← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 173

Sashe 19

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

infact za'a iya ce ma wajen hall way ne daya ke bi in zai shiga daki.. Anan na baje ina goge tiles din da basuyi kama da sunyi datti ba Allah kadai yasan meya sa yace agoge mashi. Ina cikin aikin sai ga sallama Wani mutum nagani mai kama da delivery man wearing a strip army uniform baiya ko murmushI shima box din dake hannun shi ya mika min ya juya abunshi. Duk dama Nasan kayan sakawan shin ne but I have to open it And check Kamar Dai yadda nanah A tace inayi dan na tabbatar da komai intact. Sai na aje mopper ta agefe Ban lurada ruwa yana tsiyaya A kasa Ba nan na bude box din cikin rawar jiki. Wasu haddadun uniforma naci karo dasu God Knows Its amazing,Hannu nasa akan Materials din Ina shafawa Basai an gaya min tsadaddu bane kyaun su a ido da laushin su ya isa ya sanar min.. Farin rigan uniform kal ce da royal blue army trousers da cap an nade su tsaf kamar ba mutum ne zaisa ba. Sai dai wannnan Karon wayo na ya carke min A hanya bansan ma unifom din na soja bane ko na mai tukan jirgi" ,dan Ban ko iya karanta Ma'anan Abun da aka rubuta akan silver plated insignia da aka manna agaban white shirt din ba (wato milltary badge dinsa) dake gaban rigar ba . Naga dai An rubuta wasu abubuwan a dakile kafin naga wata kalma kamar sunan shi reading BG SA'OOD HAMOOD MC. Nan na Shiga tunani ina nazari,ni dai naji ana ta Ce masa khaldun amma bashi nagani ajikin rigar ba toh what does that mean? Ko dai ba sunan shi bane?To sunan waye kenan? Wasa wasa na tsunduma kaina cikin nazarin da baida amfani ban hankara ba naji an bude kofa daga baya na Ina juyawa kuwa muka hade ido tsaban gaba na yayi rasss sai nayi saurin fizgewa na kame Nasan Shi din ne ya fito yayi tsaye yana jefo min mugayen kallo hannun shi rike da door handle dinsa A sadade na shiga kokarin rufe box din ina kokarin mikewa na kalle shi na mika masa kayan sa,ai kuwa Ina daga kafa ta sai gashi tsantsi ya debo ni nayo zutttt na zame akasa Kayan sun zube duka acikin ruwan bleach din dake kasa wanda ya zubo daga mooper duck din. A take na shiga ganin waje ldishi dishi Duk da zafin buguwan da nayi bai hanani karkarwan tsoro ba Kokarin mikewa naki sai naji na kasa daga kafa Sau dari ina kashe kaina mentally. Yau Na shiga uku na furta ina kokarin jan kafata da karfi dan Na mike nasan bazan iya Ma kallon Idanun shi ba. Im very sorrry sir!!! Dan Allah kayi hakuri... Baki na ne ya shiga furta su involuntarily Baice min uffan ba Hawayen tashin hankali bazata suka wanke min fuska ta ina famar tsamo kayan daga cikin ruwan bleach din dik sun baci sunyi rawaya Bai min tsawa ba but yadda yake kallo na in a disqusiting way nasan tawa ta kare min. Wrist dinsa ya daga ya dubo time a Agogon shi ya ce min I have A Multi billion dollar meeting in 20 minutes. Ki kawo min kayan da zansa na baki minti goma,ko dago kaina banyi ba wuff ya juya ya koma dakin sa ya barni da Jikakken kayan sa a hannu na. Follow #SURAYYAHMS COMMENT and SHARE WITH OTHERS AHUMAGGAH _A nigerian historical fiction_ *WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
Chapter 19 · 0% Book details