← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 173

Sashe 80

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka baje,after so much conversation and happy moods.. Nan junnut take ce ma bahiyyan ai jiya suka dawo nigeria daga persia, kuma dama tana so ne idan sun huta sai taje neman ta a kaduna wajen ummah surbajo Duk abunda junnut ke ciki arayuwa na ci gaba da cikar burin ta sanda ta ayyana ma bahiya step by step,har labarin hilda bahi taji amma bata gaya mata komai akan khaldun ba Bahiyya ma ta bata labarin yadda destiny yayi da rayuwan ta zuwa gidan jahan Aarah,har junnut ta gane cewa ashe jahan Aarahn da bata taba gani ba itace uwar rikon bahiyyar ta Duk dama taji labarai munana akan jahan Aarah daga wajen su dilshad,amma sai yau taji tana son ta da bahi ta gaya mata yadda suka rike ta da amana da son gaskiya. Ashe kina london? Ai dana sani da wallhy nima chan zan koma Bahi tayi dariya tace ai na gama,shiyasa ma kika ganni anan Junnut tace nikam ban gama ba ina ganin ma kamar ban fara ba...ina first degree ne yanzu....my mum tace zanyi masters kafin nan musan nayi.. .i still wanna be that girl kinganne,irin matan nan dai da idan babu su babu duniya,kuma babu sha'ani..tana ta zuba Bahiyya tana kallon ta tana murmushi chan tace junnut Har yanzu baki ko zanca ba,Ure still that mrs ambitiuos girl.. Wani rau da ido junnut tayi ta mike tsaye tana wani juyi cikin jin dadai,tace look at me bahi ke yanzu bakijin dadin yarda rayuwar muya dawo,?ki kalli fatar jikin ki..duk dama yanzu naga kin kere ni a kyau but i do have evrything im dreaming of saura kirissssssss sauran ma jira n suke yi. Bahi tace Allah ko? Wani dariyan sukayi suka dan tafa Junnut bata damu taji maye alakan bahi da khal ba tun dama taji ance mahaifiyar sa ce tayi adopting din bahi ne ....she just assume thy are con-curent siblings babu wani connection For the main time Bahiyya taji ta cikin sabon yanayi,tace lallai Allah shike yadda yaso..if not bazata taba kawo cewa yau zata ga junnut din ta ba Anan junnut ta rike ta dam hira kala kala...kowa na fadan nashi damuwar Sirri biyu ne a tsakanin su,bahi bata fadi tayi aure ba ke junnut bakice kinada mijin aure ba Sannan A duk damuwar du da suka tada haka ma bata gaya mata ko kadan daga labarin zaman ta mai muni daya shafi sadat ko khal achan gidan She was just awwed dayadda taga junnut ta dawo,ga guntun skirt cinya awaje,ga wasuxuka zukan nails da sukaji red tinted curtex..tasan dai junnut tana da dogon gashi irin nata amma kuma attchement ne akanta ayanzu. Sunfi awanni suna magana non stop,haka junnut ta matsa har bahiyyar ta yi amfani da bathrum din ta tayi wanka cikin nishadi da kewar juna suka zauna akayi serving dinsu abinci suna ci suna hira Bangaren khal kuwa gaba daya ya rasa meke masa dadi game da yawan tunanin bahiyya,..he wish zai iya jin ya tsani bahiiya amma its not feeling like it.. Yanzun haka fushi ma yake yi dakansa amma shikan sa bai sani ba He look down and angry,dandanin murmushi babu a fuska Side din dama nashi ne shikadai just like yadda yake agidan jahan mahaifiyar sa Yanzu ma Kiran ta ne ya tuno masa da cewa bahiyyar bata fa biyo bayan sa ba,. He was like ohon mata inma taje wani abu ya same ta shi babu ruwan sa. Wanka ya fada ya sauya kayan sa zuwa simple long sleev shirt da trousers,yana famar combing kansa agaban mirrror saiga kaaamil ya shigo Ba yabo ba fallasa suka gaisa.. Shikam ya rasa meyasa yaketa famar zumudi akan bahiyya... Not too long ya fara zubaa ma khal labarin duk abunda ya faru Shida baiso yanajin maganan ta amma wannan ba karamin buga masa zuciya yayi ba.. So bahi and junnut are best friends!! Ya maimaita wannan maganan a brain dinshi yafi sau goma.. Witout showing any major concern,ya amsa tambayar kaamil dake neman sanin hadin shi da bahiyyar. Sai kawai Yace masa shima hadota da ita akayi,acewar sa jahan Aaarahs adopted doter ce Kaamil was like wowww ...kace ma yar uwata ce Ko kula kaaamil baiyi ba dan kuwa Ba karamin zafin yake jin aransa ba musamman inyana tuno ranar daya zage yake bada kaamil din labarin ta Cikin zuciyan shi cewa yake She is the twinkle i wanna show you..but not anymore ...not eva.. I bet im not the guy Nayi nadaman bude zuciyata ma wata yarinya kuma sai ta san dawa take yi Tare suka fito dag sashen nashi kaamil na taka nashi zasu je suyi gaisuwa agaban su dilshad Hira sukeyi kadan kadan,nan yake jin cewa ai bahiyyar tana can wajen junnut so bai wani damu ba Isar su ya fada yayi gaisuwa,cikin so gata da nuna kaunar su suke tarairayan sa Shima sosai ya nuna jin dadin sa game da dawowar su nan nigeria... Musanm ma zuwan ita kakan nasu dan ita tassa shi har ya mata alkwarin cewa zai daga tafiyar sa dan ya mata kwana biyu. Dan itama tafiyar zatayi nan d wata guda Hira sukayi mai tsayi tsakanin su su hudu,basu ko kawo maganan junnut ba bare bahiyya Most of their talks is eida politcal or official har dare yayi kowa ya watse zuwa site dinsa To Kiraye kirayen jahan din ne yasa bahi ta dan matsu dataje taga inda suka sauka da mijin nata.. Ga Junnut ma ta gama sarai zasu kwana tare amma sai ta ki sam Duk dama yaune rana na farko da junnut ta taba mancewa da shafin khal kawai dan taga bahiyyar ta Nan ma da kyar suka rabu,Har nite gown mai kyau ta sa ta tasa dan dole tayi mata kwalliya ta zaunar da ita ta dada gyara mata kai tun anan suka fara musun yadda kowa yayi wayewar sa Junnut cant beliv that bahi har yau batayi irin budewar idon da ita tayi ba,...a haka dai ta hakura ta shirya akan zata raka ta zuwa site din khal Wanda ko rabin shiga basuyi ba jahan khatun ta raba su da kira She just dont like the girl,sosai ta raina kurwan bahi..wani gani gani take mata Tana mata kallon kaskanci da rainin wayo Cikin ranta tace hala ma yar bola ce aka dauko aka laka ma miji na dan tunda akace mata daga wajen jahan Aarah ta fito ta ji yarinyar sam bata mata ba Ko yanzun ma ta dade tana kallon su daga sama Kyaun bahiyyya har yana dan raxana ta. Haka kawai takejan tsaki,tsaki irin na hassada da nuna kyashi, badon ma khal ya bada oder lallai bahiyyar dashi zata zauna a site dinshi ba da chan wajen gidan baki zata sa akaita and she tot that wannan kawancen nasu a wajen ta is baseless aganin ta junnut din ta bazata taba hada hanya da kaskantatun kawaye irin wannan yar ba Bahi kuwa tsoro ma take ji in taga irin kallon d jahan khatun keyi mata .gaba daya bata do su cika hade idanun su Datakira junnut din ko ta dan hada ta da maid,haka bahi ta lallaba dakanta ta isa Akan gobe da safe duka zasu hadu Tafiy takeyi tana gode ma Allah tana kuma jin fargaban haduwar ta da khaldun Ashe wai yau ne first weding nite dinta? Tsaki ne ya kufce mata haka kawai bata san dalilin shi ba,dawowar junnut rayuwan yau ma kawai ta yasata taji wani sabon karfin gwia da karfin zuciya Wajen shiru babu kowa,amma da shike the same design ne da gidan su,babu tantama ta san wani kofar ya kamata ta shiga ta same shi Tana tabawa kuwa taji damm alaman an kulle da lock ta ciki Nan Tayi tsaye tana knocking almost 1 tana abu daya amma bata ji am bude ko an bada izinin a shigo ba Yana jin ta dan Yana zaune akan gadon sa ne yayi shiru yana fama da tunani kala kala aransa sa with each pain dayakeji shima so yake ya mata wani abunda zata ji abunda shima yake ji Ganin ta tsaya har taji ba dadi tuni Ranta ya baci ga bacci ga tsoro,chan dai wani abu ya sa ta ta zaga ta baya..aikuwa tana bullowa anan ta hango shi ta plain glass wall dake hango kan gadon sa direct wanda ya bada wajen mermaid world look mai gaba daya.. Wowwww tace aranta tana ware sleepy eyes din ta da kyau....daga dakin nashi zaka iya jan glasss ka bullo cikin backyard din room din wanda aka kawata shi da wasu marayun flowers masu gamshi da tsari gawata shekikiyar blue water pond mai shape din kwakwa white swan ne suke shawagi aciki Bata ma damu da kallon cikin room din ba tukuna ta tsaya kare ma wajen kalllo Sanda ya ishe ta sannan ta iso gaban glass wall tana kallon ciki tana neman ja dan ta shigo. Its heavy ..nauyin shi yasa ta kasa motsa shi...gashi yana da yawa sosai...2 coners ya rufe... Anan Wani zuciyar na ce mata ta masa maga a hala zai jita, but Ganin ya diro akann gado yana dosowa ta inda take yasa ta dakatawa daga kokarwar da takeyi da dooor din ta tsaya kallon shi.. Wani irin kallo suke ma juna ta glasss din as he was coming vwry closer fuskan sa babu alaman rahma.. In yana ganin ta Zuciyar sa taba masa wani irin zafi Son ta yafi rikita masa tsarin yanayin sa fiye da abunda ke tsakanin ta da subaya Ita kuwa kyau ya mata sosai,duk dama tana yar tsama da shi but ta shagala tana kallon sa cikin wani yanayi...he look soo handsome and gentle acikin white pjams din shi da bai saba sabawa ba Sai taga ya kama draw open din She tot bude mata kofar xaiyi sai ya dauke kansa tana gani yana danna wani abun god knows meyayi ma kofar amma tabbass dada kullewa yayi Yana gamawa Ko sake kallon ta baiyi ba ya koma yayi kwanciyar sa tana tsaye tana kallon shi Kwanciyar sa yayi kamar baisan da wata ba Looking at her straight in the eye ya danna wata remote tuni taga wasu shegun drapery curtain marasa nauyi suna haduwa da kansu suna neman mata katangan
Chapter 80 · 0% Book details