Sashe 15
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
8 ya gauce toh nasan lokacin cin abincin sa yayi Sai nayi sauri na sauko cike da sa'a kuwa na ganshi yana kokarin shigowa part din A gurguje naje na fara shirya masa abincin,gani danayi ya zauna bisa kujeran dinning din ya dada bani karfin gwiwa so i served him kamar yadda nake yi,yaci abincin kadan ina tsaye akan sa har ya tashi ya bar wajen kallo na baiyi ba bare yace min ci kanki. Haka ma yau da daddare dana zo serving dinshi dinner wani azakzalan masifan danaji yana yi ma wasu agaba na sai danaji hanjin ciki na ya kada ya gamutsa kansa. Mennhn gayen is quiet tempera mental masifaffe ne babu karya. Dan haka nima nabi shi sau da kafa har muka rabu lpya na koma dakina batare da ya sauke min ba Washe gari da safe tsoro ya hana ni aiwatar da komai mint tea din dana dafa mashi ma ban kai dakin ba ajewa nayi na hada tare da abincin shi akan dinning tunda nasan yanzu ya hanani shiga dakin sa,Jira nake inya fita naga me zan iya yi,. Ina tsaye sai gashi nan kuwa ya fito cikin shirin sa tsaf da alaman fita ma zaiyi ,da sauri na dan rusuna kai na gaishe shi duk dama nasan bazai taba amsa ni ba. Wuce ni yayi kamar mai iska nima sai na dago kai na biyo bayan sa 'Zaman sa yayi agaban table din baice uffan ba ya kama shan shayin dana ajiye baiyi korafin komai ba,.araina naji dadin haka Sai nayi serving dinshi abinci na tsaya a position dina ina jiran shi ya gama cinyewa na koma kan aiki na akan empty seat dake kusa da shi ya aje Jacket din Bakin fitted Tux din daya saka ajikin shi sai ya bar pure white shirt dinsa a bayyane Sai naga gogan ya dage yau dayawa ma yake deban abincin yake ci,. This guy is too perfect,i cant deny that zuciya ta har ta fara crushing akan haduwar sa in ina kallon sa har bana jin nagaji. 25 minutes of chewing ya aje spoon yana kokarin goge baki slighty da food napkin bai mashi ba ya ajiye Mango juice!!! Ya fada baiko kalle ni ba wata tsadadiyar transparent glass na rarumo na shiga zubawa toh bansan meya faru ba sanda nake haba haba na debo na mika masa Shin nice ban rike da kyau ba ko shine ya buge ni all i saw was dukan juice din ya subuce daga hannu na ya kwarara masa akan farar rigan sa Sake kofin akan table nayi a slow motion Da sauri na lumshe ido baki na bari na firta innalillahi waninna ilaihi rajiun wani mugun kallon barazana ya bi ni dashi ayayin da yake kokarin mikewa yana exclaiming da bacin rai afuskn sa Ban bari ya gama tashi tsaye ba na raromu napkins arude na taho zan fara goge mashi. "dont you dare touch me" ... Cikin wata irin tsawa yace min A gigice na koma baya ina neman hado kalman hakuri. Ko saurara ta baiyi ba ya haura sama a fusace, kusan minti talatin wajen ya dau shiru chan sai gashi ya sauko da rigar a fuskata ya wurga yace "I want it the way it is".bai jira na amsa ba Ya sa kai ya barni a tsaye Yana fita nayi saurin deban komai na bar wajen. Sai da nagama aiyukana tass sannan na fara wanke rigar . Ba wani stain din kirki ba ne amma Na wanke na wanke yaki fita tass har Raina ya baci. ..wannan wata irin material ne haka?,i used evrything in the loundry sai kace wani kayan sarkin aljanu?to meyasa tabon juice din bazai goge ba? Yau kam danaga babu mafita sai na fice na shiga asalin haraban gidan ko zanga ammuh adama na nemi taimako I cudnt find her sai nahadu da mami fatima": Tasha mamakin ganina awaje amma saukin kai da iya ladabi na yasa ta amsa min bukatuna Cemin tayi bata san inda ammuh adama take ba amma indai dan fitar da stain ne a riga tana da abun da zata bani na yi amfani dashi. I was happy sai nabita ta dauko wani concotion ta bani,daga ji lemon tsami aka tula aciki.. Godiya nayi mata na dawo dakin wankin,ba bata lokaci na tsoma rigar da wannan abun na shiga dirjewa yayi kumfa sosai har ina murna ko kayan zai fita Ban tashi shiga uku ba sanda na dauraye naga duk stain din rigar bai gogu ba infact ya sauya kala ne ma daga orange stain ya dawo kalar bacaccen bula duk yayi layi layi Ya ilaahiiii.. .i was not happy amma haka na daure na busar na kuma goge shi da kyau tunani na ko zai ragu amma ina kamar ma kara fito da shatin abun nayi. Haka nayi ta fama har nagaji ya yanke hukunci kai masa rigar sa hakan inyaso na bashi hakuri. As usual bamu hadu ba sai wajen cin abincin dare Har nagama serving dinshi yaci abincin baice min komai ba sai ma naga kamar shirin mikewa yakeyi zai shiga daki Ohhh Alhmadullhi Kenan ya mance da batun rigar? Tuni naji sanyi na neman mamaye cikin raina Sai dai fa Kan na sake wani motsin sai naji yace min ina rigar shi? Dumm na tsaya kamar wanda aka kira mata kalman mutuwa.... Gaba daya na rasa ta ina zan fara dan ban shirya ba. Amma da shike nasan bazai maimaita tambayar ba sai na shiga jero ...i..i. .na cikin rawan murya nace Ummmmm pls im sorry sir....kayi hakkku..ri na wanke rigar sosai amma stain din yaki ficewa.. Wani irin kallo ya bini dashi Shi dai Bai sauya fuska ba amma ya dauke kansa .. Yace shikenan kije ki cigaba da wankewa in yafita zaki iya yin bacci yau . Kaiwa nan ya haura sama ya barni a tsaye nayi durus kamar wata shanyayya Haka na ja kafata zuwa dakin wankin god knows bazan iya sake wankewa ba dan na san babu abunda zanyi ma rigar ya dawo dai dai,na lura komai dada lalacewa yayi, evrtyhing become worst dana saka wannan abun da mami fatima tabani Wani zuciyan yace na gwada takurawa wajen bashi hakuri mana ko zai fahince ni Haka na fito da rigar a hannu na har bakin kofar sa na kwankwansa kofar kimanin minti 13 sannan ya bada izini na shigo Yana zaune Ko kayan shi bai sauya ba,ya wani hakimce gaban tv yana kallon wresting asalin wwe raw na zamanin tun undertaker nada siffar abun tsoron sa. 'Ni wannan bai dame ni ba domin kuwa banyi kasa a gwiwa ba na rusuna kan duka kafata nayi kneeling agaban sa da rigar a hannu na nace " dan Allah kayi hakuri sir,nasan nayi kuskure. .nayi ta gogewa yaki fita ne pls am soryy sir Ina karasawa nayi shiru Thank god dai murya ta batayi bari ba Sai dai ko kallon arxiki baimin ba bare ya san inayi. Haka na maimaita har sau uku bai amsa ni ba i was so scared and doom Duk Sai na rasa me ke min dadi Sanda naji wani ruwa mai gishiri gishiri nabin labba na kafin na san hawaye ne ma suke sauko min. Duk dana yi sauri na goge sai dada tuluwa suke yi,haka kawai naji raina ya baci sai dai bani da ikon yin wani rashin kunya ko magana shesaheka ta ma a sadade nakejan ta kar ma yaji ni na harzuka shi yace zaimin wani abu. Haka na ci kneeling har na rabin awa agaban sa rike da rigar, idanu na sun gaji da fiida ruwa dan kansu suka bushe. Bacci ya dame ni dan nagaji sosai Dana ga dai baiya da niyyar min magana sai kawai na tattara kaina cikin sanyin jikin na tashi na bar masa dakin sa. Da nake fitan ma Na dauka zai daka min tsawa ko yace nafita ban tambaye shi ba,amma shiru baice uffan ba har na rufe kofar na bar site din. Tsaban damuwa da gajiya ban iya kai rigar dakin wanki ba dashi na kwana a gefe na. To my surprise da safe ina idar da sallah naji ana buga min kofa Toh yau kuma waye wannan? Tunda nazo nan part din gidan babu wanda ya taba zuwa daki na sai ammuh adama tun aranar farko I was Shocked and surprised at same time but ban daddara ba na taho na bude kofar Wow...its ammuh adamah!! Wani sanyin murmushi na saki ayayin da ta jefo min nata murmushin muka karaso ciki tare A ladabce nagaishe ta tana daga bakin gado nikuma ina kasa akan dan karamin beige. Tace bahiyya? Menene matsalan ki fatima tace kina nema ta jiya... I hope ba wani abu bane Ya hada ki da shi. Nan na dago kai na cikin damuwa mai dauke da zuciyan kuruciya I wish that ammu adaman tana tare dani kullum dana dinga gaya mata halin wancan mutumin,so i managed to started talking calmy ina fada mata labarin abun da ya faru da rigar sa dan yanzu shine babbb damuwa ta,ita kuwa kamar bai wani daga mta hankali ba Batace uffan ba kam amma Fuskan ta ya nuna alaman tausayawa musamn Da nace mata he is very mean and hard to understand, Wani bin murmushi kawai takeyi cikin ranta tana tunanin yadda zama na zai kankama agidan da alamu ta hango hakan. Chan tayi gyaran murya cikin lallami ta dada ja min kunne akan aiki na,cewar ta kar na biye mashi dokar jahan Aarah kawai zan na bi. Game da rigar kuma wata customised apple vineger ta bani naje agurguje na jika dashi na wanke da machine nayi instant dryng nafito dashi rass I cant believe it dan a take wanann vinegar ya wanke min shi tass ya dawo normal sai na goge ina ta jiran perfect time domin nakai mashi abinsa. Ahaka har nagama dafe dafen abincin safen sa,whith all what ammu told me akan na rike aiki na sai na mance da dokar sa na cewa kar na sake shigo masa daki,aje rigar nayi agefe kamar wata mayya haka nayi sneaking na shiga dakin na kai mishi shayi Yana bada baya na shigo na kimtsa ko ina nayi waje na wuce dinning ina