Sashe 87
Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ki fito daga cikin toilet din muyi magana zahra, ni bana so inganki acikin damuwa, kema kin sani har farin cikina zan Iya sadaukarwa saboda ke, don haka ki fito muyi magana” cikin kwantar da murya Aneelerh take yi mata magana.
“Zahra ke nake jira ki fito muyi magana, wlh idan kika bari na haura ƙafa ta daga cikin ɗakin nan to kada ki yi tsammanin zan waiwaye ki, haba dan Allah, ina amfanin irin hakan? Ashe dama baki ɗauke ni kamar yadda na ɗauke ki ba? Har zaki Iya ke6e kanki cikin damuwa ba tare da kin neme ni ba”?
A faɗace Aneelerh ta ambaci hakan, duk don ta samu zahra ta buɗe ƙofar toilet din.
Bugun ƙofar tayi da hannunta”kada Allah yasa ki buɗe ƴar rainin wayau” ta faɗa tare da juyawa ta nufi ƙofar fucewa daga dakin, Buɗe ƙofar toilet din zahra tayi, Fuskarta sharkaf da hawaye idanuwanta har sun kumbura, kumatunta sunyi jawur dasu, Short ne a jikinta tare da farar vest, Sumar kanta kamar ta mahaukaci sabon kamu.
Da gudun gaske ta nufi Aneelerh dake ƙoƙarin fita daga ɗakin, Gaba ɗaya ta faɗa saman bayanta ta rungume tana cigaba da yin shessheƙar kuka.
Ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, tare da kai hannu ta ruƙo damtsen zahra ta zagayo da ita, har saida gabanta ya faɗi ganin yadda hawaye suka wanke mata fuskarta tamkar ba zahra ba, damuwace ƙarara akan fuskarta, kwantar da kanta Aneelerh tayi saman kirjinta, a hankali take shafa sumar kan zahra da yatsun hannayenta.
“Ya isa zahra, ki daina kuka bana son ganin hawayenki,’ cikin murya kuka tace”Aunty Aneelerh ba zaki gane ba, Ni kaɗai nasan halin da nake aciki, Allah ji nake kamar in haɗiyi zuciya in mutu kowa ya huta”
Kalaman zahra sun ƙara ɗaga mata hankali, tabbas akwai gagarumar matsala, Yarinyar da koda yaushe fuskarta dauke da murmushi komai zaka yiwa zahra a duniyar nan baka isa ka 6ata mata ranta ba, sai gashi a yau itace take Yin kuka har tana faɗin kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu.
“Kiyi haƙuri zahra, bai kamata kina yin wannan furucin ba, Idan ma wani abune ke damunki meyasa ba zaki kai kukan ki ga Allah ba? sai kawai ki kulle kanki a toilet kina kuka? Hakan ya dace? Kina tunanin shine mafita a gare ki? Ga ummi ga mami, ga mahboob, ga abie da uncle uwa uba ga kuma ni meyasa ba zaki tuntu6i ɗaya daga cikin mu ki faɗa masa damuwarki ba? Kin tsaya kina yin zurfi ciki a ƙarshe ki yi wa kanki illa amma faɗamana da zakiyi shi zaisa ki samu maslaha na abunda ke damunki, ko da ace bamu da abun da zamu taimaka maki wurin yaye damuwarki zahra zamu Iya baki shawara ko mutayaki da addu’a akan Allah ya yaye maki”
Faɗa Aneelerh tayi mata, sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, ruƙo hannunta Aneeleeh tayi”wuce ki shiga toilet ki wanke fuskarki Ina jiranki” ta faɗa tare da sakin hannun zahra, baiwarAllah jikinta duk ba ƙwari tana tafiya tana waiwayon Aneelerh, yayin da hawaye ke cigaba da fita a idonta.
Kafin fitowarta Aneelerh ta bar ɗakin ta nufi falo, fridge ta buɗe ta dauko mata ruwa me sanyi.
Cikin tafiyar sauri ta nufi ɗakin.
“Aneelerh kinga zahran ne”? Muryar mami ce ta katse mata hanzarinta, ba tare da ta juya ta kallesu ba ta bata amsa da cewa”Eh mami, ashe toilet ta shiga”
Bayan ta shiga ɗakin, ta daura ruwan a gaban mirror, ta koma bakin door din ɗakin ta soma tattara kayan da zahra ta watsar ta maida su a ma’ajiyarsu.
Ba ta jima da zama a gefen gadon ba, Zahra ta fito daga toilet, ta wanke fuskarta kamar mara gaskiya ko haɗa ido da Aneelerh bata son yi, saman mirror chair ta zauna tana fuskanta Aneelerh, sai dai ta taƙi ɗagowa su haɗa ido da ita.
“Ga ruwan nan ki sha” ta faɗa tana nuna mata robar ruwan, data ajiye mata, Yatsun hannunta na kerma ta ɗauki bottle water din ta cire murfin ta soma ɗaɗɗakar ruwan kamar zata haɗa da robar duka ta shanye, bayan ta gama sha ta maida murfin robar ta daurata gaban mirror.
“Zahra ina sauraronki, Ki natsu ki fadamin meya faru dake? Da har yaja kika kulle kanki a toilet, bana so ki furta mun kalmar babu komai! Ranki zai Iya 6aci” fuskarta a ɗaure tamau tayi mata maganar.
Zahra na faman sunnar dakai, idanuwanta akan yatsun hannunta muryarta adabarbarce ta soma magana.
“Aunty aneelerh zan faɗa maki amma kada ki faɗa ma kowa dan Allah,” jinjina kai Aneelerh tayi”in sha Allah”
Cigaba da yin magana tayi”dama akan decorating company dinmu ne, ban ta6a faɗa maki cewa banawa bane, mallakin mamansu ƙawata ne, Ni a lokacin dana kammala karatu ina neman aiki bansamu ba, Nayi ma daddy magana akan ya taimaka mini in buɗe Beauty saloon nawa nakaina, amma sai yace min shi baida halin da zai Iya taimaka mani, bayan ni nasan yana da arziƙin shi kawai baison bani ne kusan halin shi ɗaya da mahboob in dai wurin maƙone ko mami fama take yi dashi, dawowar ku gidan nan ne ma ya fara sakin hannunshi gudun kada ku gane halin shi,’ Aneelerh ta natsu tana sauraranta.
Numfasawa zahra tayi kafin taci gaba da cewa”akwai wata rana da naje gidansu ƙawartawa, muna zaune a falo muna fira akan yadda zamu buɗe beauty saloon da zamu gudanar da kasuwancin su, har take ce min mommynta tana da kuɗi sai dai itama maƙone da ita ba ta Iya fidda kuɗi ta bata hakanan idan ba abun da ya shafi karatunta bane, amma da zata amince mana ko da bashine ta bamu idan muka samu kuɗi tun da kusuwancin ana samu sosai indai mutun ya samu kar6uwa awurin mutane, sai na zaro ido nace mata a’a ni bana so muci bashi muzo mu kasa biya, na faɗi hakanne saboda sanin halin mahaifiyarta masifaffiyace bata da mutunci in dai akan kuɗin ta ne, Aunty Aneeleh fatima ta matsa mini akan muje muyiwa mommynta magana tasan idan na sanya baki zata bamu tallafin da zamu buɗe, saboda muna mutunci da ita, duk cikin ƙawayen fatima tafi sakewa dani har idan nayi kwana biyu banzo gidan su ba takan tambayi fatima ina ƙawarnan taki mai dimple da yake haka take kira na, sai tace mata zata kira ni idan tana son ganina, Aunty aneelerh tsautsayi ne ya kai ni ga amincewa da maganar fatima, muka kwasa muka je wurin mommynta, muka fada mata dangane da beauty salon din da muke so za mu buɗe gashi bamu da kuɗi, matar nan tayi dariya tace mana ai ba wani abu, ta ji daɗi da mu ka yi tunani mai kyau, ita tana son mutun me burin ya nemi na kansa, don haka zata buɗe mana company da zamu dinga gudanar da kasuwancin mu harma mu zuba ma’aikata acikin sa da zasu dinga taya mu aiki, idan yaso zamu dinga raba riba da ita, a lokacin munyi mamakin jin zata buɗe mana company mu da muke maganar buɗe ƙaramin beauty saloon, ni bansan da wata manufa a ƙasa ba, Ni da fatima munyi murna muka dinga yi mata godiya da addu’o’i, tun da ta buɗe mana companyn bata ta6a kar6ar ribar da muke rabawa ba, duk in muka kai mata kasonta sai tace mana mu ruƙe a hannun mu zata nema yanzu bata buƙatar kuɗi, Aunty Aneelerh tun muna tara mata kuɗin har dai fatima tace min mu kashe kudin ai mommynta bata buƙatarsu shiyasa bata kar6a ba, in yaso daga baya in muka tara wasu kuɗin sai mu biyata, zuciya ta ɗebeni muka haɗu ni da fatima mu ka kashe kuɗin, acikin su na cika da nawa kuɗin na sayi mota, Na canza wayata na sayi iphone 15, wayar da kika ga ina ruƙewa a hannuna, Na ciri dubu ɗari uku naba ummin mu nace gashi nan tasa mun albarka kasuwanci yayi kyau, ummi taji daɗin kuɗin nan, dama tana buƙatarsu daddy baya bata kuɗin da zatayi hidindimu dasu, duk nice fa nake taimaka masu idan na samu kudi, shi kawai ta 6angaren abinci ne yake yi mana ƙoƙari, sai kuma kayan sallah idan tazo amma inba sallaba babu abunda daddy yake yi mana, kudin shi sai dai muga wasu suna ci, acikin kuɗin naba mahboob dubu hamsin shima yai ta yi mini godiya hada ƴar ƙwallar shi saboda daɗin da yaji....’ dakatawa ta ɗanyi da yin maganar hawaye nabin fuskarta, tun kafin ta ƙarasa jikin Aneelerh yai sanyi don tasan ƙarshen zancen bamai daɗi bane.
Jinjina kai zahra ta ɗanyi kafin ta daura da cewa”Aunty aneelerh saida na tabbatar kuɗin sun ƙare tukunna hankalina Ya kwanta, sai kwanan nan da Hajiya saratu ta kira awaya suna buƙatar ayi masu decoration da kitso da ƙunshi, lokacin dana duba asusun mu, ba mu da isassun kuɗin da zamuyi order na kayan da za’ayi masu amfani, dama dai ita hajiya falmata itace take yi mana hanyar da ake shigo mana kayan adon daga dubai, muka zauna nida fatima mukayi shawara sai tace min zatayi ma mom dinta magana, bayan sunyi magana da ita, sai ga fatima tazo wurin aikin mu idanuwanta jawur dasu, hankalina atashe na tambayeta lafiya meya faru da ita, cikin shessheƙar kuka tace min mominta tace idan har muna so tayi mana order din kaya mu fara tura mata ribar da muka tara mata a hannun mu, tana buƙatar kuɗin da gaggawa, tun anan fatima tace mata ai babu kudin nan mun kashe su, tsabar 6acin rai ta zazzaga mata masifa tamkar ba ƴar ta ba, hada mari ta kwasa mata a fuska, ko lokacin da tayi mini magana fuskarta da sahun yatsun hannun mahaifiyarta, Hankalina ba ƙaramin tashi yai ba, saboda ni bansan inda zan samu kuɗi na biyata ba, daga ni har fatiman bamu da kuɗin a hannun mu, Aunty Aneelerh nasan bamu kyauta ba tunda ba kyauta ta bamu ba, amma muka ta6a mata kudinta bayan yarjejeniyace muka ƙulla da ita akan duk in aka samu riba zamu raba kaso uku, matsalar da aka samu kuɗin data bar mana a hannun mu taƙi kar6arsu har saida tsautsayi yasa muka ta6a su....” fashewa tayi da kuka Aneelerh ta natsu tana dubanta.