← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 173

Sashe 3

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rayuwan ka dani?. Kokarin Sake kiran sunan shin zanyi amma ban ko karasa kalmar ba ya rufe min baki na da yatsun sa..cike da sanyin jiki ya jawo ni jikin shi Tsam sai naji ya sake rungume ni.. Wani Ajiyan zuciya na sauke Nima sai na lafe ina mai sauke ajiyayyan numfashi. Wani shiru ne ya ratsa tsakanin mu Tsawon lokaci sannan abbu ya dago ni yana mai kallon fuskata,nima kallon sa na tsaya yi dan daga ka ganshi kasan maganar dana furta ne yayi tasiri a zuciyar sa sosai. But Maybe am too young to understand what love is shiyasa bazan fahimce rashin dauriyar sa akan soyayyar sa da ammuh ba. Anma kuma Ba sai an fada min ba nasan abbu yana nadaman sakani cikin halin da nake ciki yanzu sosai. Sai da ya kure ni da ido Kafin ya numfasa da dai Kamar wani magana zai min sai naga ya sake min hannu na da sauri ya juya dubar sa kan abunda na daura akan murhu.. Ashe namar dana daura a wutar ne ke famar babbakewa nikuwa tsaban shaukin kasancewa tare da abbu na yasa ban ma ji ba,da azaman sa ya sauke namar yana yarfa hannu... Da sauri na matso,ina cewa mugani...tafin hannun shin na riko inda ya kone ina furawa da iskan baki na inai masa sannu cike da so da kulawa.. Ina Cikin haka Kwasam sai naga dison Hawayen shi ya digo akan hannu na daya ke cikin nashi,sai dai bai ma bari na daga ido na kalle shi ba ya goge idanun shi da sauri ya kuma zaunar da ni kan dutsin dake wajen baice uffan ba ya juya abunshi Nidai Ina ta kallon shi Har ya gama tsatsame naman ya aje agabana,sai ya dauki kwara guda Yace yi bisimillahi Inayi kuwa ya kaimin namar bakina. Mahaifi na kkyawar mutum ne sosai duk dama wahala ya tsufar dashi amma kuma farin fata,bakin gashi da manyan dim eyes dinsa su suke yawan sani Lumshe ido a hankali ina kuma sake budewa Cikin sauki Yake sakamin ina taunawa a tsanake. Sai da nakai kusan sau hudu kafin nima na yanka bari guda na kai mashi bakin sa.. Ya na kan ci..sai na kirashi nace "Abbu cikin son na sa shi dariya..sai kuwa ya amsa ni da na'am noor! Sai nace wai Meyasa ka daina kira na da asalin suna na?ko ya dena maka dadi ne.. Faffadan Murmushi kawai yayi yace,ai ko bayan raina ne, nasan kuwa akwai mutane dayawa a doron kasa da zasu kira ki da asalin sunan ki BAHIYYAH ta. Amma kinga ni? Dole na girmama ki da sunayi da yawa.. Dariya mai sanyi kawai nayi ganin murmushin karfin halin da yake min yana kuma maganan cikin raha pretending to be ok bayan nasan ba yajin dadin. Sai ya dafe tsakar kaina with much serious tone kamar wanda zai yimin wata muhimmin addua..Yace bahiyyah kincancaci a kira ki saiiqa..sabida ke alheri ce kuma akan hanyar alheri zaki dawwama har abada. Kece ..noor wato haske,hasken rayuwar iyayen ta...sai yayi murmushi.. Hawayen dake hargowa a idanu na na tare cikin karfin hali nayi murmushi nace ..abbu dayan fa? Baice min komai ba Hannun shi ya sauke kawai yana murmushin sa,sai da ya sake yankar namar zai kai min baki kafi yace Almass?(diamond)kar ki damu dashi. Nidai Kiyi hakuri bahiyya tah,nasan Abbu sam baya kyautawa yar sa. "Ina kan tauna na baki na, sai nace hakuri akan me kuma abbuh na?bai amsa ni ba sai yace min nayi miki Alkwari bazan sake sakaki cikin wani hali ba. Kisani nafi kowa son ki rayu cikin farin ciki ba kunci ba. Tirrr da mahaifin da zai jefa yarsa cikin kunci..dan juya kansa yayi dan da wani irin remorseful feeling ya karashe kalman. ...atake sai naga yanayin sa ya fara sauyawa. Hankali na adan tashe nace abbuh?wai akan me kake furta irin wayannan kalaman,nayi maka wani abu ne? Yace ah,a Bahiyya...ai ko kin min laifi ma na yafe miki har abada,dada riko hanu na yayi yace min Amma bansan ko ke zaki yafe min ba,bar ganin ina cikin zafin ciwo a jiya ina sane dake araina,kina wahala dani sosai naga har firgita kikeyi cikin dare kina kirayen sunana....ina tausaya miki sosai. Kuma Tin A lokacin na fara jin dole na na rayu ko dan farin cikin ki bahiyyah kinyafe min...? "Dan Shiru nayi dan banma san me zance masa ba Cikin farin cikin da bansan dashi ba na gyada kai ina goge idanuna da suka dan sauya kalar su Yauce rana ta farko danaji abbuh ya furta min hakan kai tsaye..,har abbu ne yau ya iya mance jimamin mutuwar ammuh yake cewa zai rayu dani?wani Murna ne ya mamaye kirji na sosai wanda babu misalin shi. ****** Tun daga wannan rana har cikin makon,a gaba dayan ta a haka rayuwa ta sauya mana, duk dama abbu baya fita ko ina amma bai taba kwanciya ciwo ba tun wannan rana. Muna cikin wannan yanayi Wata ranar Alhamis na fito nayi wanka na fes,ganin abbu ya warware yana kwance shiru sai na nemi izinin sa na bar shi a gidan shikadai,ni kuma na Fito cikin garin kallon wasa a chan yankin sarkin fulani domin ziyartar babban kawata wanda ake kira da JUNNUT.. Junnut ma marainiya ce,sai dai ta rasa uwa da uba ne baki daya,ayanzu a hannun yar uwan mahaifin ta wato ummah Surbajo take zama. Mahaifin junnut da sister sa ummah surbajo asalin jinsin zuriar fulanin yankin ne. Don haka junnut asalin bafulata ne maiji da kyau baiwa da kuma buri mai kyau na rayuwa. Kawancen mu da ita ya samu nasaba ne tun daga kan iyayen mu,Don kuwa mahaifiya ta itace babban kawar mahaifiyar junnut Ammuh tace min da ada chan damu ka shigo garin bamu san kowa ba mahaifiyar junnut su ne jinsin fulanina farko da suka bada iyayen nawa mafaka acikin wannan yanki har aka karbe mu.. Iyayen junnut duka sun rasu tun kafin ammuh na ta bar duniya Sam rasuwar sun baiyi mana dadi ba,gashi sun tafi sun bar dukiya mai tarin yawa da shike su masu arzikin dabbobi da kudin hadadan kasuwanci da larabawan egytps da china ne toh bayan mutuwar su sai ya kasance yarsu da suka bari wato junnut bata cikin irin halin maraicin danake ciki. ...gashi a duk tsaunin wajen ummah surbajo ce kawai tayi karatu mai zurfi,tun asali ma ta dalilin ta iyayen mu suka yarda muke zuwa makarantar bature a chan kusa da egypt dama da yankin ethiopia har muka sami ilimin bature nida junnut yanzu munkai matakin ss1.. Wanda a yanzun Mutuwar ammu na da ciwon abbu ya dan dakatar da ni daga halarta kwana biyu banje ba. Ummah surbajo tana matikar kula da junnut dan haka Ko meye junnut take so ana mata shi. Rayuwar ta take yi cike da buri da son kawo mana cigaba... Tun Muna yan Shekaru 4 shakuwar mu ya wuce yadda hankali zai iya dauka,ayanzu duk wani sirrin ta na sani haka itama kuma tasan nawa. tsaban yadda muke da ita wani bin ko ciwon kai nakeyi zaka ga itama ta fara yinshi kuma bata samun sauki har sai na samu Gashi kusan siffar fatar jikin mu da tsarin jikin mu daya, duk wani halayen mu na yaranta ma iri daya ne,banbacin mu shine ita tafi ni iya magana da mutane sabida awani wajen ni shiru shiru ne. GAshi har munkai shekaru sha hudu,Da shike al'adan fulanin su muma muke bi,mutuwar ammu ne ya hana ayi min aure,ita kuma junnut burin ta na rayuwa ya hana ayi mata musamman data samu goyon baya daga antyn ta ummah surbajo. Junnut tana matukar kaunar rayuwa,mace ce maison taga ta yi ilimin bature mai zurfi tayi kudi tana kwalliya tayi kyau,tana tuka motoci. Above all babban burin junnut ne ta ga tayi aure nan gaba kuma ta auri Babban soja ko wani iri ne kuwa bata damu ba. A hanyar mu na kasuwa Yau ma hirar data zo min da shi kenan. Sai dariya muke fuskokin mu dauke da annuri Hannun mu sarkafe da juna. Chan sai Tace min baahi?batare da na dago ba Nace naam "Daga Gobe Buri na zai iya cikawa amma kwata kwata bana jin farin ciki sabida nasan kwanan nan zamu rabu. Nace ko?..wanne daga cikin burin naki ne zai raba mu junnut.. Tayi dariya tace min buri na koyan turanci. Kinsan ko wanda anty surbajo take dan koya mana bazai ishe ni na wanku har na auro soja na ba ko? Murmushi kawai nayi cikin nuna mata rashin fahimta nace To wanne kenan?ai Nima sai inbiki ko? Junnut idan kika tafi kika barni bansan ya zanyi ba.. Dan Kallo na junnut tayi,dan Salon danayi maganan ya sata taji wani iri. jawo ni tayi muka koma gefe muka jingina da bayan mu. Wani Ajiyan zuciya tayi,Tace ashe babu dadi? ...,bahiyyah kinsan me naji kuwa a lokacin da abbu yake ciwo kika daina fitowa muje karatu kwata kwata ma na daina ganin ki? To Walhy ji nayi kamar nikadai ce a duniyan nan.. Ni Gashi ina nan Bansan wani halin kuke ciki ba gashi umma surbajo ta hanani zuwa yankin ku...wai its too far"cikin rigimammen gurgun turancin ta takarashe maganan Duk dama Damuwa ne sosai akan fuskarta. Sai nayi Murmushi nace ai babu komai junnut,nasan bazaki barni cikin wani hali ba,ba gashi abbun ma ya warware ba Dan karamin Nishi junnut ta sauke tace eh,Mungode ma Allah.. Amma kinsan me?nace mata a'ah.. Tace "inada yaqinin cewa bazamu taba rabuwa ba bahiyya, nidake shakuwa ce na har abada na Amana,soyayya na rai da rai..ina matukar kaunar ki kawata. Anan muka juyo duka muna fuskan tar juna cikin shauki mai nuna kaunar gaskiya dake tafe da kalaman zuciyar mu Nidai Bance komai ba don tausayin ta da nake ji,junnut is kind of emotional don ko ni nasan nafita karfin xuciya da jarumta. Cikin sanyin murya tace bahiyyya Na dube ta nace naam junnut Tace dama naji umma surbajo ne tana cewa gobe zasu zo su dauke ni.. Hannun ta na sake garan gatsau Cikin tashin hankali Nace su waye kuma junnut?wai Ina za kije ne? Ita ma shiru tayi ta kure ni da idon don kuwa a Ba zata naji kirji na ya buga. Nan ta
Chapter 3 · 0% Book details