Sashe 42
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
like real American celebritys Kafin kace kobo,junnut ta aje al'adan ta gaba daya ta dawo wankan damammun jeans and trousers,hot lingeries,spectacles,natural gashin kanta kuwa wani bin sai taci rabin season bata ma sanda shi ban Da ita Hilda gaba daya saida suka haukata college din su musamman da yan mata da samari suka sa ido sosai akan su kowa yana son su san dashi. Junnut har application of friendship ake rubuta musu,daga nan sai ta koyo iya maganan banza da saurin kaskantar da dan adam,hilda kam A ce dama. Domin kuwa babu marabar halayen hilda da zarah mj a wani hausa novel na surayyahms da nake karantawa mai suna sakamako. Da first session ya kare junnut da hilda basu je hutu gida ba,wani extra institution na business enterpneship na yayan masu kudi sukayo registan kansu suna zuwa ana damawa da su Jahan khatun dataji hakan kamar zata kashe kanta dan murna. **** Nikuwa da naje hutu sai na yi gamo da rashin saa,ina zuwa saudi arabia kwana biyu kawai big sis tayi tace wai zataje califonia meeting zata dawo in 1week. Nace zan bita,haka taki fir tace ai daga schl na dawo kawai ma huta Haka dai na daure na zauna I have to live with that sadat mu biyu kawai a gidan A rana na farko da ya dawo daga aiki,na fito na gaishe sa zanje dauko abunci yana ta kallo na ban kula shi ba Dana kawo abincin zan ajiye,kawai sai naji ya kama min hannu na ya ruko a nashi har yana kokarin murzawa a tsorace na dago zan fauce Sai naji Yace...bahi?..ban amsa ba nayi kokarin kwacewa Sai ya bini da wani shuumin murmushi,wai ke ya rayuwan ki haka ne? Sai Na share shi Nace here is ur food. .ni na koshi zan juya kenan sai ba ji charaff ya mike ya chapko ni,"ke zo nan ki fada min labarin london"sai ya dangwala ni akan cinyar sa da karfi dukan hannun sa sun matse ni sosai" Wani bugun da kirji na yayi alokacin bansan sanda raina yayi mumunan bacin da sai da hawaye suka ciko min ido na ba Blurting hurtful word na so nayi ko zanji dai dai But Am still respecting him sabida bai taba furta min komai ba,duk dama duk wata mace mai tunani zata gane mummunan nufin sa akaina Sai na fauce jikina a zafafe na tura sa na mike tsaye na bata raina na hade rai bance uffan ba..shima tsayen ya mike Kamar bai san inayi ba,ya kika min shiru ina tanbayar ki,.na kau da kaina gefe tsaki ne ya kufce min,ban hankara ba kawai sai naga mutum ya dada matsowa. Ni kam tsoro da haushi ya gama ma hatsala ni "Wani kuka mai sauti na fashe masa da shi,yace meye akayi miki...wont you tell me?la bari kawai zaki.. Tun bai karasa ba ya shiga mika hannun sa zai shafo fuska ta,turawa nayi na furta Ni dai Bana so!!!cikin tsawa kuma a zafafe naja zuciya ina kuka, sai da ya dan ja yana kallo na cikin mamaki. Magana yake min amma Ban kula ba,Da sauri nabi gefen sa na haura sama bayan na shiga na kulle da key har jam locks KUYI HAKURI KUNGANI LATE KO? TOH SHARRIN SYSTEM NE ALLAH SHIYASAN ABUNDA YASA YAMIN RIKICI YAU I LOST ALL MY TYPINGS,WALLHY IM SO PISSED UP KOMAI YA GOGE INCLUDING MY CHATS WANNAN CHAPTER MA IS INCOMPLETE YA GOGE SHI KUSAN 2 READ MORE YA BACE BA KARSHEN BAKENAN,IM SO DISSAPOINTED JUST MANAGE THIS HALF page KAFIN NA SAN NAYI,GUDNITE AHUMAGGAH _The love triangle_ _A nigerian historical fiction_ *WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_