Sashe 49
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ _Bismillahirrahmanirrahim._ -the venom Tun Tana daga serving spoon ya dakatar da ita ya amsa yana cewa let me have this.. A sanyaye ta sake mashi tana bin shi da kallo dan maganan kawai yayi amma bai wani kalle ta ba. Bowl din Abincin ya sauke kasa ya aje kan lallausan chinesee rug carpet,a hankali taja mashi center table din gefe dakyau sai yace mata sit ta zauna,Serving Plates guda biyu ta jera amma da guda yayi amfani a nitse har yayi serving din su,kallon shi take satan yi but to avoid being cought sai ta yi kokari ta shiga zuba musu smothie a two cups kowa da nashi Wani shiru Wajen ya dauka da suka fara cin abincin,its feels like heaven dan yayi kewar abincin ta sosai,shikam babu wani alaman jin kunyar ta dayakeyi dan cin abincin shi yake yi normally itace inta kai loma daya sai ta dan jira kafin ta kai na biyu. A farkon wanda ya zuba musu ya kare sai ta dada kara musu Taga gogan bai dakata ba har suka ci abincin sau biyu..Dan kadan ya rage sai ya jawo smoothie din ya kai bakin sa..,itama dan tura abincin gefe ta yi niyyar yi ya wani balla mata harara bai ce komai ba Bata daddara ba ta dan tura kadan,zata aje spoon yace"eat up"..duka zaki cinye..wani yamutsa fuska tayi cikin sautin shagwaba tace nifa na koshi ne.. Bai kula ba ya tura mata abincin ya dada balla mata harara,"u most eat all of it,baki da ido?baki ga kin rame ba?kaiwa nan ya kau dakai ya cigaba dashan abunsa shiru. dan shirun itama tayi tana kallon sa a sanyaye ta jawo plates din ta tuttuura sauran abincin acikin ta badon taso ba,sai da taji tayi dam har ta kasa mikewa. Shikuwa Tashi yayi da cup din a hannun sa ya koma kan cushion ta mike kenan xata tattara plates din ya mata nuni da remote akan ta miko masa kallo ya kunna ya hakimce,nan taje kitchen ta gama tsaftace ko ina ta goge wajen tsaf.. A hankali ta bude door Tana dan lekowa suna hade ido ,sai yadan kau dai ba yabo ba fallasa yace fatan kinyi sallah? Ta danyi shiru sai shima yayi shiru cos baisan ko ya dace ya mata tambayar ko bai dace ba Doguwar Rigar material ne dama ajikin ta fari mai manyan rose flower pattern,a sadade ta wuce shi ta shiga bathrum ta wanke hannu da fuskan ta tsaf sannan tayi tsarki tayi alwala,data fito kallo daya yabita da shi,batare da yace uffan ba sai yaga ta canko in da direction din gabar ta tsaya, dan hair scarf din tan ta dada lullubawa akanta ta tada sallahn azahar. Toh Dama karfe uku na yamma ya dan wuce Almost 10minutes tana zaune a position din da niyyar jiran lokaci dan ta hada da laasar,tunanin yaushe ne ya dace itama ta fada mashi zata tafi? Sai yanzu ma tafara tunanin nashi tafiyar,she just dont know why he dint say anything again Daf lokacin sallahn ya mike tsaye shima Tana gani ya nufi bathrum din a lokacin ta fara nitso cikin tunani kala kala ciki kuwa harda tunanin yadda zata fayyace masa abubuwan dake faruwa tsakanin ta da sadaat da big sis subaya. But its becoming hard a zuciyar ta,sosai abubuwa daya na waswasi suke shigowa,bayan su dija da suka san komai kuma suke ganin komai bata tunanin akwai wanda zai yarda cewa sadat na mata haka. "...game da maganan sirrin dake makale da auren sadat da subaya kuma bata san ya khal zai dauke maganan ba"... ,banda yau counting as an unsual moment har cikin ranta bata taba tunanin khaldun dakansa zaizo inda take ba bare har ya bata lokacin sa haka ba. Ahaka ma Ita sam Bata san me nufin sa ba,yazo musamman dan ita kanwar sace koko wani dalili yasa shi ya waiwaye ta? taga yana tausaya mata kuma ya biye mata fiye da yadda ya saba da chan amma ko kadan bata aminta da komai daga gare shi ba. More than anyone tasan halinshi ta dde da sanin cewa a murde yake,tsoron ta anan shine kar ta fara gaya mashi damuwarta yayi misunderstading dinta har maganan ya dawo musu wani babban matsala Aganin ta wannan Maganan babba ne, Ko ba don cin amanan da sadaat yake shirin yi akan subaya da ita ba,tunanin ta Ta yaya khaldun zai dauki maganan asalin mugun burin sadat akan subayan cikin sauki batare da wani kwakwaran shaida ba.. Bata da komai a hannun ta da zata iya nunawa Not even phone calls or mesges sabida sadat always has his ways bai taba kira da number sa ko in anyway ya farmata da real identityn sa ba kuma kullum acikin razanar da ita yake da barazanar sa na cewa tayi duk abunda zatayi he is evrywhere. Cikin juyayin tunani tace"How can she explain all this to khal?He is not a little child,..tsakanin ta da shi daban bancin duk tsiya tasan subaya ce jinin sa na asali ba ita ba,magana da fatar baki kawai wont be so easy for him to take.. gashi anan dai su biyu tasan babu mai karban ta inta kwafsa Gyaran muryan shi akanta ya hankarar da ita,fuskan sa da alaman ruwan alwala alamane na zaiyi sallahn la'asar. Mikewa tsaye tayi ta dan kurkura baki tafito sai ta samu ya juya mat din itama sai tayi sauri ta hau ta gyara zaman mayafin ta Bayan ya tada ikama,cikin nitsuwa ya fara jansu tare cikin wani kamilallen sallah mai cike da tarin abun duba,dan kuwa sosai ta gane cewa ashe shima A ne ta wannan fannin. Gashi daki daya ne a gidan ba ta inda zataje tayi wani abun ita kadai... aranta kuma tana mugun son taga ta fayyace masa komai. Bayan sun idar,shikam kan cushion ya koma yana amsa waya da mr pilot anan takejin yana cewa sai gobe zai tafi. 'nitsuwa tayi adan dofane akan gadon ta shiga texting din su jasmine ko da zata ji yadda suke ciki sannan tana mugun son su tayata yanke shawara akan maganan Hakan ya dauke mata hankali for the main time,musu sukeyi kowa na bada point dinsa in one way or the other confusion har ya shiga hidiman sosai. Cikin nazari har ya zame ya fita bata wani lura ba sanda wajen ya dada daukar shiru ta dago taga wayam babu shi a dakin..dan kwafa tayi ta mike kafan ta akan gadon,wani story book irin bedtime short stories ta dauka tana karantawa a nitse yana dan debe mata kewa "..har sai chan 10pm na dare toh da bata gansa ba sai ta dada sakewa a kan gadon tadan kwanta ta jingine tayi shiru Juyi take Cikin wannan yanayi wani iska mai karfin bala'i ya huro drape curtain a firgice ta juyo rike da kirjin ta daya buga lokaci guda..,tana kuwa juyi kallon bakin windown idanun ta suka kafe sukayi fari, a Wani duniyar ta tsinci kanta. Sai ta ganta gata nan tana tsaye da kayan jikin ta daga nesa tana hango wasu mutane bakake kirin zaune agaban wani katon tukunya mai ci da wuta Tayi ta lekowa tana dube dube amma Bata gane fuskan kowa ba,sai dai tana jin abunda suke fada sarai. Wanda ke zaune gaban tukunyar hannun sa dauke da wani bakar muciya yana tuka wa shi yace ma bakar kurwan sadat"...na kira ka da gaggawa ne sabida yarinyar tana da taurin kai zata bata maka sa'ar ka,. Zata tona maka asiri,dole ne kasan yadda zaka yi da ita yanzun nan. Wani magana akayi kasa kasa bataji ba kuma ita bata gane cewa sadat bane awajen sabida babu kamannin sa a jikin halittar Kafin kace kobo har sun iso gaban ta kamar kiftawar bismillahi,..cikin wani yanayin tsoro ta ja numfashi jikin taya hau rawa tun kan ta dawo daga firgitan da tayi mutumin ya takarkare ya doke tsakar kanta da karfi da wannan muciyar sai battt taga ta dawo dai dai bakin ta yana furta Innalihhi wa inna ilahi rajiun. wani mumunan tsoro ne ya shige ta,ta rike kai kamar zata tuno abunda ya faru yanzun amma minti 2 baiyi ba ma ta dawo normal,komai ya goge kamar ba ayi ba,Tsikar jikin ta ne kawai ya ke tashi. Dare na dada yi Lokacin hanjin cikin ta ya gama kadawa da tsoron shirun da wajen ya dada dauka haka kawai taji wani fiirgici da fargaba ya nakasa zuciyan ta bayan ta ga lokaci yayi nisa sai ta fara kai kawo tsakanin waje da cikin compound din gidan amma shiru bata gan dawowar sa ba. "A Maimakon ta cigaba da tunanin yadda zata fada ma khal matsalanta kamar yadda sukayi shawara da su jasmine Sai ta tsinci kanta da jin wani tsinannan mantuwa game da issuren mai gaba daya bata iya gane komai.... ayanzu Damuwar ta bai wuci tuninin How can she sleep outside schl ba dan Ko da wasa bata taba skipping kwana a wani waje ba inba dakin su a hostel ba. Karshe dai dawowa dakin tayi ta koma kan gadon ta zauna Da Har zata bude book din again sai ta bari ta kife shi abude wani Lumshe ido tayi ta jawo pillow zuwa karjin ta kamar mai bacci tayi tsammm tana kokarin regaining memoryn ta amma duk abanza. Jim kadan dayin hakan taji saukan wani lallausan hannu akan goshin ta,tana dawo wa cikin senses din ta kuwa ta fahimce cewa shidin ne daff da ita yana kallon fuskan ta..,wani kara kulle ido tayi gam gam batare da tasan dalili ba har ya gaji da kallon fuskan na ta ya zame ya same waje ya zauna daf da ita akan gadon Dan kadan ya juya ya kalle ta,cike da kulawa yace Bahiyyah! Taki ta motsa sai yayi tapping gefen gadon da palms din sa,r u sleeping? sorry for keeping late ... ya furta a takaice Dan karamin boyayyen ajiyan zuciya tayi Tana bude ido a slow sai suka hade ido da shi tuni wani yanayi ya jefa su cikin kallon idanun juna ya gama lura da halin tsoron datake ciki,...hakan na damun sa amma sai ya basar.. Sai Ta gaishe shi ya amsa yana dada gyara zama kan bed