← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 152

Sashe 31

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da su ka ƙaraso zazzaga masu masifa Naufal ya shiga yi yana fadin meyasa basuyi masu bayanin cewe akuyace ba, ae su basu son suffarta ba, iya namanta da suke ci ne suka sani,’ Sai da yayi mai isarshi parveen ma ta ɗaura da nata faɗan akan dariyar da suke yi masu, sauran dai basu ce komai ba, Ruƙo haris danish yai tare da taimaka mashi ya miƙe tsaye. Zuciyarsu Naufal a jagule suka ci gaba da tafiya, Rayuwarsu ta daji gwanin ban sha’awa, Ga cin dariyar kwa6ar su batul komai basu sani ba sai Angel tayi masu bayani, idan dare ya tsala gefen bishiya Danish Yake yi masu shimfiɗa, bayan sun kwanta Yabi su da barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji Ya samo itace ya haɗa masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan Danish bai runtsa ba, Su kaɗai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima, basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan Watansu ɗaya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya ɗaga hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare ya nutsa bacci ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya ya ke ɗaukar su Ya nutsa dasu Cikin dajin ya yi tazarar tafiyar awanni dasu, basu ta6a lura da hakan ba, duk don ya sauƙaƙa masu wahalar tafiyar, shiyasa ya ke yi masu hakan, don kuma su yi gaggawar barin Dajin, Don ya fara Jin alamun wani baƙon Yanayin a jikin shi, fargabarshi kada Giant’s heart ɗinshi ta motsa batare daya Nisantu daga dajin ba.

*PRISONERS💔*

Dare Ya nutsa sosai suna akwakkwance suna bacci, Hasken Wutar Dake Ci Ya haskaka zagayen wurin da suke, yana a Zaune gaban wutar idanuwanshi akan shimfiɗarsu, Sai faman lumshe idanuwanshi Yake yi, ga dukkan alamu baccine yake ƙoƙarin fuskarshi.

Angel da ke a kudundune cikin bargo taƙi runtsawa duk don saboda shi, ta kasa samun natsuwa, Yaye bargon tayi tare da fitowa daga Ciki Ta miƙe tana miƙa ta nufi inda yake zaune, Tunkan ta ƙarasa taga yana gyangyaɗi Ƙiris Ya rage ya kifa kanshi Cikin wutar dake agabanshi da gudun gaske Ta ƙarasa tare da zubewa gefen shi saman gwiwowinta, da hannyenta biyu ta tallabo fuskarshi tana bin shi da kallo, Sam ya gaza buɗe idanuwanshi sunyi mashi nauyi, rungume kanshi tayi saman kirjinta, idanuwanta suka ciko tab da ƙwalla, tsananin tausayinshi take ji.
“Danish muje mu kwanta,” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta mata”bazan iya bacci ba Angel idan har ba barin Dajin nan mukayi ba, Ina jin fargabar wani abu ya same ku ta silar rauni na” ƙara ƙanƙame shi tayi a jikinta”In sha Allah ba abunda zai same mu Danish, Allah Yana atare damu, Kuma Inayi mana addu’a, Kada kaji komai kazo mu kwanta, rashin yin baccin zai Iya ja maka wata matsalar da bana fata” A hankali ya zagayo da hannayenshi saman waist ɗinta, kafin ya lumshe idanuwanshi. Jin shiru bai ƙara motsi ba yasa tayi tunanin ko baccin ya ɗauke shi ne, Kiran sunanshi tayi”Danish” amsa mata yai”Na’am” cikin kulawa tace dashi”nayi tsammanin ka fara baccin ne, pls kayi bacci Danish, inaso ka huta, bana so kana wahala” daɗin murya yake ji acikin kunnuwanshi, har baison intana magana tadaina, Yafi son taita yi mashi surutu.
“Danish naji ka yi shiru baka ce komai ba”? Har saida ta fidda rai da zaiyi mata magana tukunna taji yace”Angel ni wannan ba damuwata bace, i ave told u duk wahalar da zanyi indai akan ku ne bana gajiya, ke ce ƙwarin gwiwar da nike da shi Angel “ murmushi tasaki idanuwanta akan Kitson zanan dake akanshi,
“Faɗamin me ka ke ji akaina? sannan Meyasa kake ƙaunata? Ta yi maganar tare da Ɗaura yatsun hannunta saman kanshi, tuntuni ta ke son ta kwance mashi kitson da akayi mashi a prison don bata son ganin shi da kitso kamar mace tafi son ta ganshi a Namijin shi.

“Nikaina bansani ba” amsar daya bata kenan,
Ɗagowa yai da kanshi tsinin hancinsu Ya haɗe jikin na juna, Hasken wutar dake cine ya haskaka fuskokinsu
Hakanan Taji gabanta na faɗuwa, ganin launin idonshi na canza mata, duk tabi tasha jinin jikinta, ƙwarjini yayi mata da sauri ta kawar da idonta gefe ɗaya
“Abu ɗaya nake fargaba a duniyar nan! Shi ne ace za’a raba ni da ke!” Dawo da dubanta tayi akan fuskarshi, jaddada mata maganar shi yai”Zan iya komai a wannan lokacin,”
“Maganar raba ni da kai ma bata taso ba Danish, dani da kai tamkar anta da jini ne, mutuwace kaɗai zata Iya raba ƙaunar dake a tsakanina dakai, Amma agidan duniya bani da madadinka” kalamanta sun ɗan sanyaya zuciyarshi,
“Ina tsoron ranar da zaki Canza min, duk da bana kawo hakan araina, Angel wani zai Iya ƙwace min ke, kinga ni bani da komai da zan iya faranta maki da ya wuce kaina” Muryarshi araunace yai maganar.

Ɗaure mashi fuska ta yi “Danish zaka Iya bari wani ya ƙwace maka ni”? Girgiza mata kai yai alamar a’a, ya ƙara da cewa”Sai inda ƙarfi na Ya ƙare, “

Lumshe ido ta ɗan yi calmly ta furta “Yadda muka sha wahala atare Danish, Haka nake so Mu ji daɗi atare, Bani da abokin rayuwar daya wuce kai a faɗin duniyar nan, Kaine mallakina, masoyi na har abada, ta ya ya kake tunanin zan iya canza ma ka? Ai kaine nake tsoron Ka canza min idan mun shiga Cikin gari, saboda nasan mutane da yawa zasu dinga rububinka saboda kyawun Da Allah yayi maka, Sannan bansan su wanene Iyayenka ba, amma inaji araina ba ƙananun mutane bane yadda kake da kyan nan da izza ɗabi’unka sak Irin na ƴa’ƴan Hamshaƙan masu kuɗi ne, Ni ko ka ga ba ƴar kowa bace, Mahaifina ɗan Jarida ne kuma ya rasu ma, “ Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi maganar, ƙwallar na gangarowa saman kuncinta yai saurin sanya tongue dinshi Ya lasheta, nan ta ke ta ji yanayin jikinta ya fara canzawa.

“Ni bani da iyaye Angel, Ki daina yi min maganarsu bana son ji, ke ce uwata kuma kece ubana, Kece gatan da nake dashi, Idan ina dake bani buƙatar kowa,” muryarshi a kausashe yake yi mata magana, Ta fahimci bayason zancen Iyayen shi da take yi mashi.

“Meyasa bakason Inayi maka maganar iyayenka? Danish Salsabeel ya faɗamin tun kana jariri aka sadaukar dakai, Naji raɗaɗi jin hakan acikin zuciyata, sai dai Ni bazan Iya yankewa iyayenka hukunci ba, Kada ka manta sadaukarwar kurkukun ƙaddara ba dole sai iyayenka ba, zai iya yiwuwa ba sune suka sadaukar dakai ba, wata’ƙil ma basu da masaniyar kana araye....” bai bari ta taƙarasa maganar ba yai saurin toshe mata bakinta da tafin hannun shi”Is ok, Kije ki kwanta dare Yana ƙara yi,” maƙe mashi kafaɗa tayi”Idan Kaga na kwanta toh muna atare da juna ne,”kafiya ta sanya mashi ya rasa ya zaiyi da ita, A ƙarshe dole Ya haƙura Ya ƙyaleta, kwantar dakanshi yai saman ƙirjinta, Taci gaba da kwance mashi kitson kanshi, Kafin bacci Ya ɗauke su saida ta warware kitson duka, A manne da juna suke ta sharar baccin su, Karo na farko da ya fara runtsawa Acikin Dajin❗❗❗

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E10🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

A Kwance ya ke saman shimfiɗeɗan gadonsa, Kamar kullum cikin shigar larabawa, hannun shi a ruƙe da wayarshi, Ya ƙurawa Hoton wallpaper ɗin shi ido, ko ƙyaftawa bai yi sam baya gajiya da kallon hotonta, Yanayin fuskarshi Ya nuna tsantsar damuwa, a hankali ya ɗaura yatsun shi saman hoton kan wayar yana shafa fuskarta, lumshe idanuwanshi Ya ɗanyi kafin a hankali ya ware su kan hoton, waƙar larabci ya soma rairawa da daddaɗar muryarsa duk akan hoton wadda ya ke kallo, ya dage yana yi mata waƙa mai nuni da ƙaunarta da yake yi, Tunawa da bata a raye yasa shi dakatawa da raira waƙar, Ya jefar da wayarshi gefe ɗaya saman mattress ɗin, haɗi da kifa kanshi saman pillow, kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, abun ne yana damunshi ya hana rayuwarshi sakat.

“Shureim, Ka yi haƙuri Ka daina sanya damuwa aranka, I know it hurts you, but worrying won’t make anything better, it’ll only make things worse kuma ka tuna Allah yanasan bayinsa masu tuba, Kana fa da ilmin ka ba sai na tunasar da kai ba,”

bai tsammaci jin muryarta ba, A hankali Ya ɗago da idanuwanshi Waɗanda su ka kaɗa jawur da su, ya ɗaura su kan fuskar Zainab.

Tana a tsaye cikin shiga ta riga da skirt, kanta sanye da hula, ga dukkan alamu daga kitchen ta fito.

“Babu wanda yasan nashigo shureim, Satar hanya nayi don nasan idan hajiya layla ta sani ba za ta bar ni in zo wurin ka ba.......” numfasawa ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa”Tuntuni na so mu samu lokaci muyi magana sai dai ban samu damar yin hakan ba saboda baka nan, till today” har cikin zuciyarshi ba ƙaramin sanyi yaji ba, yunƙurawa yai tare da miƙewa ya zauna ya jingina bayansa jikin headboard din gadon Yana kallonta, Still hawaye basu daina wanke fuskarshi ba, Zainab ta damu dashi sosai, har mamaki ta ke yi yadda wasu iyayen Allah ya basu damar haihuwar ƴa’ƴa nagartattu amma suke watsi da su, basu damu da damuwar su ba, yayin da wasu neman ƴa’ƴan su ke yi ruwa Ajallo, tana matuƙar jin takaicin haka.
Chapter 31 · 0% Book details