← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 173

Sashe 58

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi ba Nine na fito maki a daren ranar ba ko?ya kalle abun wuyan yana murmushi,to ni na goge maki mugun nufin ki akaina. I smash,smash ur big head..sabida ki rude....good for ur night huhn? Wani shiru wajen ya dauke dukan su sun gama tsorota sosai kowa ta zuba ma sarauran Allah ido Sai ya kunna wayar shi yana dialing call kowa yana jin komai...shushhhhh Listen, ya kalle su duka sai ya juya mata kan wayar a fuskan ta,video call ne da haka wani mutum a cikin wani medical lab ne ya bayyana sanye da khakhin sojoji hannun sa sanye da white hand gloves yana azabtr da wani dabba da allura a hannun shi abun har babu kyan gani. "..Hy brother pls introduce urself ....sadat ya furta yana sake mata wayar..sai mutumin ya dada kure ta da ido yana mata wani shuumin kallo.. "Mutumin ya fito da id card ya rike mata tana gani,kamar wanda aka kunna redio ya fara gaya mata shi waye.. He is an official medical consultant na brigadier general khaldun saood.. Sunan shi barak adeel...secret bro din sadat adeel wanda ko balaraben daya rike shi ma baisan da shi ba Yana aiki ne a babban asibitin usmc Wanda duk sanda saood zai je wani mission shi zai masa gwaje gwaje ya duba lapiyar sa kafin ya fita. . Barak Adeel Yana katse wayar sadat ya shiga mata bayanin komai,yana dada jaddada mata cewa in har da kashe khal yake so yayi da tuni yasa dan uwansa ya kashe sa.. Yace but bari kiji,duk sanda kika sake tunanin gaya masa wani magana akaina babu bata lokaci zan kashe shi and am not jokin about it..kinga yadda akayi ma dabban nan ko? ..slow and Painful death,..ni zan sa a masa Alluran ciwon da babu maganin sa..sai na wulkanta Kyaun shi daya ke ruda ki kike min taurin kai. Wani sabon kukan ta fashe da shi kamar wanda kanta bazai iya daukar maganganun ba " U see this ur friends toh suma zan koya musu hankali in suna xuga ki kina biye musu. I must have you...ni auren ki zanyi kwanan nan,sai ki dena kuka...Banso muyi haka dake ba ke kika jawo muku Nasan Kinji abunda na fada ko?,..sai ya tsuguna dafff agaban ta yana razanata da mayun idanun sa,...bana son kina yawan kuka,oya tell me sorry! Wani Dada matse kafafun ta tayi cikin mugun jin tsoron sa..Tayi masa shiru ko kadan bata so tama kalle shi Yaja tsaki,johnson call barak kace masa yakai alluran nan cikin lab..my friend here want to kill her little boyfriend. Wani runtse ido tayi jin yace hakan dan tasan da ita yake yi,..johnson yana mika masa wayar ta dago a marairace tace dan Allah kayi hakuri. . Ya wani fashe da dariyar mugun ta yace mene...wani razanannen kuka ne ya kufce mata cikin rudani da firgicewa tace kar ka masa Alluran..get rid of it..,i swear bazan fada mashi komai ba.... Wani marin ya sauke mata y hade rai kafin Yace good girl Ya juya ya kalle su khadija,both of them looking terified and scared. Fix some senses into her head,tsoro yasa suka gyada mashi kai da sauri Untie them...ya bada oder,tun kan agama ta taso da wani irin gudu ta zo ta rungume su suna kuka.. Kuje school,saura naji kun aikata wani shashan shi inada wanda zasu gaya min komai. 'You..yayi nuni da jasmine...case din baban ki a hannu na yake if u try me hyann....ke kuma nasan ida alhaja kafayat take nasan lokacin da jirgin ta su tashi Be very careful with me,daga yau kar na sake jin magana na abakin ku...Kuna jina? Duk suka gyada kai cikun kuka,after 10minutes yasa aka maida su har hostel.. Tun Ranar gaba daya sai basu fitowa a room dinsu ba kuma babu wanda yasan halin da suke ciki. Yau kusan sati kenan,amma basuje lectures ba kuma basu bude shagon su ba... Da kyar suka dawo daidai,amma har yanzu bahiyya na cikin wani hali Tun zazabin kukan datayi ranar har yau bai sake taba kullum sai sunyi ta mata nasiha amma tsoro saida ya kama zuciyan ta Aganin ta saadat ba mutum bane,dabbar jeji ya rikida dan bata taba tunanin akwai mugu kamar sa ba. Babban matsalan ta ayanzu wnnan sihirin nasa,taya zata yi ta kufce masa gashi ko a mafarki bata tunanin zata iya kara numfashi a duniya muddin tayi sanadiyar da zaayi ma khaldun wncan allura.. Cikin kwana bakwai din nan duk da bata da lpyan amma Tare sukeyin nafila,azumi uku sukayi suna kai karan su ma ubangiji har su suka dan samu sassauci Washe garin monday da safe, su dija suka kaita medical care na school anan aka bata gado.. Sukuma Tuesday wednesady suna dan fita lectures in sun dawo sune sukan tsaya mata Likita yace akira parent ko qurdian duka suka hada baki sukace ah'a zasu iya. Domin Komai sun tsaya sun masa fassaran bajewa da taka tsantsan... Sunsan idan suka bari asibiti suka kira jahan zata daga hankali har sai ta gane wani abu,sannan idan suka ce subaya ne basu san meye sadat zai sake aikata musu,gaba daya kansu sai ya kulle Sai suka dawo shiru shiru,not too much amma kana ganin su kasan ba lpya ba. Bahiyya,kullum in zatayi kuka takance kilan dan ita marainiya ce bata da galihu a duniya shiyasa sadat yake mata haka da rayuwan ta,.. Aganin ta yaga bata da kowa ne tana zama sanadin alfarma da hallaci bata da mafita shiyasa zaiyi abunda yake so da rayuwarta,yana cewa yana son ta amma gani take kamar asali ma so kawai yake ya kashe ta. And for khal da bata tabajin zata iya bada zuciyan ta hakuri akansa ba sai yanzu... Ji takeyi duk rintsi duk tsiya bazata iya sa rayuwar sa a wani hatsari ba duk dama tasan kaunar shi shine numfashin ta. To bata sani ba Tun ranar alhamis Jasmine da dija suka shiga neman mafita ta hanyar yadda zaa fara karya wannan sihirn nashi batare da bahiyann ma ta sani ba,..sunsan intasani zai iya ganewa tunda hakan ya fada musu. Sai kawai sukayi booking apointment da wani malamin a india..after 1 week ya amsa su,malamin babban dan shia ne kum yana dealing da irin wayannan Abubuwan...da kyar da tsiya suka same shiga shafin wanda zai taimakawa,with hiden identity suka biya kudin aiki ya musu duk ita kokarin sa sai dai ce musu yayi zai iya cire bahiyya a zuciyar sadat na natsawon makonni 9 amma kuma sihirin sadat mai karfi ne sai an tsinka abun wuyan daga wuyan sa an kona kafin sihirin ya karye.. Da babu gwara ba dadi dan haka suka amince tuni ya kawar da bahiyya acikin zuciyan sadat for the mai time sadat bazaiji abunda ke ranta cikin sauki ba . Da suka tabbatar da aiki ya gamu,ranar tana asibitin ana mata allura dan kirjin ta na ciwo sosai.. gaba daya ciwon ma ya hadu mata harda da damuwan yadda rayuwar ta zai kasance nan gaba...,anan dai suka gaya mata komai.. 9months is enough for us musan me zamuyi akansa... Dija ta fada cikin damuwa... Yasmine itama cikin kulawa ta kalle bahiyyar dake kwance tayi weak tayi fayau hawaye nabin kuncin ta cikin lallashi take shafo suman kanta tana calming din ta Kwarai sun bata mamaki da sukayi hakan tasan ayadda sadat ya yi barazanar tozarta rayuwan su da wasu kawayen ne da rabuwa da ita ma zasuyi.. Amma sai taga kamar wani sabon shaukin son su taimake ta ya kara musu U need to get better,yau satin ki uku kina kwance bahiyya..dont let anything harm ur health dan Allah ki tashi. Hawaye kawai take saukewa tana musu godiyan abunda sukayi matan,yau ta fara gwada musu cewa tana so itama taga ta warken amma hankalin ta yaki dawowa jikin ta ne.. Its obvious that she need a break..tana mugun bukatar inda zata je taji ta free ..inda zata samu kwanciyar hankalin da zai kamo mata tashan ta yadda zata fara da shi. A Halin datake ciki bata iya awa guda bata tuno da abubuwa masu firgirtawa da rudarwa ba Me zata ce ma subaya idan wata rana sadat yasa taci amanan ta Me zatace ma matar da ta dauke kamar uwa idan ta bari hakan ya faru,ko tayi sanadiyar mutuwan dan ta? Ga kuma abokan ta su dija da jasmine ,in har sadat ya cutar da su bata masan ya zatayi ba.. Zuciyar ta ya gama cikewa kota wani fanni,tana kawo wannan tunanin zazzabi ne yake rufe ta atake. A Cikin wata taran nan,nan da watanni biyu zasu fara exam din da zai kaisu ajin su na karshe a jamiar She need health for her studies To anan Yasmine da dija sai suka yanke shawaran da basu gaya mata ba duk dama suna jin dar dar akai,fargabn ya zataji bai hana su sace wayar ta subada aliyu haidar ba, class mate din su ne a nigerian fulani guy. .,he is a computer genious,shine ya taimaka musu wajen zagwalo number khaldun daga wayar ta cikin sauki Sunyi amfani ne da ranar da ya tura mata kudi sukaje shoping,cos both can neva forget dat day Ababu ababu sunsan idan yasan bata da lpya shi zai sata dawo hayyacin ta,aganin su idan suka cigaba da barin ta ahakan zata iya kamuwa da ciwon xuciya Tunda yanzu babu sadat tun awajen dija ta tura masa brief tex messege Ta rubuta "at the school hospital,she is very sick. ." Da yamma ne Yana zaune ga junnut da hilda a agaban sa ta takura shi wai ya kawo su shan coffe cewar ta sun gama exams dama kwana biyu bata gansa ba... Looking at the tex messge saida yaji kansa ya sara,dama kwana biyu idan ta fado masa aransa yakanji wani iri saidai bai taba tunanin daukar waya yasake kiran ta... Did u guys want to go for vacation? Daya firta hakan a bazata suka kalle shi,sai yayi dan quick smirk alaman he is serious. Wani dariyar jin dadi junnut tayi suka kalle juna da hilda..tace yessss...dama mun gaji da us... Ba yabo ba fallasa Yace ok,name a place kafin mutafi saiki fada mun gobe zakuje ku huta Murna kamar zai kashe ta,ta taso cikin rawan jiki zata huging dinshi...ya tsare ta ..mai kankat sai ya
Chapter 58 · 0% Book details