Sashe 67
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._ _Bismillahirrahmanirrahim._ -Golden candles ...Burin su dija ne su ganta cikin farin ciki da walwala dan haka bakara min murnan dawowar ta sukayi ba.. Guiding Sojan daya zo da itan shine ya kawo ta har hostel An bashi lodge da car,an kuma bashi umarnin ya mata duk abunda take bukata,da gifts dayawa ta dawo ma su dija kowa sanda yayi murna wajen karban nashi...hira sosai sukayi sunata mamakin yadda ta dawo a murmure cikin nishadi da walwala kamar ba ita ba.. Washe gari safe da suka tashi take nuna musu sabin dresing codes din da habibin ta yafi sha'awar ganin ta da shi,..sunyi dariyar ta har da tsokana sabida mostly musulmai masu saka decent turkish gowns da jallabiyas duk matan aure ne.. Yasmine ke cewa ko auren kukayi ne afada mana gaskiya In suna mata hakan itakuwa bakaramin dadi take ji ba,dan tana matukar kaunar yadda suke bata suport akan tsananin soyayyar dake zuciyan ta game da khaldun After 4months daga da dawowar ta babu labarin sadat,babu labarin khaldun.. Wayanda suke taimaka musu akan binciken sadat a boye ne suka sanar dasu cewa sadat yana chan china an gayyace shi wani babban case din kisan kai yana can yana fafatawa. Anan ma suka dada gano cewa acikin munafukan su harda hostel super intendant dinsu ..ashe intazo Zagayawa room check tana sa ido sosai tana kaiwa sadaat duk wani information akan su...tunda suka gano ta suka fara takatsantsan da ita hakan yasa wani abun ya ragu musu.. Rayuwar su a normal sukeyin shi kusan evrymonth khal na suporting dinta da kudi ta hannun wannan guiding soja,bata san ya ake yi suke comunicating ba amma inta kira layin shi ma ba a samun shi.. Basu jidadi ba sam sabida sunyi iya kokarin su su tona asirin sadaat cikin watannin nan amma ko ina kofar a rufe take musu,a haka dai suka hakura suna famar kokarin binciken su a hankali Ayanzu Dija da yasmine ne kadai suka rage suna kula da eatry longe din sabida tunda bahiyya ta same hutu evryday sai ankaita islamic school tana koyan karatun Qur'ani da larabci. Bangaren junnut ma kusan hakan ne,duk dama tana iya kokarin ta wajen ganin itace sama da kowa arayuwar khaldun amma hakab itama ta dangana da hakurin rashin ji ko ganin sa. After 1 and half years.. Junnut tana aji hudu ayanzu saura mata shekara guda ta kammala karatun ta sabida is a complete full business couse with all the special business hookings. To End of This year bahiyyah ita kuma zata gama school din ta,sosai jahan ke famar zumudin shirye shiryen dawowar ta nigeria sabida sosai tayi kewar ta yau shekarunta uku da watanni shida ciff a london...banda waya basu sake rabar juna ba Alhaj hamood ma ya nuna farincikin sa,shi ya dage cewa sai bahiyyan tayi special training na nutritionist da wani world health chamber da tuni An fara shirye shiryen dawowan ta nigeria a watan da zai kama.. Shikam yasan bazai samu damar halartan convocation din ta ba dan haka ya sa jahan Aarah suka shirya mata gagarumin secret Graduation Party Hade da 18th-19 birthday dinta ba tare ma da ta sani ba Duk dama subaya ta dan ja jiki da hidimar ta amma wannan karon itace gaba a wajen shirye shiryen hidimanta. Ana daf watan graduation Sadaat ya dawo sai dai baigane komai game da bahiyya ba Sai ya ga kamar komai na neman sarke masa,ya buga sihirin nasa amma baiya gane komai game da abubuwan ta.. He got really confused,sosai abun ya dame shi,gashi ko kadan baiyi tunanin Suma sunyi wayo sosai ba,dan bayan rokon Allah da sukeyi taimako suke nema akanshi bana wasa ba.. Daya ga abun nayi ne sai ya kyale shafin bahi ya shiga fidda sabbin halayen ma matarsa subaya... Wasu banzayen halaye ne wanda da chan bata san shi da shi.. Misali a kowani dare sai ya lura tana bacci sai ya dauki kafar sa Ya je chan quest room ya kwana giving her the impression of akwai abunda yake yi wanda baya so ta sani Itakuwa tunda ta tambaye sa sau daya bai bata kwakwaran dalili ba sai bata sake daga kai ba Nan ma abun ya bashi haushi sosai duk dama bayasan nunawa a fili gashi nan a dalilin hidimar partyn da zasu hada yasa yanzu subayar dakanta takan nemi bahiyya a waya sau biyu sau uku a sati. Gaba daya ya fahimci cewa bahiyya tana cikin kwanciyar hankali Bakamar yadda yayi tsanmanin barazanar sa zai kuntata mata ba Subaya kuwa wani bin Ko dan ta san me yakamata tayi mata wanda zaisa ta farin ciki sosai kamar yadda iyayen nasu su kace take kiran ta suyi dogon hira most time agaban sa kuma yanaji. Acikin wayannan kwanaki babu abunda ya dada tunzira sadaat kamar yadda subaya ta ke samun hankalin khaldun shima babu wanda ya san ya dawo sai ita,it seems he is free now,amma ko ita ma tayi ya gaya mata inda yake amma sam yaki Gashi jahan bata gaya ma subaya maganan Alkwarin nashi ba sabida tasan bayan graduation din bahiyya subayan ma zata zo nigeria hutu ,subayar kuwa a kullum sukayi hira mai nisa da khal sai ta kawo masa maganan aure amma bai taba amsawa ba. Tun da ya fara kirar ta a waya Acikin tadin su sau daya ya taba fitowa fili ya tambaye ta lpyar bahiyyar san,.ta lura abun har nauyi yake masa dan haka itama bata tsaya bata lokacin gaya masa cewa zasuyi mata harda birthday party... Bata ma san suna haduwa da chan ba all she tot was tun da aka rabu a nija shikenan bai sake ganin ta ba Data gaya masa maganan secret party da mahaifiin su ya umarta Sai ya basar baice kuma zaizo ba amma yana sane da cewa mahaifiyar sa zata zo. Ana saura 1 week graduation din bahiyya a london auren subaya da sadaat ya cika 6 gud years. "Kaamil,.da khaldun gifts iri daya suka aiko mata,Daga chan kingdom kuma suka aiko mata da silver card da kudi masu yawa. "Jahan Aarah ita kadai ce ta yi mata adduoi hade da mata nasiha akan tsarin da suka daura ma kansu Na rashin haihuwa. sadaat najin su,amma baice komai ba sai ya fita,"..dan gifts din da ya aje mata akan table din ta dauka ta bude...wani pink parcel ne mai dauke da wani doguwar riga da haddaden neck lace an rubuta santa(angel) da golden plate. "...'She was soo happy,gashi kalar rigar ja ne sai tayi deciding shirya musu special dinner date agida kafin ya dawo. Haka taci wanka ta yi kyau,ta shirya abinci kala kala ta xauna a na jiran sa,abu wasa wasa tayi ta jiran sa amma shiru babu shi babu layin wayar san Tun da Karfe 10 na dare yayi taga shiru sai abun ya fara damun ta,it cant be posible ace Saadat ya fita tun safe amma har 10 na dare bai kira ba kuma bai dawo ba. "Worst part on thy 6th weding aniversary night Kasa zama tayi tana famar jeka ka dawo a tsakar palon su bata tsaya ba har sanda door bell yayi kara saurin ta ta isa bakin kofar tana budewa kuwa Shi ta gani a tsaye a jigashe kamar wanda yayi tafiya da kafarsa ya gaji Cike da mamaki ta karaso zata riko sa sai ya ja da baya yana wani irin layi kamar bugaggen Cike da mamaki tace,sadat? Meya same ka wher ave you been,wabi kallo ya bit dashi idanun sa sunyi jajir,daya gyara balance dinsa baima kulata ba ya wuce ya barta anan a tsaye tana binsa da kallon mamaki da rudewa Meya same shi? Tasan sai tunda take dashi bai taba shan giya ba to meyasa ta jiyo warin giyan ajikin shu gashi kuma ya shigo mata yana layi, Dakin itama ta biyo sa a rikice dan kirjin ta har na dukan uku uku. . Tana bugawa taji shiru,ta fara kwalla masa kira..sadat sadat ..karshen ta haka ta kyale sa basu kuma hadu ba sai washe gari Washe garin da ta tada bori ta nuna bata ji dadi ba,cikin salon sa na iya yaudara ya mata karyan cewa tsaban farinciki dayake ciki ajiyan na cika shekaran sa shida da ita yasa abokan sa turawan nan suka sa shi yasha giya batare da yasanii ba,yace duk suka jawo Kuma shima yayi nadama. Ta dai ji shi amma hankalin ta har yanzu bai kwanta ba,shikuwa sadaat dagangan yake hakan sabida ayanzu baida wani bukata face cika babban burin sa da yake kan shiryawa akan rayuwar sa da bahiyya Toh A Cikin satin sanda ya ci nasaran dasa ma subaya mummunan zargi game da shi saii dayasa ta fara ganewa da halayen sa na asali ta hanyar ajiye sako ko short note da yake nuna mata cewa akwai wata mace dayake gani bayan idon ta. Most time zata gani kafin ta tambaye shi sai ya kwace ya fita ya barta da shi cikin zulllimi Toh ranar da jirgin su na london zai tashi tana wanka taji wayar sa nata ringing alaman baiya dakin,kawai sai ta fito,sam bata san yana gefe a bakin kofa yana lura babatakaice a shiyake kiran da wani wayar da bata san shi dashi ba,yana jin alaman ta dauka tana dubawa sai ya danna send tuni sai ga wani sako ya shigo,.. Ita kuwa babu wani abu aranta ta bude tunanin ta komai kiran ne ya turo sako Tana budewa ta shiga karantawa anan taga wasu maganganu masu tabbatar mata da cewa gifts din rigar da necklace daya bata a anbiversaryn su bama ita kadai ya siya ba harda wata. Sai dai number be babu suna kuma private line ce Abun ya dame ta sosai kenan sadaat yana neman wata a waje? Daya shigo Taso suyi magnan amma sai ya shiga gwada mata shi fa ba shi yace yana son kowa ba shima yarinyar ce take binshi, Subaya ta so ta daure amma abun ya mata zafi,gashi bai lallaba ta ba haka kuma fir yaki ya gaya mata wacece yarinyar Haka dai ta yi juriyar haushi da kishin sa sabida tana son shi sosai,iya wiya bata son abunda zai rabasu shikuwa ya nuna mata ko ajikin