← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 173

Sashe 96

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_ _*nayi tunanin na wayar ma wasu kai out of rashin sani musamman wa yanda suke ji anacewa wai sunan indians ne acikin Ahumagga..ITS A LIE..strickly ARABIC/ISLAMIC NAMES ne with awesome meanings, google it..karku bari wayanda basu san kan labarin ba su kauyantar daku su dawo daku jahilai by force..su basu sanii ba sannan bazasu barku ku sani ba. labarin Ahumagga is based on persian kingdom(iran,pakistan,laurestan,rajiskan tajiskhan etc) and little of typical nigerian fulani culture so dole ne littafin ya banbanta da yadda aka saba.*_ -Villain 1 Sa'ood A Reality yake ganin komai agabansa amma Duk da haka sanda ya ga kamar a mafarki ne. ...a take idanun shi suka sauya kala suka dawo jajir,wani zazzafan huci ne yake taso masa tun daga kahon zuciyar sa mai zafi sai yakeji kamar ana hura masa wuta ne akansa.. "So this is the real truth?..toh meyasa bata fada min ba...meyasa bata fada ba, wani dunkule hannun shi yayi cikin tsananin radadin jin haushi..wani tasss kake ji a kasan floor na karar saukan wayar sa dayayi firo dashi baima sani ba. Yau Bayan yaji mugayen boyayyun sirrikan sadat akan subaya,a Duka videos din dayake kallo na cin mutuncin da sadat yayi ma bahiyya yana razanata duk su suka fi komai tsuma shi Aynzun ko daya baiyi tunanin zai bace a kwakwalwar shi ba har sai yaga ya rama mata.. Daga jin saukar numfashin sa zaka gane cewa Hankalin sa a matukar tashe yake,..biting his lips slowly ya cusa hannun shi cikin lallausan suman kanshi yana shafawa kamar me naxari.. She was my sis ..and now she is my bby my wife.. ..tsikar jikin shi har harbawa suke suna tasowa.. a idanun shi yana imagining yanayin yadda zai cire ma sadat farinciki a rayuwar sa. Duk da halin da subaya ke ciki nai hanasa karasa kallon videos din ba He is very intelligent dan haka abubuwa dayawa sunzo mind dinshi a wannan lokaci Wani dabara ne ya fado mashi dan yasan ba iyakar abun ba kenan"idan har wannan videos din agida ne gaban subaya to meke nan yake mata idan bata gidan?..wayar shi ya daga ya binciko tun sakon da da dija ta turo masa na rashin lpyar bahi, then he call the number amma sai yasmine ne ta dauka... Yasmine Tasha mamakin data ji shine akan layi,but da shike baya cikin hankalin sa sosai so bai tsaye gaishe gaishe ba ya fara mata tambayoyi,ita kuwa bata bata lokaci ba ta gaya masa hakan yana faruwa a schl..ya lura she cant give all details sabida tana jin tsoro sai ya mata godiya ya katse wayar.. Subaya Tasha mamakin furucin yasmine dan tana jin duk tambayoyin sa da kuma amsar dayake samu.. ...."yasmine ta basu hints,tun daga farkon bakin zaren ta kamo musu su kaji komai xuwa har lokacin da yake kiran bahi yake mata barazana kala kala agaban su. Subaya bata dena nishi ba dan tayi kukan har ta gaji,ita aynzu ma dukiyar bai dame ta ba,abubuwan data gani bahiyya ta fuskan ta under her roof bata sani ba su suke zautar da ita..,a hankali cikin jimantawa take cewa ya cuce ni...sadat ya lalata min rayuwa ta.. Ta yaya zan kalle yarinyar nan...ashe har zata iya zama cikin kunci da bakinciki dan ta kare ni daga wannan babban al'amari? "She is just a little girl,me tasani da zai dauki hakkin ta haka..?ko dan yaga marainiyace bata san komai ba ...hannu ta daura akan kirjin ta tana wani irin kuka mai ban tausayi..khal har ya iso gaban ta yana rirrike ta mma bata sani ba,cike da sanyin murya da sanyin jiki yace subaya ki nitsu kiyin min bayani ..wai A ina kika samu wannan videos din? Ina son nasan meya faru did u know anything about this kar ki boye min dan Allah. Cikin kuka tace wallhy ban sani ba.. I just found out now...kukan sosai yaci karfin ta ,..pls get up ya dagota da kyar yana mai tausaya mata,tallafo ta yayi ya aje ta agado dan har wani luu idanun ta suke jikin ta yayi sanyi sosai Bata iya komai sai sauke ajiyan zuciya idanun ta har sun kumburo sun haura kamar wanda aka aika ma sakon mutuwa... Zama yayi agefen ta yana dan calming din ta har tayi shiru da kyar tayi masa bayanin yadda videos din suka shigo hannun ta komai ta fada bata rage ba..tace khal babu lokacin dogon bayani,bana son mum taji komai har sai munji sauran bayanin daga bakin bahiyya...xaka kawo ta?ko binka zanyi muje abujan. I reall..i really want to meet my sister khal... i want to make sure if she is ok...ko baga yadda yake dukan ta bane?...this is a sexual assault... abun nashi yayi yawa.. yayi tamin karya akanta and i do scold her batace min komai bayan kuma bata da laifin komai....wani matsanin cin kukkan datake dannewa ta sake fashewa dashi,tace dana san abunda yake mata kenan wallhy wallhy da na bashi dukiyar duka an rabu lpya.. He lied to me dan ya raba ni da wacce take kaunata Ashe ma karya yake mana dayace tace mashi tana son shi? Wayyyo Allah na bahiiya ta kiyafe min..im sorry for judgin u my litle sis...im so regreting this.. i just cant take it anymore. Khal shikadai yasan meyake ji aransa amma haka ya daure ya dinga lallabata musamman dan kar ciwon nata ya tashi Magana sukayi na fahimta ,..da kyar subaya tayi masa alkwarin zata danne zuci yar ta dan kar jahan ta sani yanzu sai sunyi bincike ..shikuma yace ta bashi kwana uku zai gama da komai.. A Cikin daren ya fita ya bar gidan daga subayan babu wanda ya san da abunda ke tafiya. Bangaren su kaamil kuwa ba irin dabarar da baiyi bahi ta gaya masa watake aure ba amma sam taki tace mashi komai,bai so ba amma haka ya barta ta xame ta tafi ta barshi awajen ... Yayi ta xubda hawaye saboda wannan karon ne farko da zuciyar sa yaga abinda ya biya masa sosai,he want to respesct her decision tunda tace mashi aure ne akanta amma sai yaji bazai hakura ba sai yaji wanene mijin bahi.. Bahi kuwa abun bai wani dara ta chan chan ba,taji wani iri kam amma bata zafafa komai aranta ba Washe gari da sassafe,dija na gida taji sammaci cewa ana neman ta a waje..da kyar ma ta fito dan babu wanda ya taba mata irin wannan sammakon Ganin khal har bakin kofar gidan su yasa ta sha mamaki sosai,bakin ta har na batan kalma ta ushering dinshi ciki cike da mamaki da girmawa Comfortably ya zauna akan sofa,da shike its 7 oclk sai ta kawo masa hot coffe,just one sip yay..badon komai ba sai dan ya kwantar mata da hankali ya lura ganin shin ba karamin tsorata ta yayi ba.. Ta tambaye shi lpyar bahiyyar..ba yabo ba fallasa ya amsa da cewa tana lpya..anan ya shiga kawo mata tambayar sa kamar hira tun daga lokacin da ta fara sanin bahi a schl..har ya kawo ta inda yake son yaji Toh Daya fito fili ya nuna mata yasan labarin sadat..,sai taji kawai bata da option face ta bashi labarin duk abunda yafaru.. Khadija kam bata ji tsoron komai ba,evry little details tagaya mashi na abunda bahi ya fuskan ta .. Duk dama tayi kuka sosai,amma she was brave enough to say that in har xai raba bahiyya da sadat to zata taimaka mashi ta duk hanyar da zai bukace ta. Hakan yasa ya nemi alfarman mum din ta,ya dauke ta ..by 9.30am suka nar nigeria zuwa kasar london.. Da kwararrun yan bincike tunda daga military base ya fara dora salon sa.. acikin ranshi Tsaf ya shirya irin kalar hukuncin da zaiyi ma sadat da duk wani mai hannu da bada gudumawa acikin case din Sam baya son bacin ranshi yasa yayi garaje ko kuskure Yana dai so ya tara manyan shaida akansa,yasan yana bukatar ya aje hankalin sa waje guda yanemi taimakon dija. Da suka isa london Basu kuwa samu duwawun zama ba dijan Ita ta kaishi duk inda sadat yake hada shirin sa,har wannan wood house din daya gallaba masu azaba sanda ta kaishi yayi binciken sa sosai Kwana daya da rabi sukayi a london ya gama binciken sa,nan ya hada ta da wrist wacht mai dauke da security trackers da audio recoder yasata a jirgi ta dawo nigeria batare da sanin kowa ba... Dija Tana so ta gaya ma bahi amma khal ya mata warning akan haka..m most time ma kashe wayar ta take yi dan tsaro . On the that 2- 3rd day da asubahi khal Ya wuce USMC base,da uniform din sojan nashi ma ya shigo fuskansa adaure kamar malaikan mutuwa... Anan ofishin wanda suka san case din basu fi mutane biyar ba,biyu daga kwararun masu bincike daya daga laboratory sai computer scientist din su mai gaba daya.. Wasu files khal ya karba daga wajen dayan repotern Daga nan Yayi 1hr indoor secret meeting da manyan generals da officials dake wajen ba wanda yasan meya ke nuna musu Yana fitowa A hujajan ya wuce torture room ya aika mugayen sojojin sa guda biyu har izuwa lab din..kowa anyi dismising dinsa aka bar doctor barak adeel ...barak adeel yana ta aikin shi kamar mutimin arziki ya dauka ko irin mission din su na gaggawa ne ya taso ma khal ake bukatar taimakon sa Da suka tsamo shi yaga an nufi torture room da shi abin ya dan bashi mamaki aransa sosai... ..yana budan baki zaiyi magana.. khal ya tsare su...oder kawai ya basu da idanun shi,bajira suka fara dukan sa ta ko ina da wasu irin kakkauran rubber mai irin kaurin belt din engine din nan Kowani saukan duka,thy wll make sure kayan jikin sa ya beke,doc barak adeel yayi ta ihun radadi ga azaban rudanin rashin sanin laifinshi,khal bai motsa ba yana ta kallon shi har ya bar zuba ihun ya shiga fade fade,yana neman afuwa duk jikin sa saida sukayi tambari da jini.. Sanda ya galabaice khal yasa aka barsu su biyu..barak is his private doc so ya san waye khal sosai ..duk dashi ba sojan yaki bane amma yasan khaldun din nan da ake gaya masa ba wai bane
Chapter 96 · 0% Book details