Sashe 25
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ankawo karar ta cewa tayi mummunan abu ba. And tunda taga khaldun bai kore ta ba to lallai yarinyar akwai hakuri Subaya kam is super excited already she cant even wait to call bahiyyah her sister. Bangaren Khaldun kuwa ko sake kallon su ba bare yayi responding haka Kuma ya tashi ya bar su a dakin suna ta fayyace fayyace. By noon suka tattauna su uku da jahan da subaya da Alhj gen hamood ta video call Inda ya basu goyon baya dari bisa dari akan tunda sun gamsu da halayen ta kawai suyi adopting din bahiyyar ta dawo one of the hamoods. Murna wajen subaya kamar zatayi tsalle,dan sosai take jin bahiyya aranta duk dama bata zauna da ita ba. Washe gari koda suka sanar ma khaldun cewa za'ayi adopting bahiyya shiru yayi daga bisani yace shi babu ruwansa da wata bahiyyah... He object the fact that yarinyar dake masa dafe dafe ce za'a laka masa dawowa yayan ta. Yama ki shiga zancen Kuma Dan dolen su suka kyale shi. ***** Nikuwa Ummah adama ita ta dinga bani shawarwari tun kafin su jahan Aarah du tumtube ni akan maganan. Tace min Allah ne ya kashe ya baki bahi...dan haka idan suka kawo miki maganan adoption maza ki amince Anan har tarihin kywawan halayen su sai da ummah adama ta bani. Kamar wasa aka kira ni a sashen jahan su biyun suka tambaye ni ko zan amince da qudirin su! Babu abunda ya bani sha'awa kamar yadda Jahan ta bani tabbacin cewa kar na amsa su dan na faranta musu ko dan tsoro domin kuwa maida ni cikin jinin su ya wuce yanke hukuncin cikin wasa. Sai kawai na amince nayi godiya sosai harda kuka mai ban tausayi Nan suka jawo ni for the first time duwawu na ya zauna kan lallausan chairs dinsu.. Da yamma aka kira ni again babban lawyen alhaji gen hammod ne ya ziyarce gidan Domin aiwatar da proper official adoption procedures Anan aka maida suna na asali wato bahiyyah Ahmad alba kafin aka sa HAmood a karshe. My file name was reading bahiyyah A. hamood Sai Aka bani official papers din adoption nayi signing Haka ma na family property and rights da suka bani kyauta duk na sa hannu. Wallhy ji nake kamar mafarki nakeyi dan ko murmushi bana iyayi sai yake. "TAbbas Tsarki ya tabbata ga ubangijin mai yin yadda ya so, shikenan fa rana daya na dawo cikakkiyar doughter of gen hamood and jahan Aarah, Sister to a brigadier genaral khaldun sa'ood and his sister subayah. A take rayuwa ta sauya min,ranar kwana nayi ina godiya ina salloli Na tuno ammu abbu da junnut sosai har na rasa wani kalman zan faranta ma ubangiji na rai da shi. Kawai sai na daura niyyar yin azumi guda daya batare da na fada ma kowa ba. Haka ammuh adama ta sake maida ni wani site daban wanda yake asalin cikin sashen da jahann Aarah da su subaya ke zama. Nima yanzu inada whole flat site mai dauke da wata kafurar neutral background. Ko ina An tsime shi da monochromic additives,dark beige drapery curtains,a tsakiyar space din dakin akwai stylish ottoman bench mai square pattern Tv sets da katoton silk bedding with plenty maching cushions da cubic headboad agefe. Wayyyo duniya sabuwa.. Closet dina kawai wani dakin ne mai zaman kansa... Duk da yadda abubuwa sukayin kyakwan juyin masa,sai dai Ban taba komai ba tukun don jikina ko kadan bai sake ba. Umma adama ce ma tasa ni dan dole na dauki daya daga cikin doguwar rigunan abaya dake closet din na saka sabida nasan na shiga wani matsayi arayuwa, da shike da azumi abaki na sai ban fito ba nayi kwanciya ta. Ina farkawa As expected subaya ce na gani,cike da fara'a ta rungume ni tana cewa happy sisters day" Sai da na tsinci kaina da mayar mata da dariya Ta riko hannu na tace min,ki sake jikin ki kinji ,mum is already calling Zakuyi magana da dad Wani dam naji kirji na ya buga,sai nayi yake kawai nace toh muje.. Tana gaba nabiyo bayan ta,na samu khaldun na zaune awajen alaman magana sukeyi har zan zauna kasa jahan tayo saurin riko ni tace kar na rusuna .. Nikuwa Duk hankali na nakan sa shi ko kallo na baiyi ba Har ya gama amsa wayar sa ya tashi ya fice abunsa I was lost in tot of him,gani nake dan banje aiki site dinsa ba nakeji wani iri ko yaya yau ya yi?waye ya dafa masa abinci oho? Come here BAhiyyah Jahan ce ta tsare min tunani da mika min waya Anan Dukan su suna ji Mukayi magana mai cike da girmamawa da Alhj hamood Shima karfin gwiwa ya dada min harda tuno min cewa na taba kiran sa mahaifi na a da chan dana taimake shi dan haka shima yanzu na dawo yarsa na har abada. Hawaye na su suke dada nuna musu sincerytin godiya ta. Dan dole na na sake da su, yanzu na fara ce ma Subaya big sis.. Jahan Aarah kuma ta sakamin suna mai dadi wato BAHIYYATUL NOOR. Sai aka dawo cemin baahi, ko ace min Noor bahiyyahn ma ba kasafai suke kira na da shi ba Duk wannan hidiman mu ukun mu muke yinshi sai idan alhj hamood ya kira gashi sadaat mijin subaya baya nan Yayi tafiya. Tun ranar ba wanda ya sake cemin nayi wani aiki agidan amma zuciyata cike take da damuwa da yadda khaldun saood ke yi anashi shashin He dindt say a word about me Ni dai nasan bai amince da ni a matsayin yar uwansan bane. Gashi haka kawai nake jin i really missed him,i wanna be with him ko da kallon sa nayi Bayan kwana biyu Jahan ta kira mu da rana da shike khaldun da ita yake yin lunch kowa ni lokacim Wani daure fuskn sa yayi da yagan mu akan dinning table da alaman fada jaahan tayi masa akan kin accepting dina dayayi.. Nikuwa ko iya hada ido dashi banyi ba Amma sosai naji dadi dana gansa ko na komai naji sauki Gashi dan kwana biyun kacal danayi cikin gata har kalar fatar jiki na ya fara amsa sabon ya nayin daula da ake zuba mashi. Bayan mun zauna Anan Har jahan ta kare Maganan ta ba wanda ya amsa fiye da subaya. Last last cewa tayi zata yi tafiya akan zata je kasar turkey.. Wayar sa nayin kara ya mike tsaye "Ya dora mata kiss a goshi yace safe jouney mother".ya hade rai bai jira amsa ba ma ya tafi abunsa. Bayan sun bishi da ido sai duka suka dawo suka kalle ni,kaina akasa yake dan nasan muddin ina waje nasan he will remain pissed off. Fuskata ya nuna damuwar hakan Amma bansani ba nadaiyi shiru na sunkuyar da kaina kasa.! Har Subaya zatayi magana Jaahan tace wait sai ta kira sunana cikin lallami tace Baahi? sai Na dago a sanyaye Nace yes ma.. Tace kar ki daga hankalin ki,zai saba da ke amma ba yanzu ba ko!.. Sai Nayi murmushi nace bakomai na fahimta. Sai dai alfarma daya nake nema Tace mebene? Jahan pls ki bari na cigaba da yi masa aiki kamar yadda na saba masa da chan. With full objection jahan tace a'ah ban amince ba Bazaki yi wani aiki agidan nan ba Ban taba sanin inada liver ba sai yau Tsintar kaina nayi ina ce mata,zanyi hakuri da khaldun ni dai Tayi hakuri ta barni nayi masa aiki dan nafijin dadin kula dashi fiye da dawowa equal dinsa Besides am his sister now duk abunda zanyi mashi is out of family bonding so no quest. Da wannan kalmomin nawa sai na burge su matukar burgewa Duk dama da kyar jahan ta amince subaya har da cemin zata rinka ta yani wasu Abubuwan domin mu jawo shi har ya aminta dani. "Cike da raha da fahimtar juna muka watse kan tebur Karfe 2 Jahan Aarah ta bar kasar nigeria zuwa turkey. So washe gari da safe khaldun saood ya sha mamaki ganin nayi resuming duty sai dai ko kallon arziki ban samu ba bare cikan ki! Daga yadda naga yaci abincin sosai I can tell that he misses me too. Naji dadin hakan araina,dana gama mashi komai sai na je dakin big sis subayah,she was all excited murna take sosai kawai dan mijin ta sadaat zai dawo. Anan nayi wanka har ta koya min salon hade haden bathing gels ta inda zai goge min fata na nayi kyau nayi tass Anan na fahinci Wanka ma iyawa ne fa,dan akallah abubuwan tttala jiki dake bathrum din mu yaci ya dauke ka awa biyu yana wanka bai gama ba Haka ma ta cancada min kwalliya ta koya min yadda zan nayi,gashi nayi dan karan kyau Da shike ina kama da Ariana grande sai kawai take bin salon parking gashin ta kamar yadda takeyi alwys on pony tail Idan ta tattala min shi sai ta sake sauran jelar cukun ya zube abaya na Yau ma Doguwar abaya bakake muka sa iri daya sannan mu kaje shoping mall. We had fun,har sai da naji ina kaunar big sis subaya sosai Dan kuwa tsakanin ta da Allah ta bude min zuciyar ta tana jan ajikin ta Munyi shoping kamar wanda zasu bar duniya. Ina da komai agida amma Komai ta sake siya min,shoes bags,make up lingeriea da jewries gani take kamar zabi na zaifi min Haka ma iphone11pro din kamar bai ishe ni ba ta kara min da samsung galazy x10. Cikin wata kafurar jeep kirar jaguar ake tuka mu Dan dole na na koyi surutu dan kuwa subaya is quiet intresting and jovial... Tun da muka dawo Gidan shiru,tana dakin ta tana shirye shiryen tarban mijin ta nima ina daki na ina damar tausasa kaina domin har yanzu zuciyata tana dauke da fargaban abubuwan dake faruwa dani wani bin sai naga kamarr duk karya ne But I have no choice than to accept my new life this way. Wanka nayi irin yadda big sis ta koya min My choice of body wash was makari,honey,goat milk set nivea,da wasu set of papaya scrub banda ma hand wash feet wash knuckle da under arm and pits Wasu abun ma bansan su ba.