← Book details Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 152

Sashe 130

Kurkukun Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bubbuga bayanta Aneelerh tayi da hannunta Cikin shessheƙar kuka take fadin”komai ya wuce zahra, abunda ya faru laifina ne dana baki shawarar banza duk da ko a lokacin bawai zan zuba maki ido bane don ina jarabaki ne nayi hakan, wallahi duk wani motsinki atafin hannuna, tun bayan dana baki shawarar, fargabana kada ki amince da shawarata ki kama hanya ki tafi kai mata kanki, shiyasa na sanya maki ido, akarshe na yanke shawarar zuwa gidanta don in gargadeta akan ta fita sabgarki, Cikin Ikon Allah sai gashi na 6uge da yi mata nasiha, ashe nice silar shiriyarta, naci ribar jarabawar da nayi maki zahra, Naji dadi kuma nayi farin cikin samun ƴar uwa mai tawakkali irinki, zan iya cewa duk namijin daya mallaki mace irinki yayi nasara sai dai fatan ya cika da imani”

Dariyar farin ciki zahra tasaki, tare da dago dakanta daga jikin Aneelerh
“Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya saboda babu su auntyna, Ina fatan nima Allah yabani abunda zan kyautata maki da shi, sannan mahboob Ya faɗamin cewa kin bashi kyautar kuɗi duk da yaƙi gayamin nawa ne kinsan halinshi May be Yana gudun kada Ince ya bani kasona, baisan cewa Nima na samu alheriba, abunda nake ta so in faɗa maki kenan”

Waro ido Aneelerh tayi da alamun farin ciki akan fuskarta tace”masha Allah, kice kun samu abun arziƙi” Jinjina kai Zahra tayi”zakisha mamaki auntyna, naga yanzu kika farka daga bacci, da anjima idan muka kammala yin breakfast zan fada maki komai”

Murmushi Aneelerh tasaki”Yau zansha kanun labarai, Yanzu bari na shiga toilet in yi wanka”

“Auntyna wai yaushe za’a dawo mana da baby junaid dinmu, nifa nayi missing dinshi, Allah na kusa zuwa in dauko shi, Jiya har mami na tambaya game da zancen dawowarshi”

Aneelerh tace”kada ki damu, Babyn mu yau zai dawo gida, Hajiya adama zata kawo shi, Nima yau da shi na tashi araina”

“Allah ya kawo su lafiya, shima na tanadar mashi kyautarshi ta musamman da zan bashi” Aneelerh taji dadin maganar zahra.

“Kada na cika ki da surutu, nayi kewarki ne auntyna, bari nabarki kiyi wankan in kin fito mun tattauna, amma kafin nan niko inaso in tambayeki wani abu in ba takura” dariya aneeleh tayi kafin tace”okey ina jinki fadamin menene”

Da ido tayi mata nuni da hoton dake amanne jikin bango.

“Wacece wancan black beauty din mai diri? Ita kadai ke bansani ba cikin ƙawayenki, nadai san Benazir mahaifiyar kyakkyawar yarinyar nan Angel”

Jim Aneelerh ta ɗanyi kafin ta furta”Aishatu bintu sheikh Iman Malik, shine sunanta, kamar yadda na fada maki aminnan juna ne mu”

Cike da son jin ƙarin bayani Zahra tace”to amma ta rasu ne ita? Naga ko waya ba ku yi, Ita dai benazir nasan abunda ya faru da ita” a kagare ta jefa mata tambayar.

Cikin sanyin murya Aneelerh tace”ƙaddarace ta afka mata wadda tayi silar tarwatsewar farin cikin rayuwarta, baiwar Allah, nan da kike ganinta mahaddaciyar alƙur’anice, tun tana ƴar shekara goma sha wani abu ta haddace shi, Tana da kaifin basira mace ce mai kamun kai, tana da aji, idan nace zan baki labarin rayuwar Aisha wallahi saikinyi sha’awar yin koyi da ita, saboda kyawawan ɗabi’unta da halayanta, Ni kaina ban ta6a tsammanin zamu rabu da itaba.....” tun da ta fara magana zahra ta kafe ta ido tana sauraronta, idanuwan Aneelerh sun kaɗa jawur, sam bata son tuna baya, hakan zai fama mata ciwon dake acikin zuciyarta.

“Aunty Aneelerh kinyi shiru? tun da kika ambaci kyawawan halayanta naji na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarta”

Girgiza kai Aneelerh tayi”Am sorry zahra, bana son tunawa, “ bubbuga ƙafa zahra tayi tamkar zata fashe mata da kuka tace”please Aunty Aneelerh, wallahi tana burgeni duk da ban ta6a ganinta ba”

Murmushin yaƙe Aneelerh tasaki tana duban hoton yayin da hawaye ke bin fuskarta”Ni kaina bani da masaniyar tana araye kota mutu, tunkafin muyi aure tabar gidan iyayenta, Silar wani mummunan abu daya faru, wanda ni nayi imanin bata da laifi, tuggune da makirci aka shirya mata.....” dakatawa Aneelerh tayi dayin maganar tana kallon zahra, tsabar son jin gulma har ta jefar da cazbar hannunta batare da saninta ba.

“Aunty Aneelerh kinyi shiru! Meya faru da ita? Wanda yaja har tabar gidan iyayenta? Wani irin tuggune aka kitsa mata”?

Tuntsurewa Aneeleeh tayi da dariya, juyawa tayi da sauri ta nufi toilet door tana fadin”Zahra ƙwara ki fidda rai da son jin labarin Aishatu Bintu sheikh imam malik, dan zan baki shi ba yanzu ba sai kin ƙara hankali” ta kare maganar ta shige toilet taja kofa ta datse.

Ta tafi Tabar Zahra da cizon yatsa, idanuwanta akan hoton fuskar Aisha, aranta ta ayyana ai wallahi saina ji labarinki baiwar Allah, Ai ni dama tun da naga hotonki na shaida kinbar tarihi arayuwarki, Oh ni ƴar ubansu, gata kyakkyawa, mace har mace, ga diri kamar nicki minaj, ko tana ina ahalin yanzu”? Sambatu zahra tadingayi tana kallon hoton aisha, sai daga bisani ta duƙa kasa ta dauko cazbaharta, ta futo daga ɗakin ta nufi nata dakin don ta kimtsa kafin lokacin yin break fast.

*Daular Alhaji Musa🏙*

A zaune take kan darduma, bata jima da kammala sallar asubahi ba, hijab din data sanya launin milk, gaba ɗaya ta tattara natsuwarta akan addu’ar da take Yi, ta ɗaga hannayenta sama cikin harshen larabci take karanto addu’o’i, yayin da hawaye suka cika idanuwanta, bakomai take roƙo ba face Allah ya dawo mata da mijinta lafiya da ƴarta, bata da burin daya wuce tayi tozali da su, tayi matuƙar ƙagara da son ganinsu.

Ƙamshin turaren dr.shureim ne Ya dakatar da ita daga yin addu’ar da take yi, da sauri ta shafa saman fuskarta, A hankali ta fuskance shi, yana daga zaune gefen gadonta, bai jima da shigowa ɗakin ba, fuskarshi dauke da annurin farin ciki, Daren jiya da tunanin ƴar uwarshi ya kwana, ya damu da ita.

“Yayana nakaina, Ina kwana ka tashi lafiya”?

“Lafiyalou rabin raina, ina fata kin yi kwanan farin ciki agidan Uncle” shiru tadanyi tunawa da abunda ya faru duk da ta dauki hakan amatsayin mafarki, jinjina mashi kai tayi”Alhamdulillah, jiya naji dadin bacci, hada munshari, balle ni da nake atare da Zeenatu, yarinyar akwai shiga rai”

Murmushin gefen fuska dr shureim yasakar mata”hala tacika ki da surutu”?
Girgiza kai benazir tayi”a’a, ai yarinyar kunya gareta, tana jin nauyin yi min magana yadda kasan bafullatana”

Dariya dr. Shureim yai kafin ya tsagaita yace”hakane tana da kunya, amma fa ta iya zuba kamar aku, sai kun saba da ita zata saki jiki dake”

Dr shureim yasaki baki yana maganar zeenatu, baisan cewa tana la6e cikin toilet tana sauraronsu, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, kalmar akun daya furta ta ta6a zuciyarta.

Murmushi benazir tasaki, abunda baisani ba tun jiya tasan da surutun zeenatu, kafin su kwanta bacci, sunyi firar dare, ta saki jiki da ita tamkar abokiyarta.

“Yaya shureim, Ni yanzu damuwata Mijina da ƴata, mami ta fadamin cewa basa ƙasar, amma sun kusa dawowa, ni namanta ma ban tambayeta sunan ƙasar da suka tafi ba” ta fada tana dubanshi”yaya shureim ko kana da number wayar taj”? Ras yaji gabanshi ya fadi, saboda shi baisan komai dangane da mijin benazir ba.

Shiru yai mata batare da ya iya furta mata kalma ba, don baisan amsar da zai bata ba

“Au namanta, kaima bakasan mijina ba ko? Lokacin dana aure shi......” bata ƙarasa maganarba cak ta ɗago suna kallon juna.

Cikin sanyin murya yace”ai ba laifi kikayi ba, lokaci bana acikin hayyacina, ban kaiga farfaɗowa daga radadin abunda ya same ni ba, Benazir bansan mijinki ba, bana zumunci dashi, saboda ni kaina bana cikin natsuwata, kuma hada ƙarin ni ba azaune nake ba, idan baki manta ba, da abun duniya ya isheni, tattarawa nayi na koma egypt wurin ammim mu da zama” daƙyar yake furta maganar, launin idonshi harya fara canzawa
Numfasawa yai kafin ya ɗaura da cewa”nasan ban kyauta maki ba, amma kiyi hakuri, daga ni har ke ƙaddarar rayuwace ta afka mana,”Wallahi bazan Iya misalta maki ƙunci da radadin da naji ba, lokacin da labarin tafiyarki ya same ni, idan bazan manta ba, aunty zainab ce ta sanar dani komai dangane da guduwarki da jinjirar da kika bari, bayan haka bansan komai game da rayuwarsu ba nima ban jima da dawowa gida ba.......”

Bai ƙare maganar ba ta tari numfashinshi da cewa”kana nufin baka ta6a haduwa da ƴata Angel ba? Amma ni ayadda mommy ta fadamin taj yana kawota gidan mu, suna daukar dawainiyar kula da ita kuma suna nuna mata hotona harma tana tambayarsu Yaushe zan dawo”

Zaro ido dr.shureim yai alamar mamaki da jin ƙaryar da mommynsu ta shirgawa benazir, duk da ba a ƙasar yake zaune ba, yasan komai dake faruwa a gidansu, ta hanyar aunty zainab dake fada mashi akai akai, shi dai a iya saninshi Hajiya layla bata zumunci da tajuddeen, hatta auran benazir da Alhaji ubaid ya bashi bada son rantaba, saboda ita ta tsani bare, balle shi da yakasance mai rufin asiri ba attajirin mai kuɗi ba, har fada saida sukayi da Alhaji ubaid saboda yabama ɗan jarida auran ƴarsu.

Ganin yanayin fuskarshi ya canzane yasa jikin benazir yin sanyi,

“Yayana kayi shiru baka ce min komai ba! Mommy ba gaskiya ta fadamin ba ko”? Adabarbarce ya girgiza mata kai yana kokarin tattara natsuwarshi yace”bahaka bane, ai ni bana a ƙasarne, bani da masaniya akan komai, lokacin dana dawo Nigeria shi taj din da yarinyar sun riga sun bar ƙasar, nima awurin Aunty zainab naji labarin”

Ajiyar zuciya benazir ta sauke, fatanshi Allah yasa kada ta kuma tambayarshi wani abun da zai kasa amsa mata.

“Mommy ta fadamin cewa yarinyar kamanninta sak dana tajuddeen amma hasken fatarta nawane ta dauko, yarinyar kyakkyawace idan zan iya tunawa, kafin na gudu nabarta dana haifeta saida na kalleta har naga launin idanuwanta ruwan tokane kalar na amminmu, kuma tana da curly hair kalar nawa, ni dai fatana Allah yasa bata dauko halina ba, banason ace bata jin magana.

Dariyace ta kubce ma dr shureim, sambatun benazir ba ƙaramin kayatar dashi suke Yi ba.
Chapter 130 · 0% Book details