← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 173

Sashe 18

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ammu adama Nasha mamakin ganin ta sai dai kafin na budi baki na gaishe ta ta jawo hannu na tana cewa u have to come quick Jahan na neman ki a falon ta cikin gaggawa Nace toh,sai dai Kirjina kamar zai fashe tsaban tsoro da fargaba ban iya cewa komai ba na bita har muka isa palourn jahan Aarah. Muna shigowa shima fara hangowa,a sadade nake tafiya crushing and falling for his gesture duk dama nasan bada ni yake ba,For the first time eva yau naga wata kawataccen murmushi a fiskan sa daya sani jin zuciyata ta yafe mashi duk abunda yake yi mata. Toh Lallai yana kaunar Mahifiyar shi,wannan yanayi nashi ko amafarki akace xan gani bazan taba yarda ba. Sai da ammuh adama ta rusuna tace ma jahan gata nan kafin ma ya dago ya kalle ni,atake na ga ya sake daure fuskan sa Ban damu ba na rusuna cikin sanyin jiki da ladabi nace ina kwana jahan? Tayi min murmushi tace bahiyya ko? Nayi sauran gyada kai tace Taso ki tsaya anan. Sai ta sallami ammmu nikuma na tashi tsaye agaban su duka daga gefe kaina na a kasa. Inajin ta Sai da tafara bashi hakuri kamar wani sarki, sannan tace masa sunana bahiyyah nice zan dinga kula dashi for the main time.. "Tsaban yadda kirji na yake bugu bansan sanda ya amsa ba Ji kawai nayi ta saka masa albarka Ta kuma jaddada min Dokokin aiki na agaban sa. Nace insha Allah xanyi.. Nan ta sallame ni na koma site dina na fara shirin jiran malamina. Washe gari da safe,tunda jahan tayi clearing tsakani da shi akan maganan aiki sai bani da wata fargaba na cigaba. A kullu yaumin zanje na samu yana bacci haka nake kammala komai cikin sauki Sai dai kamar an dauke masa magana baki yau kwanan mu 10 kenan bai taba budan baki yace min uffan ba" I was happy tho atleast babu tsawa babu tsiwa Ranar juma'a da yamma na baje littafan biology ina dubawa kawai naji an taba kafada ta. Ammuh adama nagani tare da wani mutum cikin uniform din aikin sa. Ban bata lokaci ba na sauko karasowa nayi cikin girmamawa na gaishe ta nan ta shiga min bayani Akan cewa na shirya yanzu khaldun zaiyi tafiya dani kuma za'a je. Sai da naji kaina yayi bugu na secnds kafin na dago murya na a karye nace ammuh har ibadan? Tace min yes baahi,and you have to get ready now,daga nan ta tashi ta fice sojan na biye da ita Wani sauke ajiyan zuciya nayi na shiga bathrum Haka dai na tattara kaina a sadade duk dama banajin dadin abun amma haka na shiga shirya kayana Ko wani minti 10 daga fitowa daga wankar banyi ba aka kwalla min aika daga waje na fito. Ammu ne kawai agaban manyan motoci kirar GTR i8 bakake har shida da aka shirya zasu kaimu aiport dan haka ita ta rungume ni tana min Allah ya dawo damu lpya. Ayayin da ogana ya fito kowa ya shiga hankalin sa,motar dake kusa da tsakiya daga karshe ya shiga nikuma aka kaini na farko tare da security arm da driver har muka kai aiport Duk da private plane ne kuma babu kowa daga ni sai shi Anan din ma ina daga bayan seat din shi shi kuma yana zaune agaba air hostess tana famar jigila da fitinan shi. I was like chan muku,jim kadan sai gashi mun sauka a oyo,ibadan state. Anan ma wasu bakaken motocin kirar mesarati su suka zo suka dauke mu. Munsha nisan tafiya daga nan kuwa dan Ba a tsaya ko ina ba sai da muka kai wani haddaden estate wanda ake masa lakabi da white house. Tsaban kalle kalle na Ban lura da kyau ba har sai da driver na yace min mun iso Anan ma cikin wata katafaren gida aka sauke mu,nikam sai danayi kallo mai isata. Dan kuwa its a huge transitional building,wato gida mai dauke da both modern and traditional structures. Masha Allah as we walked in mutane daban daban ke wulgawa cikin uniforms dinsu kowa na harkan gaban sa. Ji nayi an dafa ni ina waigowa naga wata mata tana murmurushi nima sai na mayar mata. Tace bahiyyah? Nace yes maa.. Tace ok zo nan,banyi gardama ba dan kuwa ta kusan kaiwa ammu adama agirman jiki da dattako, nan dai na bi bayan ta zuwa wani shashi,inda ta kaini cikin wani daki mai shegen kyau Tace ni sunana aminah u can called me nanah A..im the chief maid here. And This is ur room.. Nayi murmushi, na amsa ta ganin kind gesturen ta nace ok nanah A nagode. Murmushi itama ta sake min" Kiyi da jikin ki ki fito pls,u have alot to do hala ku koma kanon gobe" Da sauri na ansa mata da toh na shiga kimtsa kaya na Daga nan ma Bathrum na shiga na watsa ruwa A Lokacin yunwa kamar zai kashe ni dan banci komai ba tunda muka dauko hanya,nan na fito na sanya simple jallabiya ina neman hanyar kitchen ina kuma dada kare ma gidan kallo dan shima ya hadu babu karya Sai dai har yanzu ba damuwa ta bace Nasan me muka zoyi gashi tunda muka zo ban ma ganshi ba. Ina sharo kwana kuwa Cikin sa'a muka gamu da nana A tana haurowa site dina. Na dada gaishe ta,itama jawo ni tayi muka shiga wani shashi mai girma sosai. "...Ashe ma a private part nake ban sani ba maybe ko dan anan shima ya sauka so babu hayaniya. 'Da muka fito sarari yanzu ne nake ganin asalin mutanen dake gidan... Its actually one of his mums personal houses, ita ma idan tazo wani abun a ibadan anan take zama duk dama gaba daya estate din da sunan shi tayi signing. Anan ba kowa sai nanah A da sauran ma'aikatan gida tsawon lokaci suna lura da komai "He is here for an important 100 billion dolla national security meeting wanda za'ayi shi gobe da safe karfe 10 tare da taron duka wersten kings, obas and govenors of nigeria. Muna sauka daga part dinshi nanah A tayi da ni kitchen a wani sashi,Kamar wanda take kallon hanjin ciki na Tace am sure ure hungry"na gyada kai na asaukake. Sai Tayi murmushi ta bude wani katafaren food store iya kallon idanu na Tace here!! sai dai ki tabbata ko wani abinci zaici awaje kina wajen,ki fara tabawa kici kiji, kar kiyi kuskuren sakewa har wani ya saka masa poison. Na gwalo ido Nace ehm?Saura kadan nayi blurting out loud but i kept shut,so idan ma poising din ne nina fara mutuwa kenan ko?.... Chaii this ppl are funy. Ban dai ce komai ba har ta gama shimfida min dokoki kusan iri daya ne da normal aikin dana saba mashi a chan gida kano So i can quickly memorise everthing. Kafin na daura girki muka koma ciki, Anan ta gwada min dakin shi da sauran part din kafin ta kyale ni tayi gaba I stood there staring ina ta kalle kalle kamar wata fatalwa,dakin Bai dai kai na chan gida a kano girma ba amma yana da girman shima sosai. "katoton Kingsize bed ne da tufted head boards crown molding over walls tare da white ceilings sai wasu golden drapery curtains da tarin stylish funirtures. Tabe baki na nayi na fito na shiga hade masa abinci kodan na samu nima naci ko naji dai dai ajiki na. I did evrything accodingly babu wani matsala dan gidan sam babu hayaniya. Its seems like Yana busy dan haka daya kammala cin abincin ya shiga daki ban sake jin shi ba. Washe gari da sassafe nana A ta shigo daki nah, Bayan mun gaisa take cemin Nayi sauri na hada mashi abincin safe ta dada jadadda min karfe 10 ne meeting din shi, Ta kuma cewa Khaldun ya bada umarni in goge floor din dake kofar dakin shi Nasha mamakin wanan oder, dan nasan bana irin wannan aiki . Amma sai nana A tace min ai anan gidan babu mai shiga shashen sa sai ita,yanzu kuma nine dan haka ni zan je na goge. Nace mata babu komai Ban wani daga hankali ma ba na saka rigar material ja da baki nafito kitchen na shiga na fara hada masa break fast Bayan nayi serving dinshi ban tsaya ba ya sallame ni sai na je hada mashi ruwan wanka Anan sai na lura bai sha tea dinsa na safe ba,.. Nayi sauri dai na kimtsa na fito still banganshi akan dinning din ba na duba naga anan ma ko taba abincin baiyi ba.. Strange! Zuciyata tace ina faman tattara abincin zuwa kitchen. A hanya muka ci karo dashi duk da ma nayi saurin rusunawa adaddafe bai hanashi daura min wata muguwar harara ba. Drop it and come Yace ya wuce Nayi sauri nakai kwanukan kitchen na dawo zan shigo dakin san sai naji a kulle yake gam gam Dan wulakanci haka nayi ta knocking yana ciki yana ji har sanda na share mintina talatin ina tsaye kafin ya bani izini na shigo A gaban wato sharbaben full size mirror na ganshi Combin kansa yake da soft hair brush Dan Baiko bani daman daidaita tsayuwa ta ba naji yace min Almond cakes and orange juice Daga nan bai kara cemin uffan ba yayi shiru. Wani rau da idanu nayi I was like New breakfast oder kenan?hmmm kirjina ne ya biga Ayayin da na ja kafata nayi hanyar kitchen na masa exact abunda yake so. Fresh orange juice with spicy almond pan cakes na hada mashi da cool raspbery desert. A tsanake yake ci yau kam ya taba duk abunda na ajiye masa. Ina tsaye daga gefe ya ajiye food napkin din ya gama goge bakin shi ya kalle phatek philp din sa ya dubi time. Kinyi aikin dana saka ki? Da sauri Nace ah'a Sai Ya dan tabe baki Yace 9,45am u wll get my dresses.. Kafin na gama amsa shi yayi gaba ya haura dakin sa. Da sauri na kimtsa komai banma iya neman wanda zasu ci abincin daya bari ba sai na juye a wani warmer na jika ruwa a mopping duck na taho inda yace na goge din Daf da kofar dakin shi ne
Chapter 18 · 0% Book details