Sashe 83
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._ _Bismillahirrahmanirrahim!_ _*For you sis Ayusher moh'd.*_ -evolution Wani shakurarren kuka mai kakarin rudewa ta fashe dashi duk jikin ta sai da ya dauki rawa.. Dafe kirjin ta tayi cikin numfasawa tana furta innalihhi wa inna ilaihi rajiun Tsaban bugu catake zuciyan ta zai fito daga kirjin ta,ji tayi kwalwwlkta na ce mata komai ma mafarki ne. Dan Har yanzu Ta kasa yarda da cewa abu daya suke so ita da junnut din ta,"dama ashe har sa'ood yana son wata?...to what about me?i truly loved himm hala shiyasa yake wasa da hankali na, bai ma taba jin nayi masa ba,..but why junnut...why my besfriend, meyasa zuciyata ta zata so abunda kike so kuma yake sonki. Dan pause tayi tana jan numfashi idanun ta gaba daya sunyi jazir..yace ya aure ni,amma yaki yace ni matar sace?..,bisa ga abubuwan da junnut tace mata ayau..ba tantama ta kawo cewa maybe suna matukar son juna...maybe he dosnt even want hurt junnut for my sake.. Kuka kawai takeyi tana birgima akan floor cikin tsananin tausayin kanta Tayi ta maganganu daban daban amma bakin ta ya kasa furta mata mafita guda daya akan lamarin What is even upseting her more bai wuce wani azaban wutar kishin sa datake ji ba...abun ya mata yawa har taba mamakin kanta Ji takeyi kamar bazata taba iya hakura da son shi ba Dan ance junnut zai aura,bai fi damun ta kamar yadda junnut din take bada labarin sa ba Ayanzu Wani Haushin sa takeji kuma tasan son shi da mummun kishin san suke tada mata haka Takune kanta tayi akasa a tsakar dakin cikin kunci ta ta kife kanta da gwiwa feeling so lost and confused Tunani takeyi ko zata iya rayuwar ta acikin su a haka? Beside bata san me yasa ya aure tan ba Wasu hawayen ke sauko mata,sad and trembling voice dinta yake cewa In har junnut ce ka zaba tuntuni why did u marry me?wai ko ce masa akayi ne ina sonshi yake neman wulkantani?... To wazai fada masa sirri na?...is that why he call me cheap...in zata iya tunawa babu wanda yasani daga sadat dai sai su jasmine su kadai suka san yadda take kaunar khaldun Tace gaskiya bazan iya hada miji da junnut ba,tunda yace ai ba so na yake ba why not ni ka sake ni na koma gida nayi rayuwa ta?..But can she? a take wani zuciyar yace mata meyasa bakiyi tunanin haka tuntuni ba sanda kikaji maganan kishiya,kin amince kin zama matar sa duk da abunda yake gaya maki,to kenan zaki sadaukar da mijin ki sabida yayi alkawari da wata? Dan Shiru tayi tana duba da lamarin can ta jingina kanta da bango slowly ta runtse idanun ta.. Tasan dai har yanzu khaldun shine abu mafi soyuwa aranta wanda take ganin kamar rabuwa dashi abu ne wanda zai iya mugun azabtar da ita. Sannan A Duniya tasan junnut ta fi karfin komai awajen ta,not even a guy that is mistreating her feeling,bisa ga maganganun junnut na dazu a yanzu kam ta amince khal ba ta ita yake ba,to ita ma me zatayi da shi? Gani take kamar itace matsalan yanzu data kwallafa shi aranta Tace Ko ma ta fada ma junnut komai ne dan suyi shawaran yadda zata rabu mata dashi kowa ya huta?. Ayanzu gaskiyar ta shine Tasan bazata iya hada kishi da junnut din ta ba kuma tasan bazata taba iya daurewa akan soyayyar shi ba... What a strange world..tayi ta juya tunani,ta bada kwalwalta dalilai amma har yanzu dai bata gane komai ba Takance dama ace banyi aure shi ba da sai ince zan yanke wani hukuncin na daban Shiru dai tayi tana maganan zuci,a hankali tana sauke ajiyan zuciya...Ganin kamar numfashin ta na neman daukewa sai tayi saurin sulalewa ta mike kafafun ta akan floor din tayi tsam da idanun ta na aikin zubar da rudaddun kwallla A duk tunanin datayi sai take Jin kwakwaltar kamar shirme yake mata She is in extreme shock and pain,bata ma san lokacin da wani hutaccen bacci yayi awon gaba da ita ba. Bangaren khal kuwa haka kawai ransa ya bashi cewa duk inda bahi take ayanzu tana cikin rudani dan yasan bazata ji dadin abun ba Shikam yasan yana son ta,kuma Duk da abubuwan da yake faruwa har yanzu bai cire rai ba Yasan xai iya yuwa itama tana son shi,sanin hakan ne yafi tasiri aransa fiye da duk wani laifin datayi masa . kuma Yana da yaqinin da wata na dabance ba junnut ba da abun zai zo mata da sauki,but her best friend?. yasan is not gonna be easy for her to asimilite...toh a duk da yana tuno hakan amma yake tursasa zuciyan sa jin dadin da hakan ya faru da ita Gani yake wannan al'amarin shi zai rama ma kanwar shi azaban da ta dandana mata akan sadat somehow Dama shi da kaamil ne awajen to da junnut ta iso sai ya share su ya tsunduma kanshi gaba daya cikin tunanin bahiiyar sa baiya ma sauraran hirar su Kaaamil is so intrested in her,dan tun daya ganta zuciyar sa take faman harbawa Koda junnut tazo wajen ma hirar bahi kawai sukeyi Khal Jin tace ma kaamil ai hira sukeyi bahin tayi excusing dinta ta tafi tuni sai yaji zuciyar sa ta amsa Ba bata lokaci ya xame ya wuce bai tsaya ko ina ba sai site din sa sauri yake kamar wanda ake tunzira shi,bude kofar dakin ta yayi da sauri daga idanun shi ke dawuya ya hango ta dunkule akasa tayi laushi har abun tausayi hawaye sun gama bushewan su akan kuncin ta Dan karamin ajiyan zuciya ya sauke Ya dafe kansa...."Mixed feelings na damuwar ganin ta Ahakan da wanda yake so ya ji na dadi daya ganta hakan duk su suka dama zuciyan shi..." Kallon yanayin ta ya tsaya yi almost 20minut bai daga idon shi ba,dan kuwa ba sai angaya mashi meyafaru da ita ba jikin shi sosai ya bashi halin datake ciki Sai yace Duk dama amanar wata take shirin ci now she is jelous dan ance ina tare da kawar ta ..what is wrong with dis girl,ya dada kare mata kallo...xuciya nawa take da shi?Allah ya tsine ma zuciyar da zai so ni ya so wani wawa kamar sadat Daure fuskn sa ya dadayi Har wani kikkifta ido yake yana Kallon ta Shi sam bai fahimce ta Farkawan ta ke da wuya suka hade ido dashi amma bata tashi akan floor din ba ta lafe Wani kallo suka maida ma juna yana binta da wasu zafafan harara fuskan sa a daure Itama Hade rai tayi cikin jin kishin sa tana mutsuka ido tana dan turo baki a shagwabe sosai taji dadin ganinshi akanta.... "..Yace Whats all this?...baki da hankali ne zaki kwanta ma mutane akasa...will u get up before i crush you.. Wani share sa tayi,tana dan kau da kai maganganun da suke wanzuwa azuciyar ta su suka fi dauke mata hankali har ya tashi ya fita waje bata ma sani ba yana dawowa kuwa wani shahhhh taji ana gwaro mata ruwan sanyi tun daga kan tsakar kanta har cikin jikin ta A mugun fusace ta mike tana huci ruwan na bin fuskanta mikewa tsaye tayi zumbut har ta hayyako zatayi magana ya wani daka mata tsawa yace... "...Ina wasa dake ne da zanyi maki magana ki zauna ki namin shiru,ni sa'ar ki ne? Wani kuka ta fashe masa dashi Tace ina ruwan ka dani? Shiru yayi ya kure ta da ido tana famar komar da kukan amma Wasu sabbin hawaye ne suke sauko mata dan Tsaban fushi bata san sanda tace masa hakan ba.. Yace ohhhh,to doka ne ba a kwanciya min akan floor dina Duk randa kika sake kwanciyar sai na karya kafarki Ciikin kakarin kukan Tace ai ba dakin kaba ne sai ka fita.. Bai kulata ba yace ni dai na fada maki,kar na sake ganin ki a kasan flooor dina Unless u want me to trow out. " wani harara ta jefa mashi A dan fusace ta dago cryn balls din ta cikin sanyin murya mai nuna firgici tace mashi throw me out now...ni wallhy nagaji..i just want to go home Ai ni bance ina son zama da kai ba Shiru yayi cikin hade rai yanajin ta sanda ta gama maganganun nata kafin ya matso kusa yasa hannu ya jawo ta Har gabansa kamar wanda yake shirin cakumo ta... "U aint going anywhere,gidan nan shine prison dinki.. Zaki ta zama dani har sai na auri kawar ki,she is the only one i want... ..ke Baki da amfanin komai,and dont you dare say ure my wife to her dan nikam nafi karfin ki Ko kallon shi batayi ba,A duk abunda yace "sai na aure kawar kin shiyafi mata zafi"hannun ta take shirin kwacewa ya ki ya sakar mata,..wani Cizo ta danna masa a hannun A mugun fusace ta shiga firgici zata kwace jikin ta daga nashi,shikuwa bai sake tan ba sanda ya gama karance duk wani hawayen dake sauka akan fuskan ta yasan wannan duk borin kishin sa ne...dan yau ne ranar daya fara jin tana maida masa magana cikin fushi da firgici Shikansa ayanzu ta gama ruda masa tunani,dan kuwa balain son shi da kishin sa yake hangowa a yanayin ta just like shikadai ne a zuciyan ta babu wani Cikin ranshi sai yace wai kam Ba sadat take so ba?meyasa take fushi dan ni nace zan aure kawarta,wato ashe ba dadi take iya ma wasu? Wani murmushin mugun ta yayi aransa yace ai Allah ne ya kama ki"da zan iya gaya maki laifin ki amma duk abunda zai faru dake shine dai dai ke..very stupid girl sai ya sake ta ya futa abunsa. Itakam Kuka ta cigaba dayi,daga nan tunda ta wanke fuskanta sai bata sake lekowa tsakar gidan ba Har sanda tayi kwana biyu masu kyau a dakin ta bata kuma kira kowa ba. Dama in bawai ta fito bane babu mai shigowa site dinsa dan haka bata sha mamakin da taga ko junnut bata leko ta ba Wani bin in ta zauna har mamakin kanta take yi sosai,a duk sanda taji zimman cewa zata yanke hukuncin gaya ma junnut komai toh wani azaban fargaban