuwa da sauri ta nufi su hawwa ta ruƙe hannunta acikin nata suka fuce daga ɗakin.

Bayan fitarsu, Big guy ya miƙe ya dubi mutumin”Muna buƙatarka da gaggawa, ka koma ɗaki ka sanya sutura a jikinka, idan kuma zamu Iya tafiya haka toh,” ya fada yana nuna gajeran wandon jikin shi da hannu.

Mutumin yace”bari naje na sanya jallabiya, ƙwara aganni da mutuncina” da zolaya ya faɗa, murmushi sojojin suka saki, fice wa yai daga dakin.

“Yalla6ai wani abu na faruwane”? Tiger ne ya jefa ma Big guy tambaya”kusan haka sai dai kasan yanayin aikin mu” jinjina kai big guy yai don ya fahimce me yake nufi
Shigowa ɗakin matashin saurayin yai, Jikinshi sanye da jallabiya fara tayi mashi kyau.
Miƙewa big guy yai tare da kallon su tiger”zamu tafi gidan chief, babu tabbacin zamu dawo yau, wani muhimmin aikine me girma agaban mu, dan Allah ku kula da yaran, babu wadataccen tsaro agidan” amsa mashi sukayi da toh, army boy yace”Amma yalla6ai zaku sanarma chief abunda ya faru tsakanin Jazz da sir mubarak”?
Big guy yace”ya zama dole mu sanar dashi, sai dai ba yanzu ba tunda shi kanshi hankalin shi ba akwance yake ba, amma idan komai ya lafa zamu fada mashi” gyaɗa kai army yai”okey, Allah ya tsare hanya”
Amsa mashi yai da ameen, kafin Yaja hannun mutumin suka fito daga gidan, jin ƙarar tashin motarsu, Yasa Army da tiger suka sauko down, zuwa sukayi bakin gate din gidan suka datse shi, kafin suka koma palour suka zauna saman sofa suna fuskantar juna

Army boy yace”tiger ya kaga yaran? Nayi mamakin kyawunsu, Allah yasa oga ya amince min in samu matar aure acikinsu” tunkan ya ƙare maganar tiger ya wurga mashi kallon harara”amma baka da hankali, kai waɗannan yaran sunyi maka kama da matan yaku bayi? Ka manta matsayinka ne? Karfa ka cika zaƙewa, wallahi yazu kaji ka a saman kujerar lantarki kana kar6ar punishment, ni kaina ƴan matan sun burgeni, gaskiya Oga ya iya kiwo, fatarsu har ƙyalli take Yi sunji hutu abunsu, yara kamar matan aljanna gashi har gadon baya, gaskiya dakyar idan iyayensu ƴan nigeria ne”

Ya fada yana yin hamma”ni yanwa ma nake ji, Allah yasa suna da abinci agidan, nasan ba za’a rasa farfesu ba tunda Chief owais ne ke kula da cinsu nasan za’ayi harka ta arziƙi, duba mana kitchen dinsu” yai maganar Yana duban Army boy, miƙewa yai da sauri ya nufi hanyar kitchen, har zai wuce yaci karo da freezer, buɗewa yai ya leƙa ciki, Kayan marmarine nunannu, da drinks”

washe baki yai yana faman shafa ciki yace”mutumin yaufa kakarmu ta yanke saƙa”
Tiger yace”ba kallo zaka tsaya yi ba, ka shiga kitchen ka dauko tray ka kwaso mana sauran abincin da suka rage” amsa mashi yai da toh, da sauri ya shiga kitchen.
Jim kaɗan sai gashi ya fito hannunshi ruƙe da katon tray, daga saman tray din plate biyu ne, ɗaya na fried rice daya kuma na chicken wings, saida ya fara tsayawa agaban freezer ya buɗe ya dauko masu kayan marmari ya jera gefen plates din ya ƙara da robobin juice masu sanyi, tiger sai faman haɗiye yawu yake yi,.

Zama su ka yi saman lallausar carpet din falon, kamar masu fama da ciwon yunwa haka suka dumbuza hannu, sunaci suna fira.

Kamar daga saman suka jiyo muryar matashiyar nan mai fama da ta6in hankali tana fadin”wayyo Allah, mayu zasu cinye mana abincinmu!” afirgice suka ɗago suna kallonta, daga can saman bene take zazzaga masu masifa, gashin kanta duk ya rufe gefe da gefen fuskarta, da gudu ƴar uwarta hawwa ta fito daga ɗaki, Taja hannunta suka koma ciki, ta rufe kofar ta yadda bazata sake fita ba.

Tiger yace”jarababba, wallahi hartasa gabana ya fadi” ya fada yana dariya
Army yace”ai daga ganinta anyi rashin ji a ƙuruciyarta, kunnuwanta tsaitsaye suke irin na zomo, gata kyakkyawa da ita” cigaba da cin abincinsu sukayi hankalinsu kwance, bayan sun kammala army boy ya tattara kayan abincin ya maidasu kitchen, a saman sofa suka kwanta ga sanyin A.c, sufa ashar kakarsu ta yanke saƙa.

*Daular Alhaji Musa*

*BENAZIR💔*

Tayi nisa acikin baccinta, ba zato ba tsammani taji an shaƙe mata wuyanta, shaƙa bata wasaba, nan take numfashinta ya soma kiciniyar ɗauke wa, mutsu mutsu ta somayi yi tana harba ƙafafuwanta, hannayenta biyu ta daura saman wuyanta a ƙoƙarinta nata kwace kanta daga hannun mutumin dake yunkurin kasheta, wata irin zuface ta soma tsastsafo mata saman goshinta, zuciyarta tashiga harbawa da ƙarfi da ƙarfi, ta zazzare idanuwanta cikin duhu bata Iya ganin komai saboda sun kashe ƙwan dakin, duk yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa, an toshe mata baki babu halin ta ƙwala kira don azo ataimaketa, hannunta tadinga lalubawa saman mattress cikin sa’a ta cafko hannun zeenatu dake akwance gefenta, cikin fitar hayyaci take tsunkulinta har saida zeenatu ta farka tana shessheƙar kuka ta furta”wai.. wanene ke cunkulina” tunda zeenatu tayi magana, Benazir taji an sakar mata wuyanta, fashewa tayi da matsanancin kuka, sakamakon raɗaɗin azabar da taji wuyanta nayi mata, a matuƙar ruɗe zeenatu takai hannu saman bedside drawer ta kunna fitila haskenta ya haskaka saman gadon, muryarta adabarbarce take fadin”Auntyna meya faru kike kuka? Baki da lafiya ne”? da rarrafe ta ƙarasa gaban benazir tana duban fuskarta, a lokacin ta zabura a furgice ta mike zaune tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta biyu ruƙe da wuyanta, fuskarta tayi sharkaf da zuba, maƙoshinta ya bushe ƙamas, tsananin rudanine ya kamata, kokwanto ta somayi akan abunda ya faru da ita shin dagaske ne wani ya shaƙe mata wuyanta ko kuwa mafarkine take yi”?

“Aunty Benazir dina, dan Allah kiyi min magana, meyasa ki yin kuka? Ko kinyi mafarki ne? Sam takasa buɗe baki tayi ma zeenatu magana sai faman zazzare manyan idanuwanta take Yi tamkar kwayar zasu faɗo kasa, haƙika ta shaƙi ƙamshin mutuwa.
Dafa kafaɗarta zeenatu tayi”mafarki kikayi aunty? ko wuyanki yana yi maki ciwo ne” ta fada cikin kulawa da nuna damuwa take duban fuskar benazir.

Dogon numfashi benazir taja yayin da zuciyarta ke harbawa da sauti mai ƙarfi, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta, gaba ɗaya ta dabarbace tarasa gane meke shirin faruwa da ita! Idan mafarki ne tayi an shaƙe mata wuya meyasa take jin raɗaɗin bayan tafarka daga bacci?
Chapter 122 · 0% Book details