Sashe 142
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Idan muka koma 6angaren Sheikh Imam tun bayan da Chief Ya buɗe ƙofar dakin Danish, Kowa fargaban Abunda idanuwanshi zasu gane mashi yake yi, ƙarfin hali chief owais yayi wajen zura ƙafarshi cikin ɗakin, rass yaji gabanshi yai mugun faɗuwa ganin hular sheikh imam da arab turban dinsa yashe kan floor kamar an wurgo dasu sun tarwatse, ga takalmansa ware ɗaya bakin gadon ware ɗaya kan carpet, a ruɗe chief Ya wurga eye balls dinsa kan katafaren gadon Danish, lamarin yayi matuƙar ɗaure mashi kai, ganin bargo lullu6e da mutun, ƙafafuwansa sun leƙo waje, farare sol da su, Iya neck dinsa bargon Ya lullu6e hakan ya bayyana lallausar sumar kanshi data tarwatse saman wuyanshi hatta gefen fuskarshi ta lullu6e, Chief Ya fahimci yaron ya dawo suffarshi ta mutane sai dai abunda bai gane ba Ina sheikh imam yake? Saboda kwata kwata babu shi a ɗakin babu alamar shi.
“Yalla6ai lafiya”? Salsabeel ne Ya ambaci haka yayin da yake shigowa ɗakin daga bayanshi boss man ne da prime minister hateem suka shigo ɗakin suna ƙarema ko’ina kallo.
Idanuwan mai girma prime minister basu sauka akan kowa ba sai akan matashin dake lullu6e da bargo, tun daga kan shantala shantalan ƙafafuwanshi yasoma kallo har izuwa kan brown hair dinsa, aruɗe ya furta”dama yaron macace ba Namiji ba”? ya jefa tambayar yana dubansu.
“ba maca bace, Namijine Yana da sumar kai ne” acewar Boss man
“Ni abunda bangane ba, Ina sheikh Imam”? Chief ne ya faɗa yana bin ko’ina na room din da kallo.
“Allah dai yasa ba wani abunne ya faru da shi ba” acewar Boss man.
Sunyi tsaitsaye cirko cirko bakin gadon fuskokinsu da alamun ruɗanin rashin ganin sheikh imam.
Prime minister ya kasa kau da idonshi daga kallon sumar kan Danish da yake yi, Ya ƙagara da son ganin fuskarshi.
A lokacin da ba su yi tsammani ba, suka soma jiyo motsin buɗe toilet door, kusan atare suka kai idanuwansu ga kallon ƙofar, bakowa bane yake fitowa face sheikh imam malik, hannun shi ruƙe da cazbaharshi, hankalin shi kwance sai dai da alamun damuwa akan fuskarshi.
Nauyayyar ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, har suna haɗa baki wurin ambaton sunan shi”Sheikh Imam! Muna fata babu abunda ya same ka”?
Jinjina masu kai yayi batare da yace komai ba, har saida ya dawo gefen gadon ya zauna tare da ɗaura idanuwanshi kan bargon dake lullu6e da danish tukunna
A hankali Ya furta”Alhamdulillah, cikin Ikon Allah nayi nasara, Yaron ya canza halittarshi........”ya faɗa fuskarshi da matsakaicin annuri.
Har cikin ransu sunji daɗin jin hakan, musamman prime minister, atare suka haɗa baki suna ambaton Alhamdulillah sannu da ƙoƙari malam.
Girgiza kai sheikh imam yai kafin ya ɗaura da cewa”sai dai ina mai baƙin cikin sanar daku cewa Har yanzu baƙaƙen shaidanun dake atare da shi suna nan daram daƙam, babu alamun zamu yi nasarar raba shi da su..........”
Kallon juna su ka yi kafin suka maida dubansu ga sheikh imam
Cigaba da yin magana yayi”Ina buƙatar neman ƙarin bayani dangane da abunda ke faruwa da yaron? Shin Menene Yajaza mashi faɗawa tarkon miyagun matsafa? da har suka samu ƙarfin ikon Juya shi son ransu’?
Kallon salsabeel Boss man yayi”kai kaɗaine kasan komai Ya kamata ka sanar da Sheikh Imam, kada ka 6oye mashi komai dangane da rayuwar yaran ta hakanne kaɗai zai Iya shawo kan matsalar.
Jinjina kai salsabeel yayi alamar ya gamsu da bayaninshi.
“Labarine mai tsayi, zai ɗauki tsawon lokaci,” acewar salsabeel.
Sheikh Imam Yace”tun da kace labarine mai tsayi, inaga mubarshi zuwa lokacin da yaron zai wartsake, Yanzu Yana buƙatar kulawarmu”
Prime minister yace”Ni kaina zanso naji tarihin kyakkyawan matashin saurayin nan, In sha Allah saboda shi zan nemi iznin ƙara kwanakin tafiyata, but abunda nake son sani, Yaron idonshi biyu? Ko bacci yake yi”? ya tambaya yana kallon sheikh imam.
“Ba bacci yake yi ba, idonshi biyu, sai dai bazai iya ɗaga ko yatsan hannunsa ba, shaiɗanun sun sakar mashi da kasala Ya jigata sosai, Bayan haka akwai tabonni saman fatar bayanshi” sheikh Ya faɗa tare da miƙa hannu ya ruƙo bargon tare da janshi Ya yaye shi gefe ɗaya, faffaɗan bayan danish ne Ya bayyana, Fari sol sai dai ko’ina da tabon ja.
“Wannan tabon na bayanshi, sahun harsashin bindigar da jami’an isod suka harba mashi ne, dama ya faɗa min sunyi mashi illah” acewar salsabeel.
Tsananin tausayinshi ne ya kama prime minister, ji yake tamkar ya rungumoshi, baisan ya akai ya tsinci kanshi da son ganin fuskar yaron ba, shi dai ya kwanta mashi arai,
“Nayi mamakin ganin suffarshi, naji kace min yarone amma surar jikinshi bata yara bace” prime minister ne yai magnar yana duban owais
Chief dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa ya furta”wata’kil halittarsace haka, Girman jiki da ƙananun shekaru”
Jinjina kai prime minister yayi kafin ya kuma cewa”baba Yanzu me yakamata muyi mashi don mu taimakashi ya dawo normal? Ko dai zamu kira likitane Ya duba shi”?
Sheikh Imam Yace”kada ayi haka, saboda bakowa bane zai Iya tunkararshi a wannan yanayin ya zauna lafiya, kawai kubi shi da addu’a in sha Allah zai warware”
“Akwai ruwan zam zam na addu’a da na ta6a jaraba bashi, inaga da za’a same shi wata’kil Ya taimaka mashi wajen samun lafiyarshi, Kafin rasuwar mahaifina Yana yin amfani da ruwan zam zam din wurin yin treatment din mutanan dake fama da irin lalurarshi.
Salsabeel ne ya kora masu jawabin, sheikh Imam Yace”ƙwarai kuwa zam zam Yana da amfani, idan akwai inda za’a same shi kuyi ƙoƙarin samun shi”
Prime minister yace”in sha Allah zamuyi ƙoƙarin samun zam zam din, baba mun gode da ƙoƙarin da kayi mana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka”
Boss man yace”ya sheikh ya akai rawaninka da hular suka faɗo ƙasa? Allah yasa dai ba wani abun bane ya faru” Ya furta maganar tare da juyawa ya nufi bakin ƙofar, Ya dauko mashi rawanin da hular.
Murmushi sheikh imam yasaki kafin yace”kai dai bari, sha’ani da baƙaƙen shaidanu ba abune mai sauƙi ba, ai dambe muka yi dasu, suna bugu ina bugu na haɗasu da ayar Allah, Ni ban ma lura babu rawanin akaina ba sai da ka yi magana” murmushi kowannansu yakeyi, maganarshi ta basu nishaɗi.
“Yaron nan fa sai mun dage da yi masa addu’a, Yana buƙatarta, domin kuwa shaiɗanun dake atare dashi mugayen shu’umaine suna da hatsarin gaske, ba’a ta6a su a zauna lafiya, amma da yake mu da Allah muka dogara kuma munyi imanin cewa shi kadaine gatanmu in sha Allah babu wani mahaluƙi daya isa Ya karya mu sai dai mu muga bayanshi, Na tausaya ma rayuwar yaron kuma ashirye nake da in bada gudummuwata don ganin mun raba shi da su” da kakkausar murya sheikh imam yayi maganar, gaba ɗaya sun natsu suna sauraronshi, har ya kai ƙarshen maganarshi kafin chief owais ya soma yin magana a tsanake”sheikh zamu iya sanin me yaron yake buƙata a yanzu”?
Numfasawa sheikh imam yai yayin da yake bin sumar kan danish da kallo ya furta”Idan zaku Iya taimaka mashi yai wanka, tabbas zaiji daɗin jikin shi, sannan ashirya mashi lafiyayyan abincin da zaici inyaso ko abakine sai abashi tunda bai iya ci da kanshi, Bayan haka daga rana irin ta yau duk wani abu da zai yi amfani dashi kada a kuskura abashi batare da an tofe shi da addu’a ba, tun daga kan ruwan da zaisha, shimfidarshi, ruwan wankan shi da suturar sanyawarshi........”kafin malam ya ƙare jawabin, Boss man yai hanzarin tarar numfashinshi da cewa”Allah yaja da ran malam, yaron ba musulmi bane, hakan zai yiwu kuwa? Yar Uwarshi unaisah ta fada min cewa sunyi fama dashi akan ya musulunta amma yaƙiya, ko kalmar bismillah bai ta6a furtawa ba”
Har cikin zuciyar prime minister baiji dadin jin cewa Yaron ba musulmi bane, Sheikh Imam yace”in ba wani iko na Allah ba zaiyi wuya ya musulunta idan har shaidanun jikinshi basu rabu da shi ba, sune suke hana shi ambaton sunan Allah saboda lagwon su ne, In sha Allah zamu magance matsalar nan badajimawa ba”
Ajiyar zuciya prime minister ya sauke, haɗi da numfasawa yace”Ina son ganin fuskarshi” ya furta hakan Yana duban chief owais, da sauri salsabeel Ya zagaya ta 6angaren daman gadon, Ya haye tare da ruko bargon da hannun shi ya tattare shi gefe ɗaya kan mattress, santala santalan cinyoyinsa farare sol sunyi sambal dasu, sai uban tabonni, kafin komawarshi maciji short ne ajikinshi haka zalika A yanzu haka da yake akwance gajeran wandonne.