Sashe 89
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_ _Bismillahirrahmanirrahim._ -bonds Da fushi junnut ta nufi dakin ta bata sake kula kowa ba. Bahiyya taso tabi bayan ta amma anty murjan sai ta janye ta suka bar site din dan dole Ta kasa zama sai juye juye take, tsaban ruwan ciki sai taji kasa ayyana komai sai jeka ka dawo take tana karkada phone din ta tana tuno da guts irin na hjy indirah Cikin ranta tace wannan wata irin tsegeriyar mata ce,ita tunda aka haifeta bata taba ganin mai furta kalamai yadda taga dama masu dilshad ba sai yau.. Who is this woman?Cikin wannan zulumin wayar ta yayi kara kawai sai ta amsa tana kammalawa ta dau jakarta ta fice agidan.. Bangaren su bahiyya kuwa zama sukayi da anty murja tana dan studiyng mood din ta she understood that diyar shiru shiru ce,kan kace kobo kuwa har ta capko tashar ta. To Ganin shirun nata yayi yawa yasa tace,gimbiyata muje ki nuna min site dinki kafin hjyr mu ta dawo.. Babu tantama bahiyyar ta mike tana dan sake mata sassaukar murmushi nn ta ja ta suka shiga zaga site din ta da khal har dakin bacin ta ta kai anty murja ..anan suka dan ja time ant murjan tana dan jefa mata hira tana kare ma dakin kallo. After like 30minuts suka rabu,toh bata sake ganin su sanda ta musu dinner,ta dau wanka tayi kyau har tana waswasin zuwa sashin nasu da kanta batare da maids ba. Haka dai ta daure ta je..babban site ne kusan irin nasu,2 main palours da manyan royal bedroms guda hudu..tana isa kuwa taga suma sun shirya tsaf cikin shiga ta alfarma. Bata cika saka atamfar ba amma just today taji shigar su ant murjan ya burge ta...komai da ake bukata ajikin mace sukan cike shi tsaf akowani fitowar su Wankan yamma ne amma hjy indira tasha gwalaglan ta yan dai dai mai abun wuyar sa ga gold ring din ta masu dauke ido a hannun ta suna haskawa. atamfar ta tasha dinkin mai zubin silver stones ta kuma yafa babban mayafi sharara ajikin ta tana kime akan center chair tana latsa babban inote din ta..aunt murjan ma waya ne a hannun ta sunyi shiru wajen ba hayaniya.. ..Sallama alaikum.. Bahi ne ta shigo da sanyin sautin murya, idanun ta adan sauke kasa fusknta na mai fallasa asalin ladabtaccen kunyar daya dace da fuskn kowacce ya mace kamila Dan Kallo suka bita da shi har ta gama gaishe su ta kuma shiga serving dinsu abuncin data zo da shi din.. ..Anan take dada sanin cewa hjy indirah jini ne na kusa daga asalin dangin mahaifiyar alhj hamood. ..itace kamar step sister mahaifiyar shi kwalli daya data rage masa a duniya An haifeta amma a Lokacin alhj hamood yana hannun sarauniya dilshad a matsayin dan riko ...daga nan mai gaba daya da ya rasa kakan nashi alokacin ita kuma hjy indirah bata girma ba,qaddara ne yasa ta yi zaman kasar nigeria acikin garurruwar su daban daban kamar ibadan,lagos,kaduna da kano,anan nigeria din har tayo aure ta haifi yarta kwalli daya mai suna murjanatu wanda suke kusan saa da khaldun saood. Toh Gabanin bahi ta shigo rayuwar su jahan Aarah,murja ta yi gamu da sharrin kishiya mai tsanani wanda ya jawo sanadiyar mutuwar 2 years aged mariage din ta,jinyar aljanun da kishiyar ta jefa matan shi ya dauki hjiy indirah kusan shekaru biyar suna zagawa kwaro kwaro suna neman mata magani har Allah ya sa sukayi dace. hjy indirah asalin jinin persia ce,amma dabiun ta da duk wani shigar ta na yan nigeria ne Ta girme jahan Aarah da shekaru 5 na haihuwa,duk dama A kusan lokaci daya suka haifi yayan su na fari wato Murja da saood. Sannan ita ta xama kamar uwar daki da uwar amana ma jahan Aarah a lokacin da ta zo nigeria da cikin saood bayan rabuwar ta da chan persia cikin kangin sarauniya dilshad.. Dan haka Duk wani halin da suke ciki ta sani,ita ko kadan bata jin shayin fuskantar sharrin dilshad khatun har fiye da sanin kowa Ayanzu ma jahan Aarahn ce takai mata kukan ta akan auren bahiyya da saood.. Jahan Tayi mata bayanin komai game da yadda akayi auren har suke boye shi ma su dilshad,ita sam ba haka taso bahi tayi rayuwar ta ba.. Taso ne tayi mata gata wanda kowa ina ya gani basai an fada ba zai ji ajikinsa cewa ita ma kamar asalin uwace ma bahiyya.. sannan ta kuma nuna mata tsoron data ke kwana dashi akan zaman bahiyyan acikin su dilshad khatun din Tasan su gaba da baya Ahalin sa ake ciki Tun da bahiyya ta bar kano hankalin Jahan Aarah bai taba kwanciya ba ..gani take kamar bahiyya zata fuskance zuxguni da bakin rayuwa a hannun su dilhad kamar yadda itama ta ji jiki da su Kuma ita bata san hakan ya faru shiyasa bata boye ma hjy indiran ba ta gaya musu labarin komai ta kuma jadadda mata cewa bahiyyar marainiyar Allah ce bata da kowa sai su.. Tun daga nan hjy indirah ta dauki alwashi cewa zata zo abuja ta zamto kariya ma bahiyya har sai an samu kwakwaran fahimtar juna game da boyayyen auren sun agaban dilshad.. Anan Bayan sunyi hira kadan,tace ma bahi yata kije ki kwanta zanu huta sai gobe zan shigo inda kike in duba ki.. Ahaka sukayi sallama bahi ta koma dakin ta ta shiga shiryawa bacci batare da ta kawo komai aranta ba Bangaren su Junnut Kuwa hirar hjy indirah kawai suka wuni yi ita da hilda acahn dakin su. Ba irin maganan da basu fada ba Tsaban diri hilda har cewa take da ita ce aka mara da sai ta rama marin ta a duk dama ta dan sha mmakin yadda junnut take bada labarin tsegerancin irin na hjy indira agaban kakar nasu Washe gari da safe ranar jumaa ne dan haka tun da bahi ta farka sallan fajr bata sake komawa ba tayi zaman ta tana karatun qur'ani tana hadawa da azkar bata tashi ba har sanda zaren hasken rana ya faso .. Wanka ta fada tana mai mutsuka mayukan wanka masu shegen qamshi ma fatar jikin ta cikin tattali da iya tsari.. Ayau tana jin xuciyar ta very light dan kuwa ba karamin nitsuwa ke shigo mata ba.. Bayan ta dauraye jikin nata ta daura light blue body towel da wani fari dan dai dai akan ta dan yana tsantsame mata ruwan dake bin sumar kantan.. Wani heavy knock yasa ta isowa bakin door din da sauri tana isa ta bude batare da ma ta tsaya tunanin waye abakin kofar ba ... "Hjy indirah ta tarar,Suka kalle juna tayi saurin kau da idanun ta dan kunya, a ladabce tace barka da shigowa hajya...ba yabo ba fallasa hjyn ta kalle ta bata ce uffan ba ta maida kofar ta rufe ta shigo. Yau doguwar rigace ajikin ta puss pink amma ta lullube kanta da mayafi dan dai... Kwaliyar hjyn kullum abun burgewa.. Sit down ..ta fada a nitse tana mata nuni da dressing chair dake gaban standing mirror...a sadade bahin ta taho kamar mai jin tsoron taka kasa ,silently ta zauna cikin jin sanyi da kunya tana dan jan towel din ta kasa kasa cikin dabara dan ya dada rufewa zuwa rabin cinyar ta Hjy na lura amma bata ce uffan ba sanda ta ga ta nitsu,tana daga bayan ta daf take kallon ta cikin madubi...bata wani sake fuskn ta ba tace yata ashe haka kike attending doors dinki batare da kin rufe jikin ki ba?..so what in nan sashin mijin ki..to yau ya zamto rana na karshe da zakije bakin door da body towel muddin ba muryan mijin naki kikaji.. Bahi sai ta sunkuyar da kai..cikin ladabi da sanyin murya tace ayi hakuri hajya insha Allah bazan sake ba ...Mayukan kan table din hjyan take dan dubawa slighly Tace good...jiya bamu samu dama munyi magana ba kinga ni tsohuwa ce duk na nagaji..but yau ya kamata kisan bakuwar taki ko? Bahi ta gyada kai Sai ta mika mata body toner tace to shafe jikin ki kar ya huce..,ta lura bahi tana jin kunyar ta sosai dan bata sake ba...bata damu ba ta shiga tattala ta slowly tana kuma sa ido tana ganin yadda take shafa mai da turare tana gyara mata inda bata iyayi da kyau ba.. Ita ta warware mata jikakken suman kanta ta busar da shi da kyau da handryr sannan ta nuna mata hanyoyii kala kala na yadda zata gyara suman kanta ta yadda zaiyi qamshi da kyun gani,a step by step.. ita kanta bahi sanda taji ajikin ta cewa a hannun gogagiyar mace take.. Sunfi 40minutes suna gaban mirror the same hirar jiya da sukayi shi hjy ke mata jifa jifa tana dan mata gyara da nasiha game da yadda zatayi tattalin kanta akasaitan ce. .. Sanda ta sa ta yi dressing ta gani ,sannan ta kuma nuna mata salon saka kaya daban daban wajen ya mace kala da iri Bata kyale ta ba sanda tayi mata gamsashun lectures Tun Daga kan yadda ake saka inners, bra pant shots nitys,kananun kaya,manyan kaya da duk irin choice din kalar daya dace ta sa a lokacin daya dace da wanda bai dace ba.. Choice of perf and make up..anan ma ita ta ke sanar da bahi cewa a kullum idan ta yi wankan safe to maza ta nitsu ta tsala kwalliya ma mijin ta,acewar ta maza sunfi ganin tasirin wankan safiyar nan da kuma kwaliiyar yamma fiye da na ko yaushe idan sunzo hutarwar su. Tace kar ki dauka ko evrything da zakiyi danki burge mijin ki is much,kisa duk abunda zai fito dake ki hadu sosai ba lallai sai zakije biki ko wani hidima ba. Tace yakamata Kisan choices din gwalaglwan da zasu dace da kwalliyar zaman gida da wanda zaki fuskan ci taro da shi.. Make sure that baki rage mijin ki da komai ba ta inda duk inda zai daga ido ya kalle wata mace sai yaga banbancin ki da ita Koda mijin naki ya nuna bai damu ba dont just give up,tace shi kwalliya da tsafta da iya magana shiine kadai ke kara wa mace daraja a idanun mai gidan ta.