Sashe 69
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._ _Bismillahirrahmanirrahim._ -the secret of our weding Wani irin Kallon juna sukeyi,kowa yana makale da unsaid things aransa amma sun kasa furta ma juna ko daya hade da suprise din daya mata ayanzun sai take mugun jin shaukin ta budi baki tagaya masa how much she misses him amma kunya ya hanata aikatawa.. Shikuwa yau kyaun nata ne ya gama rudashi,kwalliyar ya mata bala'in kyau har yake ganin babu mahadin ta acikin dukan matan da yake arba da su.. Karar wayan ta ne ya fargan dasu sai ya sake mata cake din yace suna jiran ki ko?Ta gyada mashi kai tana mumurshi. ..wani card ya zare a aljihun sa mai dauke da street adress ya bata,yana mata kallon shi tafiya zaiyi,Bata ki mashi ba ta karba ta adana sabida ganin sa awannan lokacin it means alot to her.. Wani abu ke yawan gaya mata cewa ita na dabance a duniyar sa Bayan tafiyar sa sai ta koma dakin ta aje cake din ta fito,batare da bata lokaci ba ta haura sama chan inda suka shirya mata suprise partyn da bata sani ba Tana saka kafarta kuwa wani white bubling snow flakes suka poping akanta gaba daya sanda taji ta lume cikin duniyar nishadi da mamaki She looks Alluring datayi fuskan suprise tana tare snow flakes din da hayyaneta,juyawar da zatayi sai taga kowa na tsaye na mata wakar happy birthday ana mata tafi ga cameras ta ko ina suna daukar ta hotuna. Wani rau tayi da ido cikin tsananin farinciki tun kan ta motsa Wasu kananan yara tuni suka zagaye ta da colourful ballons suna flying dinshi sama. tsaban murna da nishadi har bata san wajen waye zata fara zuwa ba Duka duka mutanen dake wajen basu fi ashirin da biyar ba Ga yasmine tazo da bro din ta omer ga dija da mum din ta anan ne ma jahan ta ke sanin ma haifiyar dijan wato alhaja kafayat. Happy bithday my princess.. jahan ta fada tana rungomota jikin ta tana dan encouragin din ta ta maida hawayen farinciki dake neman kufce wa afuskan ta,ga su subaya suma sunyi kyau sosai duk suna maida mata murmushi in a very pleasant manner. In a very special way aka yanka mata 7 step birthday cake tasa ma jahan abaki tasa ma subaya and the next thing she was wishing that khaldun ma yana wajen... "Hakan nan Komai ya tafi dai dai,dan karamin hidima amma anyi shi in a grand and special way.. Abunda kawai ya so ya bata mata mood din ta shine bayan jahan ta bata kyautatauka sadat ne ya biyo baya,sai nacewa yake a musu hoto shi da ita,and she cant just hide the fact that ta tsane shi kamar mutuwar ta.. Sai yana yi ya ma subaya wani irin maganganu marasa kama kai,burin sa bai wuce yasa ta tafara jin wani abu akan bahiyya ba. Awajen subaya Yayi ta yabawa da kwalliyar bahiyya har abun ya bata haushi,duk misalin da xai bata sai ya hada da ita amma bai fito direct yana nuna zumudin sa a idon kowa sai awajen ta slow and tactfylly yake shiga mind dinta yana cakulawa amma kuma bata dago shi After that moment kowa ya watse an tara ma bahiyya gifts dayawa daga wajen friends din jahan ga nasu subaya anan ne sadat ya saka nashi munafukan packages din mai dauke da irin kayan aniversaryn subaya. Ita kuwa bahi tafi damuwa da babban diamond necklace da alhaj hamood ya sa akayi mata sabida nuna murnan sa musamman akan sakamakon jarabawar ta.. She feel so special,ranar yana daya daga ranakun da bazata iya mancewa da su a duniya.. washe gari da safe jahan zata koma nigeria toh bahiyya ne ta raka ta airpot soyayyar datake nuna mata mai sanyi daga nan ma zaka gane cewa bata nadaman jawo ta cikin rayuwar su Subaya kuwa na cahn suite din da suke da sadaat akan in few days time idan suka kammala documtation din bahiyya gaba daya zasu dawo nigeria Tana kwance sadat ya fito daga wanka,abu daya yake bata ciwon kai da auren nasu shine Har yau baiya nuna mata kamar ita mace ce akangadon shi She is sexually starve and depresed amma saidai tana mugun son shi ta kuma yarda da shi sai take biye mashi bata masa korafi abunda ya shafi jikin sa bata da iko sai abunda ya bata.. Yau ma hakan ne,yana jin ta tana neman kulawar sa cikin dare amma sai ya basar,gaba daya ta rasa gane meyake yawan yi da wayar sa da sam ya kasa ajiyewa a kulata bare ya runtsa shima Da safe She woke up angry,amma bai damu ba ya bude bathrum ya shiga wanka.. Dube dube take yi tana so tayi masa bincike amma tsoro yana damun ta sabida bata saba ba Wayar daya rike jiya bashi ya bari akan gadon ba amma tsaban son ta ga meyey aciki yasa bata lura ba sai bata ga komai ba Bata sani ba a hakan Wayoyin shi da dama wanda bata san dashi ba yana dakin dan sosai ya san yadda yake so yayi playing games din sa akanta Bahiyya kuwa tana dawo wa dama da shirin ta,adress din da khal ya bata tabi ta je har inda yake ta same shi Same apartment amma basu zauna ba ya fitar da ita yawon shakatawa.. Babu wanda yasan khaldun ya dawo kuma yana london sai ita da sadaat dake famar bibiyan su a boye. Duk motsin su yana shigowa kunnen sa Har Yanzu ya fara gane cewa soyayya mai karfi ne a tsakanin su kuma hakan yana mugun hassaa mashi kishi aransa Bawai don son zuxiyar sa kawai yasa yake bin bahiya ba,harda jarababben kaunarta dake neman fin karfin kawklan sa He desperetly want to end the game yanzu kam, wannan karon yana so komai ya watse musu.. Daya tabbataa zasu kai dare a dates din nasu sai ya fita shima dan ya juya abun a idanun subaya har ya dawo wani abin zargi Da sukaje diving site Khal ya kashe wayan bahiyyan bata sani ba,subaya tayi ya neman ta gaba daya bata ganta,hakabma ta nemi sadat din shiru Sai Kusan daf magrib zuwa Bayan ishai khal ya dawo da ita,tsaban nishadin data yi aranar sanda gajiya ya nuna sosai akwayar idanun ta,.. Yana tafiya sadat ma ya iso wajen bata ganshi ba ya wuce da sauri ya labe yana kallon ta sanda ta shigo subaya ta fara mata fadan ina taje tun safe dayaga bata iya amsawa basai kl ya sako kai ya shigo agajiye yana wasu kinibin... Looking at both of them take surutun cewa idan zasu fita su dade haka to su gaya mata ko subar wayan su a kunnee Kwata kwata bahi da subaya basu gane me hakan yake nufi ba Amma sadat sosaai yaji dadi aransa da hakan ya faru musamman daya lura cewa bahiyya takan bata rai in tagansa yasan subaya bazata kawo tunanin tsananin shi ya kaawo hakan ba zatayi tunanin ko fadan ne bata so After 1 week hakan ya cigaba da faruwa sabida babu ranar da bahiyya bata sneaking suna fita wajeje da khal a boye suna having good times. Sadat ma baiya gajiya wajen bibiyan su da kuma nuna ma subaya alaman dake dada rikitar da ita akasu. One fateful morning bahi ta fito da kaya A hannun ta zata kai dakin subaya akan cewa anjima jirgin su zai tashi Lokacin Subaya tana wanka,to babu ko tsoro a idanun shi ya tsare ta yake gaya mata cewa ai yasan inda take zuwa kuma sai ya ci ubanta... She dint take it serious duk dama bayan tsanar sa tana dan jin tsoron muguntar sa,dangwala kayan tayi ta fita batace mashi uffan ba A fannin khal kuwa yagama sakawa aranshi cewa da sun dawo nigeria zai gaya ma bahiyyar asalin abunda ke zuciyat sa game da ita Yana so yace mata yana kaunar ta kuma zai aure ta,amma yana so yayi shi ne ta salom da bazata taba mantawa ba Kaamil daya makale mata suna mrs unkown..kullum sai sunyi dogon hira da khal yana tsarasa kalmomin da zaiyi amfani dashi ya tsara ta. Duk da taurin shi He is litle bit nervous about it,amma kuma ya karbi shawaran hada musu dinner dates agidan dan ya fada mata nashi sirrin yana kuma saka ran itama zata amsa mashi.. Daf zasu tafi,sadat ya gama nashi hade haden yana da sim card dayayi saving suna,sakonni, harda hotonan bahiyya. aciki yake tara fake calls da messges masu abun mamaki Ana daff hours din da jirgin su da zai tashi dagangan Ya cire codes din wayar sa ya aje akan gado kamar baisani ba ya shiga wanka Ya riga ya gane cewa subaya tana mugun cikin halin son taga waye yake yawan chat da kira cikin dare Aikuwa yana bada baya ta dauka ta shiga bincikawa Iya duba tayi amma ta kasa barin kwaklata ya yarda mata cewa bahiyyan data sani ne take cin amanan ta Take taji jikin ta ya dau dumi tana zufa tana karkwarwa wani dafe kanta tayi cikin wani zautaccen yanayin bata san sanda kuka mai zafi ya kwace mata Those tex mesges looks so real,yayi amfanida lokaci da kwalkwa ya tsara komai ta inda dik kulawar ka bazaka yi saurin amincewa ba Cikin wannan Mumunan yanayin rudani ya fito daga toilet ya same ta A zuciyansa wanii mugun dariyar ta yake Yasan burinsa yanzu kam na daf da cikawa Bakin cikin bahiyya yake so ya buga zuciyan subaya ta mutu ya sace arziki Itakuwa Tsaban mamakin abunda ta tagani Bata ma san ya shigo ba,da sauri ya kwace wayarsa ya rike dan ta farga ta ga shidin ne a tsaye Da ta dube shi Wani azaban kukan rudani ta fashe da shi tana tambayar sa metake gani? ...duk bori da hauka sanda tayi masa amma baice uffan ba sanda ta gama ta rusuna gabansa tana kukan cewa sun cuce ta kafin ya motsa Cikin salon iya munafurci da yaudara ya fara nashi maganan,duk dama baiyi tsammanin zai sha wahala wajen cusa ma subaya wasu abubuwan ba Dan da kyar ya cusa mata cewar bahiyya ce ta fara neman sa ba