Sashe 114
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan haka Bata son cika damun ta sai dai ta sai maasu aiki suna duba ta suna gaya mata halin da take ciki. So take sai junnut tayi sanyi kafin taje mata,tasan suna da kishi sosai,so is not advisable taje mata da shawarwarin da take sakawa aranta har sai ta dawo hayyacin ta. Bahi na tashi da asuba ta nufi windown site din gym dinsa don ganin ko ya dawo amma bata ga alaman haka ba, ta tabe baki ta koma tayi kwanciyarta don ba sallah take ba. After 25minute tana na kwance n tana tunanin ko me ya hana junnut zuwa mata har yanzu,nan taji an bude kofarta ta Mike da sauri don tasan ita kadai ce a site din..ya tsaya daga bakin kofar fuskarsa a dan daure yana kallonta, kasa kallonsa tayi ta koma tayi kwanciyar ta ta juya masa baya,jin takunsa cikin dakin yasa ta kuma mikewa xaune da sauri kamar xata yi kuka tana kallonsa, ya balla mata harara yace "tashi ki dauko hijab din ki" mikewa tayi a hankli fuskar ta daure ta bude wardrobe dinta ta ciro hijab ta saka, karasowa kusa da ita yyi yana mata mugun kallo,"gaban su dad zamuje zaayi miki tambaya saura naji kina maimaita abunda kikace ma mum jiya.. Kawai gyada mashi kai tayi a tsorace dan tun jiyar daman take jin shakkun shi. Sai suka fita Yana gaba tana biye da shi,bayan ya gaida iyayen nasu itama ta zauna...,kaamil ne yayi sallama ya shigo shima. Dad ure needed urgently ...alhj hamood ya kalle jahan yace ok carry on,duk abunda suka yanke sai a sanar dani... Hakan ya dada sa gaban khal ya fadi amma sai ya matse ya hade rai yana saurar yaji me za'ace Jahan tace kaaamil nemi waje ka zauna kai zakayi mana shaida.. Ya nemi waje shikam,yana ta satan kallon bahiyya. da suka hade ido,wani Murmushi suka sakar ma juna sunyi kifi kifi suna comunicating da idanun su Nan jahan ta shiga tambayar bahiyya ko tana so ta cigaba da zaman auren.. Tace kwana kadan ya rage a yi hidimar, kinga tun kafin iyayennku sugama riritawa is better ku yi magana daya sai ayi ta ta kare. Khal ne ya fara magana cewar sa shi yana son auren sa ..thou bayadda suka so ya fada ba ya fada..shi sam baiya don cika sauke kansa Bahi ta maida kai kasa,tayi ajiyan numfashi... Cikin sanyin murya tace mum,ai nagaya maki nikam bana so..ta turo baki Jahan taji wani iri aranta amma ta fuske tace ok noor di na ..tunda baki so Allah ya kawo wanda ya dai dai Kwanan nan sai ayi naki bikin ko? Ta gyada kai a slow...jahan tace hope is soon dan bana son ki zauna hakan nan..bahi tayi saurin gyada kai ...khal kallon su yake amma aranshi ya gama jin kamar ya shakure su... Dai dai nan aunt murja ta shigo da tsokonar ta,da dai bata san kan maganan ba kaamil ya shafa mata a kunne,khal ne cikin su ya tsime baya cewa uffan bai cika daga kai ba,hirar bahi da jaahan na mugun kona shi..ga nan kaamil da aunt murja sun fara wani irin annoying site talks agefen sa suna yi suna matse dariyar su,aunt murja tayi gyaran murya,.Kamar bata san da shi "mum,ashe noor ba rabon Aaban bane.. To mudai bazamu yarda abawa bare ba Kawai ayi Yar gida tunda second angon yana shirye ..kaamil dauke kai yayi kamar anbarshi a duhu bayan shirya hakan sukayi yanzun nan.. Ayayin da jahan ta kalle su kaamil ya kashe ma bahii ido..Cike da mamaki jahan tace Second angon?.. Aina kenan,..khal ya dada daure fuskan sa sosai kamar zai fashe... Aunt murja tace mum baki sani ba? Ai abun dayasa ni baxan damu ba sabida na hango fa kamar angon namu agidan nan yake ..jahan tace nonsense bana son maganan banza ...tace ohhh mumy what if bahi rabon kaamil ne..ai sun dace ko Tsaki mai sauti ya kufce ma khal,... Dukan su sun sha mamaki Nidai ayi araba auren nan noor nake so nagani cikin sabon kayan auren ta ...ko bahaka ba noor? bahi ta dago da murmushin ban mamaki tana washe baki..suna tayi nothing is funny akan fuskan saood,mikewa yayi yabar wajen a sadade,... jahan tana binsu da kallon tuhuma... Dariya kaamil yayi yace mum wallhy wasa take miki.. Jahan tayi scolding dinsu,hira mai dadin gaske sukayi kan bahiyya na kafar jahan tana lailaya ta cike da nuna mata gata. Anan Har ta gaji ta barsu ta nufi site din junnut,bata fasa ba lallai tana so su fahince juna.. Site din ya dau wani shiruu na ban mamaki isar ta bakin door iya bugawa tayi amma babu wanda ya bude mata kofar Haka ta gaji ta fice daga site din mai gaba daya Saood Shikadai yake tafiya yana zaga saman benen site dinsa ranshi a matukar bace.. This girl is jokin with me Wai ni zata rinka juyawa? God pls me zanyi mata tasan ina son zama da ita har abada? This is geting serious,bazan iya jure wannan wasan ba.. Brother?... Muryan subaya ya dakatar da shi daga tunanin shi,sai ya wani lumshe idon sa ya sake budewa kafin ya juyo... Subaya Tana tahowa tana magana "What is wrong?...ya naga ranka abace" Yayi furzan iska,duk tashin hankali ya nuna a idanun shi Huhhh,i dont know,nidai nasan Duk laifin ki ne Subaya,.. ure very close to her amma baki ko gaya mata abun daya dace. ..,kinaji ta hada kai da mum xata raba auren nan u kept quiet wai sau nawa zan bada hakurin ne? Subaya ta sa fuskan tausayi "Khal..pls calm down.. Akan bahiyyar me kake daga hankali ?Ta fada da sautin damuwa tana matsowa kusa sosai ..yace ni Kar ki fada min haka..kinsan ina son ta and right now cewa take bata son zama dani,and mum is on it..ya kuke son nayi? Tayi sauri ta dafo shi,Khal pls listen ka kwantar da hankalin ka..ni wallhy bansani ba ma. Bahiyya ce take cewa araba auren ku.? Ya ja tsaki Msssw..yana mai dafa balcony da palms dinsa yana wani irin sassanyar hushi He is really anoyed,bari ma yanzun daya hango aunt murja tana shigowa site dinsa Sai Ya juya ya kalle subaya Da Allah ki fita..wai ina masu aikin gidan nan..dint i said kar ana barin kowa yama zuwan min site.. Bunch of nuisance. pls leave.. Kije subaya ni nafasa maganan dake. Aunt murjan ta san duk da ita yake mitan nashi,bata fasa ba kuwa sanda ta iso har gabansa tana kallon yadda bacin ran nashi yayi affecting mood din subaya. Tayi tsuka.. ..Aaban wai meye wulakanci dan zaka rabu da matar ka shine kake sauke ma kowa Ya bata ransa sosai,ta lura idanun sa na neman sauya kala yaki kulata baice mata uffam ba "Ohon maka,yarinya is already making arrangement for her future auren soyayya..kinaji kuwa subaya,? bahiyyan ma tace kaaamil ne next angon namu..i know thy wll look so cute together, kinsan kaaamil fa dan duniya ne,gashi hot guy ga sense of humour,a yadda noor take danye sharr ai idan akayi hadin nan kuma sai anga abun da ya nade ma buzu nadi. Yake kawai Subaya tayi,cos taga yadda bro din ta ya tsume A sadade tace,bahi da kaamil sharp sharp haka Ant murja na satan kallon shi tace eh mana,..wai me zaa jira abu a gida? before she realise khal ya kama hanyan sauka kasa yabi ta step dawowar sa ke da wuya sukaga security har biyu abayan shi,ya tsaya agefe ya dake ya hade rai.. "Show them the way.. Aunt murja ta kalle shi tana sallamewa Aaban?meyayi zafi Bai ko kalle su ba Subaya ta kama hannun aunt murja dake tambayar shin sikinini tace ant mutafi kawai,dan mood dinshin ya fara bata tsoro Security sunsa su agaba aunt murja ta watsa masa hararar oho dai Tace To muntafi..ta tsokane shi ..bazakace min gudnite bane bani na kar xomo ba rataya akaban "Just leave me alone murja ..iskancin banza kawai. Murmushin data sakar masa ya dada kular da shi. Ba sani ba sabo ya sa aka musu jagora har waje kafin nan ya wuce dakin sa.. Anan ma kasa xama yayi,ya juya wayar sa yafi sau goma amma ya rasa wanda zai kira ya gaya masa kalma daya mai dadi. Wai kaamil take so?hmm msw ..kaaamil din ya kira atake..cikin mintina goma kaamil ya bude kofar ya shigo Bro u called? Khal ya juyo ya kalle shi babu sauki.. Yess,wai menake ji kuke fada daxu.. Kaaamil ya dan shashantar da fuskan sa alaman what? irin baima fahimce shin nan "Zaka maida ni abokin wasan kane..She is still married to me...can u ppl just respect that Kaamil sai yayi shiru ya nitsu dan da fusata khal ya fadi maganan Bro..nifa bance komai azancen nan ba..cupcake ce take ce musu wai ni take so Cup what? Cikin wata dalakkiyar murya yace ma kaamil din Kaamil yana sosa gefen kunnen sa yace cup..ca...ke "Wani banzan suna ne wannan? will u get out?" "Im sorry..kaamil ya furta da sauri yana satan kallon shi 'out...ya masa nuni da kofa sai ya fita abunshi Murmushi kaamil yayi yana dariyar sa aransa. Aranar gaba daya khaldun bai gane komai ba,bahiyya tunda taji ant murja tana mita akan abin daya musu sai ta shafa ma kanta ruwa bata je site din ba ..kin shigowa part dinsun tayi har dare gashi bata ganin hilda ma bare junnut Yau kwana biyu kenan amma har yanzu basu hadu ba Wajejen 9pm khal bai dawo ba,gashi yau hjy indrah tana less busy,about gyaran jikin amarya da xaa fara mata a goben sai hjy ta kora ta dakin mijin ta tace maza kije ki kwanta danki tashi da wuri Haka ta ja kafar ta zuwa dakinsa tana yi tana leke Tana ganin baiya nan kuwa tayi sauri ta kimtsa ta lume kan gadon sa nan da nan bacci ya kuma dauketa. Karfe biyu saura na daren Khal ya shigo dakin,kallo daya yayi mata ya dauke kansa ya kulle dakin da key sanann ya nufi inda wayarsa ya ke ya dauka ya ajiye gaban mirror,nan ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa can nesa da ita,juyi yake yana lazy turns sam ya kasa samun bacci,yau anci kwana daya saura kwana biyu,bayan minti talatin da kwanciyar sa