← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 173

Sashe 90

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toh ire iren wayannan kalaman ta cika mata a brain Hjy indirah Sai da ta lura bahin ta gamsu da lafuzan nata Kafin ta zaunar da ita Tace ki kalle ni.. karkice zaki najin kunya ta...ki fada min duka matsalolin ki Ke ta daban ce. .kinga wanda take matsayin mahaifiyar mijin ki itace a matsayin mahaifiyar ki ...kinsan kuwa ko babu komai zat na jin nauyin ki ko? ..ba komai Aarah xata iya daura ki akai ba sabida itama mace ce mai kunya da kawaici.. Hakan kuma zai iya cutar da rayuwar auren ki...u see this family?ba kananan mutane bane so Ki dauka ba aure kawai ba har da yaki kika zoyi,u have get up and b a woman not a girl kinji?..already nasan sun gaya maki kina da ajiyayyar kishiya ko? Bahi tayi shiru tana san sauke asitaccun ajiyan zuciya Tace hmmm ai nasani, She is the girl i slaped.. Kuma na fada ma Aarah jiya cewa yarinyar sam bata da da'a..dan haka har yau kece tamu.. Ni kuma nice sabuwar mahifiyar ki,if Aarah is ur big mum then am ur small mumy..can i call me dat? Bahi ta gyafa kai tace yess smal mum Hjy tayi murmushi Babu batun jin kunya ta,ki fadi min duk abunda ya shige maki duhu,ni zan zauna tare dake har na tsawon wata guda so ki nitsu ki bada hadin kai domin kiyi abunda ya dace ..kinji ni ko? Cikin sanyin murya da nitsuwa tace naji small mum.. Hjy ta sake yin murmushi...tasa mata albarka..suka rabu bahiyya tayi zaman ta a dakin tana jirwayen maganganun hajiya azuciyar ta. Ita sam bata fara ma tunanin kasancewar zaman wannan auren ba,but right now sai taji karfin gwiwa da kuma nauyin fuskntar abunda ke gaban ta kamar yadda small mum din nata ta fada.. Aunt Murja bata cika shiga damuwar bahi ba itama tana da jan aji kusan irin na khaldun saood maganar ma wuya yake mata most times amma sam bata da wulakanci dan tasan ta dan girme bahi sosai,so thy keep a very respectful relationship kowa na bada kowa girman sa...jifa jifa takan ja bahin ajiki tana dada wayar mata da kai sosai dan bahi ta nuna maitar ta akan irin tsarin dresing dinsu musamman irin na hausawa. So kwana biyu idan tazo aunt murja tana nuna mata styles kala kala a instgram da yadda zata yi wankan materials ,leshuna da atampopi daidai da zamani.. Yau zuwar hjy indira ya cika sati guda agidn,to Sabida presnce din ta yasa junnut takanyi kwana biyu basu hada ido da bahi ba. Dan a koyaushe hajya tagamu dasu awajen dilshad takan tsige su da masifa daga sama har kasa bat sararawa har hildan dake kuri ma bata bar ta ba...dan sosai ta karbi mari itama a hannun hjyn Gashi duk abunda aka mata akan bahi take lakawa Sai take ce ma junnut,ai dama ta gaya mata duk wani abu da zai fito ta shasen bahiyya ba alheri bane.. Badan ma taga jahan khatun bata zauna akan abunda hjy indirahn take musu ba hilda tuni da tayi zuciya ta bar musu gidan da kuwa haushin su take ji Abubuwa dayawa na damun junnut game da su bahiyyar Amma bata cewa komai sabida tana kaunar kawanta har ila yau,Yanzu haka basu wani zama agidan ita da hilda yawo sosai suka bude wani bin ma sai kaji tamkar basu nan Kaaamil shima ya dawo amma hankalin sa duk yafi zamewa akan bahiyya fiye da komai Toh Xagowar ranar wata jumua,lokacin smal mum tagama shirye shiryen magunguna da wanka da gyaran jiki da suke tana dawa ma bahiyyar. She is very much aware that khal bai samu bada lokaci ma matar nasa ba.. Dan haka suka kashe kudi masu yawa sukayi yi masifan tanadi ma jikin amaryan nasu ta duk hanyar daya dace Wanda ayau din suka fara aiwatar wa a boye.. "Tsumi da kayan gyaran jiki masu tasiri shi su ake sata agaba tana using kadan kadan ba dayawa ba.. Wasu tana sha wasu tana wanka da su,wani ma haka zasu bata tana tsosewa har sai ya kare...most time idan zatayi tsuguno hjy indirah takan tsaya sosai akanta tun bata so har ta fara sabawa.. Wani bin zata ji jikin ta adadaure sometimes,zufan tafin hannu da kafan shike damun ta dan tunda ta fara anfani da magungunar dana wankar sai duk wasu kofofin niimar dake jikin ta suka shiga buduwa dakan su Toh Daga sun hadu da su kaaamil sai kaji yana ta yaba qamshin haddaiyar deer/ember musk din daya riga ya kama fatar jikin ta har yana neman Ya zame mata jiki Gashi ko zama tayi kusa da ita zaka iya banbance qanshin suman kanta dana jikin ta kuma kowanni babu na yarwa aciki Hade da karawar koyarwan kwalliya irin na aunt murja,to idan bahi ta fito hilda bata iya danne kishin ta akanta ta rinka jan tsaki kenan tana kushe ta Shikuwa kaamil tuni yaji kawai bazai iya daurewa,ayanzu idan bahi na kusa dashi har wani imagining ya aure ta yake yi...gani yake tunda bai taba jin so na gaskiya aransa game da kowace mace kamar yadda yake jin na bahi ba tabbas bazai dauki lokaci ba zai bayyana mata sirrin zuciyar shi.. Hakan yasa yayi tattaki ya same junnut suka tattauna akan maganan ..she dint object tunda dama ta gano shi Amma tunanin yadda jahan khatun take nuna bata son bahi yasa junnut ta dan nuna masa fargaban ta A duk abunda ke faruwa agidan,she still respect and cherish her bahi.. Ko kadan bata son taga bahi acikin wani matsala Akomai ma Ita bata ganin aibun kawarta,game da hilda kuwa ta bari kawai cewa tsanar datake nuna ma bahin kishi ne kawai irin na kawance da banbancin dabia.. Kaaamil yace shidai kwanan nan zai gaya ma bahi yana son ta...sannan yana so ne ya nemi auren ta alokaci guda basai an bata lokaci ba Junnut tace in gaya mata kana ciki kenan? Yace ah a..akwai abunda nake planning insha Allah ni da kaina zan gaya mata komai.. She wish him luck suka aje magana ahaka.. Bangaren bahiyya abubuwa sun fara dauke mata hankali, gashi dija ta dada bata goyon baya akan abunda small mum ke daurata akai,yau ma bata bar shashen da wuri ba sai chan yanma suka fito ita da aunty... kaaamil shima yazo har ya koma yau ma sunyi hira sosai . Wani pitch sheraton suka sakaya ajikin su ita da auntin dan iri daya tasa aka musu dinki for the first time simple fitted gown wanda ba atula masa kwalliya ba. Tafiya suke yi small mum ta sa a raka bahi zata koma site din ta,suna dan hira da aunt murja a bazata sai suka jiyo sallamar mutum,wani irin kallon daya bita da shi sai da taji gaban ta ya yi dukan tara tara itama sai tayi tsam Tana kallon yadda yake sake wasu shegun asitarcun murmishi wanda bata san da iya yake yi koda ant murjan ba anty murja da sauri ta sake jiki ita kam ta isa gaban shi...cikin yanayi mai nuna tsananin kewa ta fada jikin shib ta rungume shi tana mai lunshe idanun ta tana dan jinjinawa ajikin sa sosai.. He looks hppu to see her,amma yanayin sa baiya saurin nunawa Sai ya dan tallafo ta da hannun shi baice komai ba yan kallon ta, After like 3 minute ya maida mata murmushin sa mai sanyi da tsada Yace Tare da ke aka zo shine bazaki fada min ba? Cikin silent dariyar tsokana ta kalle idanun shi tana murkuda baki Tace laaaah Aaban...ashe haka ka girma...? Wani harara ya jefa mata ya zare jikin shi ya juya zai bar wajen ..dariya ta fashe dashi ta riko arm dinshi,cike da tsokana tace thats like you,yanzu na san dakai nake tare...i misss u .. Aaban ko nema na bakayi ba,atake ta shagwbe masa... bahi kam kanta ta mayar kasa tana dan satar kallon su duka. Bata san haka ant murja ta saba da khal ba...thy r age mates sunyi tashin saa dan haka bata sha mamakin sabon su ba Baiyi murmishin ba Ya juyo kamar zai ja chics din ta ya amsa, amma dayaga bahin na kallon sa tuni ya hade rai ya basar da komai Sai yace ina hjy ummah?bari naje i wll get back to u Adaidai zai wuce ta yawani shakko azaban qamshi dake fita ajikin ta,bai shirya ba ua kalle ta,tayi saurin dauke kai ta furta barka da dawowa....he looked at her kamar abunda zuciyar shi yake jira kenan,wato yaji sautin muryan ta... He feel reliv atlast Kayan data sa ma ya burge sa amma baya jin yana da time din ta, sakai yayi kamar baiji metace ba dan daya bar gidan cikin kwanakin baya ma iya bacci batare da tazo masa a dream ba Gaba daya ta dama ma kwakwalshi seti har bai san taya zai bullo ma al'amarin ba. Nan itama suka wuce da anty murja,tana dan tsokanar ta cikin bata hakuri akan cewa ta rungume mata mijin ta agaban ta,take cewa ai shekaran ta bakwai kenan rabon ta da ganin sa shiyasa... Shikuwa khal ba bata lokaci ya nufi wajen hjy indira ya rusuna,..a duk dama tana da zafin fada ma yara amma shikam tana sakalta shi dayawa Zuwar sa ya daura kansa akan kafafun ta tana shafa kanshi tana tofa masa aduoi... Tasa shi aranta sosai,wani bin takance dashi dan baiwa...Tace nayi kewar ka dana..dan sarki jikan sarki...in a calming manner take shafa kanshi kamar dan jariri .....ya riko Yatsun hannun ta yana dan wasa dasu cikin sauke ajiyan zuciya yana cewa bazaki ce min zaki tafi gobe ba ko? Jiya mum take ce min ashe kinzo gidan nan,i really miss u...zaki min madaran naki na sha har sai na dena jin kishin ko...tayi murmushi tace yanzun nan ma dan bazakayi bacci ba sai kasha madaran ummah... A hankali sai Ta dago kanshi da murmushi akan fuskanta tana masa kallon so kamar wacce zata hadiye shi,kamar wani karamin yaro tsaban nuna kulawar ta babu abunda bata tambaye shi gne da rayuwar shi ba,sai tayi shiru tanajin yana amsawa ba. Da suka rabu kuwa Har site din shi ta kawo masa skimmed milk ta bashi yasha ta gyara masa lallausan duvet tace mashi kayi bacii
Chapter 90 · 0% Book details