Sashe 9
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daga gani yasha tsere dan haki yake yi irin na gajiyyau Kafin ma ya bide baki yamin magana sai na ji maganganun wasu mutane,a iya turancin dana iya wajen anty hanne yasa na gane cewa kashe shi suke neman yi shiyasa suka biyo sa nan Sai na yi sauri nima na dauke numfashi na,na ruufe shi da ciyawan wajen nikuma nayi gefe da shi ina lekowa haka na jira har saida mutanen suka bar wajen. Nan na shiga duba mutumin nan har nagane cewa.An harbe shi a gefen kafada ne Ne toh jini na zuba sosai sai kawai na yage dankwali na na daure wajen.. He looks very healthy and rich kaya masu shegen yau da tsada ne ajikin sa sai naga kuma ya tsufa sosai akalla zai kai shekaru saba'in ko tamanin a duniya. NAsan bazan iya daukar sa ko motsa shi ba,dan haka na shiga jejin wajen na shiga nemo mana hanyen mafita.. Karshe dai akan bola na tsaya na taho da sauran tsimammen giyar da aka sha ala watsar da broken botles da aka jefar kan wata open dump daukowa na yi na zauna na goge na kimtsa,da shi nayi jinyar sa duk dama yaban wahala sosai, mutumin nan yayi dauriya iya dauriya sa shure shure da komai har Allah ya bani sa'ar cire masa harsashin bindigar agafen kafadar sa.. Babu magani mai kyau ko wani mafita dan haka sai mutumin nan ya sume min Daga nan Mutumin nan bai farfado ba har sai da gari ya waye ni kuma ban yi bacci ba don tsoro haka na tsaya gadin sa. Da ya dago lunsamshun idanunsa ya kalle ni sai yace meye sunana nikuma nace mashi suna na bahiyyah. Yace min ya gode sosai da na ceto rayuwar sa amma nataimake Shi mubar nan wajen dan yasan za'a sake dawowa neman sa. Banyi musu ba na tallafa masa da kyar dan kuwa bantaba ganin dauriya da gwarjini irin nashi ba. Haka muka dafa juna muka shiga wani waje chan bayan garin inda babu mutane sai go naki da shukoki. Sai dai na lura raunukan jikin sa ya takura masa sosai kuma yana shan wahala. Muna kaiwa wani waje naga ya sake ni ya dan kwanta,yana dan dauke numfashi. Tausayinsa duk sai ya kamani dan Ji nayi kamar wani mutuwar zan sake gani agaba na, dan haka na shiga hade haden ganyen kusa dana nesa mai amfani da marar amfani har naci sa'a na gogga ma mutumin nan ya dan ji dama dama ya farfado. Sai Yace min na fita bakin hanya na nemo masa aron waya zai kira azo adauke sa Cikin mamakin ta ina zan fara nema Nace eh? Bai kula ba Yace kije kiyi sauri..kinji yata..? "Yanayin da yayi maganan yasa ni na mike tsaye Bansan meyasa ba sai naga kawai naje bakin hanya..da shike wajen baya ne sosai babu kowa Nikaina Na kai wajen minti 10 kafin naga wani saurayi akan machine roba yazo wucewa. I know i have to be smart sai na sa masa hannu na tsare shi a nitse. Cike da wayo da iya magana nace mashi dan Allah ya taimaka min nace dani da mahaifina ne muka zo wucewa sai mukayi hatsari kuma wanda ya buge shi ya gudu gashi babu wayar da zan kira gida. Naga fargaba a idanun saurayin amma dashike I look very cool and innocent gashi ina da kyau mai jan hankali, a haka har ya biyo ni na nuna mashi mutumin a matsayin mahaifi na .. Saurayin ya jimanta har da cewa zai taimaka mana amma mutumin sam yaki,shidai kawai yafi damuwa da yayi kirar da wayar sa. Bayan ya gama kirar sai Yace masa ya tafi babu damuwa za'a zo adauke mu. Nima Godiya na masa kamar da gaske Shikuwa haka yaki tafiya shima sai ya zauna damu har kusan mintuna ashirin duk ya dauka ko mahaifina na gaskiya ne dan kuwa sosai mu kayi pretendingn hakan "chan bada dadewa ba sai naga wasu kerarrun motoci har guda biyu manya manyan jeep daya an rubuta GMC YUKON daya kuma TOYOTA RAV4. A rayuwata inba a tv na ni bantaba ganin irin su ba.. Motocin Suna gama parking agaban mu Sai naga Wata kyakywar hmsahkiyar mace ta fito da sauri tayo kan sa Salati ta fara yi sannan ta rusuna gabansa Tana jajantawa,shima da kyar yake mayar mata magana, Ashe ma wani secret meeting ya fito da shugaban sojojin nigeria shine saii yan ta adda suka biyo sa sai naga sauran sojojin da suka fito daga toyotar sun tsaya sunyi jungum jungum anan dan dole aka sallame Saurayin nan aka karbe sunan shi da lambar sa,har soja guda daya ya raka shi har inda zaije Mukuma a cikin motar matan nan aka tafi damu. Nidai sun bani mamaki sosai Don A tunani na asibiti zamuje sai naga kuma an dau wani hanya Anbi damu wata sabon anguwa Cikin wani boyayyen gida mai azabban kyau muka sauka Sunan matar nan begham sahiba. Tana da taushin hali ga yawan murmushi.tunda mutumin ya bata labari na take ta min murmushi da saukin hali Anan naci abinci mai mugun dadi, nayi wanka na kwanta akan gado mai laushi Har sai washe gari Kafin matar take tambaya na labarin meya faru,ban damu ba nayi mata bayani. Kamar yadda shima mutumin ya gaya mata anan tace min nayi kokari sosai dan kuwa bansan waye na taimaka a jiyan ba. Tace nayi hakuri nadan zauna anan dan Babban hatsari ne su kyale ni na fita bare shikuma mai jinyar. Dan haka ne tace ba zamu je asibiti ba sai an tabbatar da safetyn mu anga komai is set ba mai kuma bibiyar mu Nikam bance komai ba nasan ko ansake ni ma bansan ina zan dosa ba,but Ni kaina Na fahimce cewa wannan din wani babban mutum ne,dan kuwa tsaro mai karfin bala'i aka saka acikin gidan Da muke Wanda ya kasance daga ni sai shi sai wannan hamshakiyar mata. Duk da ana bashi kulawa amma nima ina bada taimako na dai dai gwargwado Wasa wasa har Sati biyu mai kyau mu kayi anan kafin har Allah yasa mutumin yawarke ya tashi akan kafar san. Nan yasa aka kawo ni,muka gaisa sai yake tambaya ta tarihi na da inda za'a same iyaye na da gidan mu. A wajen sa is a matter of my security shiyasa suka ajiye ni nikuwa ban boye mishi komai ba na fadi masa komai daga inda na fito. Mutumin Yaji tausayi na sosai,sai ya aika aka kira begham sahiba. Banji dai yace mata uffan daga abunda na fada mashi ba dai, sai ya danka mata ni amana A hannun ta,yace mata gani nan sai ta kula dani,na lura cewa Mutanen suna da kirki sosai dan har hakuri sukayi ta bani Toh Tun Daga nan sai bansake ganin sa ba. Da safiyar ranar aka saka shi awasu motocin kirarar bakaken Mecerdes maybech wanda kamannin su iri daya ne har bazaka gane wanne yake ciki ba. Bansan ina za akaishi ba kuma ban tambaya ba. Nima Chan cikin dare bayan nayi isha'i na dan kwanta sai ga begahm sahiba,.. Kallo na tayi,sai na mike na zauna ina mai gaishe ta Batare da wani dogon bayani ba tace min na biyo ta mu tafi Sum sum na bita muka fita har waje, wata bakar jeep kirar nissan aka bude min tasha tinted babu tunanin zaka iya gane komawa ne daga ciki tare da begahm a seat din baya nayi zugum ana jan mu. Tsawon awowi uku muna tafiya har bacci ya kwashe ni,sanda na bude ido na na ganni a wani gari wanda bansan inane ba. Cikin wata katafaren gate aka bude aka shigar damu A duk da bacci da gajiyan dake idanu na bai hanani kalle kalle ba dan kuwa rudewa ne kawai banyi ba. Begham tace min sauko bahiyya ai mun iso ko. Baki na dana wangale ina kallo na rufe Nace toh na sauko cikin ladabi da sanyin jiki na iso gare ta Dan tafiya kadan mukayi zuwa wani shashi, A hannun wata mata sanye da kayan aiki ta damka ni sai aka kaini wani waje Aka bude min wata daki na shiga nikadai. Juye juye nake yi ina tunani iri iri Anan Har bacci ya dauke ni ban sake ganin begahm ba! #followSurayyahms SHARE AND SHARE UR VIEWS #SURAYYAHMS [9/29, 2:42 PM] 0mer Farouk: _* AHUMAGGAH _A nigerian historical fiction_ *_WATTPAD SURAYYAHMS_* _Brilliant writers association_