Sashe 109
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._ _bismillahirrahmanirahim._ *For my durling Ahumaggaress siyamah ibrahim* *And all members zauren littafan hausa da* *Taskar billy galadanci* -frail heart Forgive my typing errors i wll sort it out a next page. tare da sauke ajiyan zuciya Hannun shi duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa Yana tsaye yana bin closed doors din da kallo kamar marar aikin yi. "..Minti uku masu kyau ya dauka bai motsa ba..,shikansa yasan Daurewa yayi ya bar wajen dan kuwa yasan shiyafi bukatar ganin ta ayanzu fiye da kowa,ita kuwa bahiyya daga shigar ta dakin ta doka sallama.. 'Sallamu alaikum" sai Ta tsaya daga baki baki bata shigo ba Tayi sau uku ba ansa ba,Da har zata juya ta fita sai tajiyo muryan sa daga dayan part din "2 minute pls" Ta dan tabe baki fuska ba yabo ba fallasa ta dawo ta nemi waje ta zauna cike da nitsuwa take jiranshi Bai fito sarari ba amma ko ina adakin ya dau qamshin wanderlust wato iren turaren mazan nan masu karfi da dadin qamshi. Babu tantama tagane yana daga closet ne, after like 3minutes ta dan motsa.... Jikin ta ne kawai ya bata ya shigo tana juyi kuwa taganshi jingine da wall scounce idanun shi tsam akanta kamar yaune ranar daya soma ganin ta arayuwar sa,ya fito rass dashi kamar babu abinda ke damun shi,Golden Versace shirt da bakin wando ne sanye ajikin shi. .. mikewa tayi tsaye batare da tace mashi uffan ba,soft and girlish drape skirt da pink top din ta ya dada kara fallasa tsarin kyaun jikin ta tasan shi ya dauke mashi hankali,.. Tunani take ko ta fice ne ma kawai ta bar mashi dakin Sai taga da sauri kaamil din ya dauke idanun shi yana mai gyara zaman haddaden golden clive cristain watch Dinsa cikin salon basarwa da nuna alaman baiji komai aranshin ba. "ganin tayi shiru ta nitsu kamar marainiya yasa shi ya karaso inda take..,jin saukar iska a fuskan ta yasa ya ta farga suka hade ido bata dena kallon shi ba...he looks cool amma fadawar da yayi a kwana biyun ya nuna a jikin sa da idanun sa sosai ...murmushi mai sanyi yayi,cikin muryansa mai dadinji yace cupcake.. Batayi kasa agwiwa ba tace Ya jikin? Bai amsa ba ...adan rude ta sauke kanta bayan ta furta hakan Wajen Yayi shiru sanda ya nemi waje ya xauna cike da neman tsokanan ta cikin saukakkeen sautin murya yace twinkle ta cupcake kenan, sai yanzu zaki zo gaishe ni?..ok..sai ya tabe bakin shi..,ba damuwa ni nayi fushi ma. Wani kallon kasan ido tayi mishi..cikin rashin sanin me zatace masa .....ta turo masa Baki a hankli ta furta kayi fushi?to ai shikenan,nima bana yi....Ba cewa ma mum karya ake maka bakace kana so ba?...meyasa kayi karyan toh...nima karya kake min ko? ..yar tsirirayar dariya ce ta kufce masa.. shagwabben sigar fitinar nata yake duba dan ya lura kamar she is serious about what she is saying .... wani bata ranta take neman tayi ta masa surutu ..yace hey babe..sit down zan fada maki gaskiyar toh.. Ta basar shi "Nifa bazan zauna ba,kawai dama nazo ne ince dakai ya jiki...im going Allah ya kara sauki... A bazata ta wani hade rai cikin fushi zata fice,jitayi an riko hannun ta dam dam an dawo da ita"look ni bana son fitina...ya dawo da ita normal position din ta,claiming sturbon ta kau da kanta gefe,..she is intensed,kuma sosai take jin wani bangaren xuciyan ta ya amince da hankali da nagartan kaamil Ayanzu ma shawarar sa take nema amma bata san ta ina xata fara ba Ayayin da take kau da kai..cikowar hawayen ta da suke neman subuce mata ya gani muryan sa na dan shaking yace twinkle cupcake dina wai me haka ne?...me yayi zafi "..Ta share sa ta dada bata ranta kamar bashin maganar take binshi na asali ...Kinsan dalilin dayasa nace musu hakan ne? ..im not lying to u bahiyya,Ba karya nayi ba. kawai bana son kowa yasan nace ina sonki ne Sabida wallhy na hakura dake har Abada.. ke matar dan uwa na ne yanzu ...even if i know ur love derseve a fight back from me ..amma saood ya fi karfin komai a waje na...Ana barin halak kodan kunya ko?.. Tin da ya zage yana maganan nashi bata daga ido ta kalle shi ba,Dada sanyi jikin ta tayi data ji wayannan kalaman nasa Da sautin magiya ...yace kar ki bata ranki dan Allah kinji ...comon sit let me tell u who saood is to me nasan zaki fi fahimta ta ...jikin ta ya mutu amma bata so ya fahimci hakan,a haka ta kyale shi ya jawo ta dan dole ya aje ta kan cushiion dinsa,shima gefe da ita kadan ya zauna yana fuskantar ta Nan ya fara bata labarin rayuwar sa da saood tun suna kanana... Tayi shiru ta nitsu..,dukan hankalin ta ta mayar kanshi har ya gama bata labarin Cike da kyakwar nazari a kwakwalrta sai taga kamar Kusan abu daya ne ya faru daga cikin labarin amana da sadaukarwan da ke tsakanin ta da junnut babu maraba acikin labarin face su da suka kasance yan uwan juna.. Kaaamil ya bata labarin yadda saood ya dawwama acikin sadaukar da farin cikin sa da rayuwar sa akansa tun suna yara har suka girma.. Yace cupcake,zan iya fitowa bodly nace shikadai ne zai iya mallaka min ranshi babu tantama... wani labarin daya rike aranshi tsawon lokaci bai manta ba ya shiga bata atlast yace Alokacin da mukaje wani yakin hadin kai cikin wani makaken jeji achan kasan syria,..yaki yayi muni sosai dan munyi kan biri da makiya kuma munsha wuya sosai nikaina da harbi uku ajiki na nake numfashi. ayakin duk sojoji na sun mutu saura nikadai,hakan yasa aka hada da taimakon team din sa'ood har aka samu sassauci. To kusan dukan mu da raunuka masu nauyi ajikin mu bazaiyi mu cigaba da ayyana komai ba Aka bamu other daga sama akan mu bar wajen cikin minti 10..100mtrs run tsakanin mu da jirgin mu kuma jiki na yayi laushi bana iya daurewa sosai.. saood ne comander so ya sa aka rirriko ni "Daga nan Gudu mukeyi kowa na neman ceto ransa at dying minute wani sniper ya harbe wanda ya riko nin sai ya sake ni ya fado gawa agaba na tsoron kar nima asame ni yasa na dunkule awajen naki na ta shi,.. ...da ba aganni ba so,atake aka bada saood oder ya tuka jirgin da ni dama ya kamata na tukashi Ga Abokan gaba suna daf da riske ni niyyar ogogin mu alokacin shine a barni ajejin su suyi tafiyar su,saood ya kasa hakura kwalla min kira yake againts oll odds yana nema na,anan sai da ya rufe idon sa ya taka babban dokar kasa ya kuma saka dukan rayuwar sojojin sa a hatsari Dan ya ceto rayuwa na... Kar kice dayayi hakan ba asamu nasaran kashe su ba,amma babban laifi ya aikata wanda yasa aka azabtar da shi azaban da ko mahaifina daya haife ni bazai iya karban rabin shi sabida dani ba... Da muka dawo kwana uku bangan shi ba,aje shi sukayi a dakin horo He was beaten and tortured by a wicked comando.. ..kwanan sa sha hudu a prison sanda suka galabaita shi...kinga wannan labarin?bazan taba mancewa da shi ba a kundin tarihin rayuwa ta.. Har yau nasan iyaye na da suka haife ni ma baza suyi min hakan ba. To meye soyayya da bazan sadaukar masa ba? ..agani na wannan wani dama ce da Allah ya bani dan na saka mashi da iya abunda yayi domina arayuwar sa ..kaamil din dakike gani ba shi bane idan babu sa'ood. In kinga hali mai kyau awaje ne ya birge ki dauka Shi ya bani tarbiyar sa.. Ya kalle ta calmy with much seriouness a muryan shi..Kiyi hakuri cupcake nidai wallhy na hakura dake. ..ki rike min shi amana kinji?. bro yana son ki kuma kece mace ta farko a rayuwar sa.. Labarin san ya bata tausayi,kallon sa take duk dama hankalin ta na kan Yanayin mood din daya dora akan fuskan sa Wani Nannauyan ajiye zuciya kawai ta sauke ta masa shiru kamar mai tunanin wani abu aranta,..cikin ranta har mamaki take yi sosai daya kasance Rayuwar ta kusan iri daya ne dana mijin ta saood thy always secrifice.. farin cikin su kullum na wasu daban ne bana su ba. Yanzu kam Ta fahimce kaaamil din sosai. ,...taso ace haka junnut ma tayi tunani..but ta bata uzuri..ta karbi rashin gaskiyar,but a ganin ta bai dace suyi nisa cikin wannan hali batare da sun fahimci juna ba. Tayi ajiyan zuciya ta dago ya kalle ta..,nan ta gaya masa abubuwan da ta raya aranta game da al'amarin tana mai wayar masa da kai akan kamancecceniya dake tsakanin yanayin rayuwar sa da khaldun da wanda tayi da kawarta junnut.. Ayanzu Tasan ita khal ya fara cewa yana so ba junnut ba,amma yanayin yadda junnut ta birkice yanzun shine take neman shawarar sa akai. Rimi rimi ta gaya mashi abunda suke ciki da junnut ayau din. Akarshe Tace mashi"wallhy She is upset with me, bata taba yin fushi dani irin haka ba..muryan ta a maraice looking so down to earth kamar marainiya ta karashe Dan dariya kawai Kaamil yayi,he relax his head first kafin ya dago ya bata amsar ta "ai halin ku ne na mata,wai ku kishi,. Dama dai haka kawar ki takeyi Ko a Us ma ita dai dama bata da hakuri ne.. Am sure da wata daban ne ma da zaki ga drama Amma nasan tana sonki sosai,ki kyale ta kawai intagama fushin zata fahimce ki... "Tace Allah ko?..sai naga kamar bazata yafe ni ba...taki fa ta saurare ni..kaamil yace chill cupcake,just let her be.. kedai kije kiyi tunani shin zaki iya zama da ita a matsayin kishiiya? if ure sure zaki iya din,sai ki fada min.. toni zan tayaki mata bayanin komai zakiga komai ma wuce.. Bahi ta sauke numfashin ta cike da sauke ajiyan zuciya ta kalle sa tana masa godiya.. .. murmushi kawai yayi baice uffan ba yafara tsokanan ta yace mekeki shirya mana ne na honeymoon..saura kuma akashe yaya na da soyayya... Ta harare shi ta dan turo baki kasar wuyar ta