← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 152

Sashe 17

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskar mami ɗauke da matashin murmushi ta soma magana a tsanake”kwantar da hankalin ki zahra, Ai duk kyan takalmi ƙafa ce ke taka shi, kuma idan Allah ya ƙaddara cewa shi Yaron wanda kikeso Mijin ki ne duk min muƙamin shi duk mun izzar shi da kyanshi wlh da kanshi zai nemo ki a duk inda ki ke, Ai shi so bashi a matsayin mutun, mai kuɗi ko talaka Zahra kuma ta haɗa komai da duk wani ɗa namiji zaiso zama da ita a matsayin matarshi,...” Tunda mamin Aneelerh ta soma magana zahra ta washe baki tana zabga uban murmushi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, Tsabar murna batasan sa’adda ta sauko daga saman sofa ɗin da ta ke zaune ba, ta dawo ƙasa saman carpet, Ta kafe mami ido tana kallonta kamar wadda ta samu Tashar Bolly wood, Hakan ba ƙaramin dariya yaso ba Ummi ba, Ganin yadda zarah ta ke sakin murmushi jin ana yabanta.

“Mami ni ba ina kushe Zahra bane, Just bana so ta ƙwallafa rai akan abunda ita kanta tasan bazata ta6a mallakarshi ba, Yakamata ta runƙa tuna matsayinta, Mahaifinta fa ɗan bangar siyasa ne ba wani shege ba, Ta ya ya ta ke tunanin zata Mallakin Hamshaƙin mutun kamar *OWAIS SHARAFUDEEN OBINNA*!? Bazan iya lissafi ma matan da su ka yi hauka akanshi ba, Daga cikin hada Ɗiyar Chancellor na ƙasar Germany bayan ita akwai Ƴar sarkin saudi arab, Ga ɗiyar shugaban ƙasar America.....” Lamarin ya ɗaure wa mami kai, Baki asake ta ke kallon Ummi sai da ta kai ƙarshen maganar tukunna tace”Ni ko zanso In ga wanene wannan Namijin hurul ainin, Farin Jini sai kace ɗan gwal yo wannan koda lu’u lu’u aka ƙera fatar Jikin shi sai haka,” Dariya su ka saki gaba ɗayan su.

“Saboda Farin Jinin da Allah ya yi mashi kakan shi Ya toshe duk wata ƙofa da za’a Iya ganin shi, Zaiyi wuya ki samu hoton shi a social media, shahararre ne sosai babu inda ba asan shi ba, Da zarar kin ambaci sunan shi awuri sai an girgiza” Ummi ce ta kora mata jawabi, Al’ajabi Ya kama Mami”Na ƙosa Inji tarihin Family ɗinsu, Najima Ina jin zancensu abakin mutune da kuma labaransu a gidan radio, Nasan fuskokin Ya’yanshi a tv sai dai bansan Komai dangane da su ba”

Gyara zama Ummi ta yi”Jinin Nasara shi ne sunan da akeyiwa family ɗinsu laƙabi da shi saboda wadatar Arziƙin da Allah yayi masu, Suna ɗaya daga cikin Most richest family in the world, shahararru ne na bugawa A jarida, shi Obinna da ki ka ji ana faɗi Kakan su ne tsohon ɗan siyasa ne wanda yai gwagwarmaya ya ruƙe muƙamai da dama tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje, Allah ya yi su da farin Jini, matan shi biyu a yadda naji labari, amma dukansu basa araye yanzu, shi kaɗai ne ya rage, ƴa’ƴan shi bakwai kaf ɗinsu suna ruƙe da manyan muƙamai, su ke ruƙe da ƙasar nan, Manyan ƴa’ƴan shi ƴan Uku ne sune first born ɗin shi” numsafawa Ummi tayi kafin ta soma zayyana mata sunayen su kamar haka.

“SENATE PRESIDENT LATEEF OBINNA, bayan shi akwai CHIEF OF ARMY STAFF SIR MUBARAK OBINNA, cikon Na ukun su shine HIS EXCELLENCY ABDUL RAZAK Obinna Gomnan Jihar Lagos, waɗannan sune yan ukun shi, bayan su akwai ƙannan su maza HIS EXCELLENCY DEEN OBINNA Gomnan Jihar kaduna state, mai bi mashi PRIME MINISTER HATEEM OBINNA Shugaban ƙasar Canada Shi ne ya ke auran Gimbiya mujeedat ƴar Sarkin Dubai.....” Tun da Ummi ta soma bata labarin Mami ta baza kunne tana sauraronta, ga dukkan alamu al’ajabi ya kamata duba da yadda ta saki baki tana kallonta

“Bayan Hateem sai mai bi mashi SHARAFUDEEN OBINNA Current president na ƙasar Nigeria, Adalin shugaba hawan shi mulki da wata biyar kacal ba a ƙara jin ɗuriyar Ƴan ta’adda ba” Fuskarta ɗauke da murmushi ta yi maganar”Kada ki ji Ina yabon shi ya cancanta ne, matan shi biyu Uwar gidan shi ɗiyar Sarkin Yarbawan Jihar lagos ce, Ta biyun kuma ƴar gidan Alhaji wada ce, Ƙanwar former Gomna na Jiharku Jos” Murmusawa mami ta yi fuskarta da alamun mamaki tace”Wai Alhaji Ubaid ki ke nufi surukin tajudden? Dama ƙanwarshi ke auran Sharafuddeen”? Dariya ummi tayi”haba dai kada ki ce min ba ki da masaniya,” watsa hannu mami tayi”taya za’ae in sani? Ni da ba shisshige masu na ke yi ba, In banda ma abun ki ae bani da alaƙa dasu da ya wuce ƙawancen Benazir da Aneelerh, Makaranta ce ta haɗa kuma Yanzu sun rabu, amma duk da haka Na yi mamaki,”

Ummi tace”Auran su shekara goma sha ɗaya kenan A lissafi na, kada ki yi tunanin ina sanya masu ido ne, Kinsan in mutun nada Arziƙi da ɗaukaka a kyauta ake bin diddigin shi....” ta ƙarasa maganar tana dariya Mamin ma dariyar ta ke yi.

“Nasan zakiyi mamaki Idan na faɗa maki cewa Duk irin wadatar Arziƙin dake gare su da ɗaukakarsu Basu da yawa family ɗinsu, Jikokin Obinna Goma sha Biyar” A ɗan ruɗe mami tace”kai! Wai dagaske”? Jinjina kai mami tayi”ƙwarai kuwa, Saratu Obinna ce kaɗai ta ke da ƴa’ƴa Uku, twins zaid da zain sai autarsu Faryat Obinna, Na manta ma ban faɗa maki ita a jerin ƴa’ƴan shi ba, Saratu obinna Itace Autarsu, tana ruƙe da muƙamin Minister of health Mijinta Pravin Obinna ɗan ƙasar india ne silar zuwanta karatun likitanci india Allah ya haɗa ta dashi.....” Ummi bata ƙarasa maganar ba, Zahra tai saurin cewa”Cin Arziƙi ya kawo shi, tsabar son banza mami ya canza sunan ubanshi ya maidashi na Obinna, Sai ki rasa gane ɗa ne ko suruki a gidan” tun da suka fara magana sai Yanzu ta tsoma masu baki hannunta ruƙe da wayarta da alama chatting ta ke yi.

“To ke ina ruwanki zahra? Na rasa meya tsone maki ido da mutumin nan, ya fa riga daya zama ɗan gida, yafi ƙarfin a kira shi da suruki sai da ɗa” Ta6e baki zahra tai”Haba Ummi haka ake surukuntaka, mutun ya tare a gidan surukai don kawai yana auran yar shi, nifa Pravin sam baya burgeni mutun kamar ɗan ta’adda” mami sai kallonta take yi, ta fahinci bata ƙaunar mutumin.

Ummi na ƙoƙarin buɗe baki don ta yi magana Muryar Baby Junaid ta katse masu firar tasu.

Mommy! I’m back! I really missed u, Na maki tsaraba” Gaba ɗaya suka ɗago suna kallon shi, shigowar shi kenan Cikin Falon Jikin shi sanye da suit Na yara Black colour, Madarar kyau, Ya ƙara girma ayanzu yana acikin shekara ta biyar a duniya. hannun shi na aruƙe da Farar leda ta shopping, ba shi kaɗai ya shigo palourn ba, Yana atare da Mahboob Ƙanin Zahra, Kamar su sak kamar tagwaye shi da ita, Crazy Jeans ne a jikin shi, daga sama Ya sanya farar t shirt, Sumar kanshi kwance luf tasha gyara, Miƙewa zahra tayi da gudu ta nufi baby junaid tana ware mashi hannu don yazo ta rungume shi, tunkan ta ƙaraso ya girgiza mata kai Yana faɗin”Na mommy ne wlh, Wayo kike so ki min dan In ɗan maki tsarabata” Dariya suka saki, Zahra tace”matsalata dakai kenan, Komai Mommy mommy, idan da kara nima ai uwarka ce, Zonan dallah” ta ambaci hakan tare da janyo shi zuwa jikinta.

Ummi tana murmushi tace”Kada ka yarda Junaid, Aunty zahra wayau zata maka don ka ɗan mata tsarabarka, “ ɗaure fuska zahra tayi”Ummi kada kisa ya raina ni fa” Ummi tace”ƙarya nayi ne? Yaro yayiwa babarsa tsaraba ke kuma Uwar wayau kina son cinye mashi abu” gatsina mata hanci zahra tayi tare da Wuce Bedroom ɗin Aneeleh ɗauke da Junaid a hannunta, Ya ɗaure mata fuska duk don kada tace zata Ci mashi tsarabar shi.

“Sannu da dawowa,” Mami ce tayi maganar tana kallon mahboob dake zaune saman Sofa, Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya ce”Yawwa mami fatan na same ku lafiya,” Suka amsa mashi da lafiyalou

“Har an kammala registration ɗin”? Ummi ce ta yi mashi maganar, ɗaga mata kai yai alamar eh Saura zuwa school Ya rage mashi On monday zai fara zuwa, Uniform ɗinshi suna acikin mota nabarsu, wlh nagaji Ummi yunwa nake ji kamar in ci ƴan hancin Cikina” yai maganar Yana yamutsa fuska,

Ummi tace”nayi zaton Kun biya restaurant Cin abinci” ɗan zaro ido yai kafin yace”Tab, Ga abinci agidanmu sai in kwasa in tafi restaurant cin abinci saboda almubazzaranci, “ dariya mami ta saki, Mahboob Ya iya tattalin kuɗin shi, Ya tsani almuzarranci arayuwarshi. Yasan ciwon kuɗin shi.

“Tsokanar ka na ke yi don nasan halinka, Da shegen maƙo, Fatana Allah yasa ba ka bar mana yaro da yunwa ba” ta6e la66ansa yai”Tun da muka baro school ɗin ya fara yi min kukan yunwa, don dole na tsaya a wata plaza na siya mashi snack, shine fa daya ci ya rage saura nace ya bani inci yace mommyn shi zai ma tsaraba, ni da na sayi abu da kuɗina amma ya hanani ci, Sauƙin ma wurin jatumarshi zanje ta biyani ƴan canji na,” tuntsirewa Mami tayi da dariya, ita kanta Ummin murmushi ne akan fuskarta, Lamarin mahboob sai addu’a, Babu mutunci indai akan kuɗine
“Kai yanzu saboda rashin ta ido, Sai ka je wurin Aneelerh ka ce ta biya kuɗin daka siyama yaronta snacks? Ɗanka ne fa” Hura hanci yai tare da cewa”Kusan fa dubu ɗaya na kashe mashi, haba ummi, kinsan fa yadda nake wahalar neman kuɗi, Daddy fa ko sisi baya bani sai in yaga dama kema kuma haka” Baki asake Mami ke kallon shi Ummi tace”indai mahboob ne kaɗan kika gani, ae baida mutunci indai akan kuɗin shi ne, Mara Kunya tashi ka bamu wuri, kuɗinka kuma Ka zo da anjima ka kar6a ni zan biya ka,” har ya yunƙura zai miƙewa, Idon shi ya sauka akan Ana mai aikinsu Aneelerh, Fitowa tayi daga Kitchen hannunta ruƙe da tray an jera kayan breakfast ɗinsu, hankalinta kwance take tafiya jikinta na sanye da Skirt pensil baƙi yabi shape din Jikinta, Daga sama ta sanya Riga launin green, Ƙura mata ido yai yana kallonta, Idon su mami akanshi ganin yadda yake binta da ido.
Chapter 17 · 0% Book details