← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 173

Sashe 22

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ sempa fidelis_ Da safe na dade akan gado na kafin na sauko,wanka na shiga zuciya ta cike da mamakin abunda yayi jiya. Ina gama shiryawa na fito na wuce kitchen Na girka masa abinci,bai amsa gaisuwa ta ba bare yace min ya jiki,kuma tun Ina jera mashi abincin ya kore ni ko bari nayi serving dinshi ba baiyi. Haka rayuwata ta kasance like a living hell,ban isa bayi ignoring duties dina ba amma innaje inayi kuma baya kyalewa na karasa sai ya korani Duk sai naji nagaji da ibadan,haka Nayi ta sa kunne ko zanji ance zamu tafi gida amma shiru har muka cinye kwana takwas Kullum inna zauna sai na tuno kano I seriously missed ammuh adama ita kadai ce nake tunanin zata warware min duk wani matsala ta,. haka nayi ta zaman hakuri ban tashi jin meke faruwa ba kuwa sai da najiyo shi yana waya. Ashe cewa sukayi ya sake saka musu lokaci wanda hakan ne ya jawo delay din tafiyar mu. Aranar Cikin dare su kayi meeting dinsu,it was very successful komai ya tafi mashi dai dai. Da safiyar Allah kuwa ko wanke ido banyi ba yasa aka tarkato ni da kaya na na shiga mota akan zamu koma kano Tsaban iya shege shi sai yabi private jet dinsa nikuma yasa aka bi mota dani Kusan tafiyar kwana biyu ana jan mu,banda yawan bacci ba abunda nake yi a motar har muka iso kano Muna isowa naje na gaida jahan Aarah cikin sauki bata ce min komai ba har na fito. Wajen Ammu adama naje,muka gaisa tana kallo na tace baaahi?..Meye faru ne naga kamar kin fada... Nace banji dadi bane amma na warke. Taje ayyah,Allah ya baki lpya khaldun ya sanda haka kuwa? Ko da shike ma naga kamar tun shekaran jiya shi ya dawo me kuka tsaya yi to? Nan na shiga bata labarin abunda ya wakana ina maganan bansan ma hawaye na sauko min ba Kunya yasa Ban dai gaya mata abunda ya faru akan period ba Nace sabida ni yayi kusan buga kansa ko meeting din ma adalili na aka daga har muka ja lokaci.. Ammu Adama Ta ji tausayi na sosai ita da shike ta fahimce mmbi sosai ko fadan ma bata min ba Tace muje ki huta kici abinci,kafin anjima kije ki gyara mashi site dinsa kinga tunda baki gidan nan ba wanda yaje ta wajen Ban yo musu ba,hakan kuwa ya faru ammu ta gama petting dina nayi wanka na huta Chan anjima naf shirya naje site dinsa na shiga kimtsawa fiye smda kwana biyar bamu nan nayi aiki sosai sai dana gaji. A Kitchen dinsa na tsaya na jira domin na mashi abincin dare mai gaba daya,koda nagama nayi serving dinshi baiko kalle ni ba yace min get lost Dama nikam nagaji dan haka da murna na bashi waje,sai dai ko karasa isa site dina banyi ba ba sai ga aikan sa akan cewa naje na karbi kayan da aka shigo dashi yanzun na jera masa a closet kafin yayi bacci Haka na koma na karbe tarin kayan nasa,wasu irin super huge designer shopping bags ne mai dauke da designers shoes perfs,watches and other clothings. Zama nayi anitse ina jera su,ina kuma binsu da kallon sha'awa ,Allah kadai yasan yaushe za'a saka su dan anan dinma akwai kaya da uban yawa wanda ko taba shi baiyi ba. Bayan kwana biyu ranar na tashi da safe sai naga ko ina agidan ya cike da motoci anata sharing plesantries da formalites. I was surprised na fito inata raba idanu, koda naje dakin gogan nawa ma yau a kulle take kuma shima baya ciki. Ammu adama ce ke sanar da ni ashe yan uwan mahaifin khaldun ne suka iso tun daga kasar iran din bada sakon jajen su akan abunda ya same shi kuma tace zasuyi mana Kwana biyu So the house become 5 times busier than normal Da shike gangamin jinin sarauta ne sai suka taho da dokokin su masu tsauri da ban mamaki Wai tare za'a dinga cin abinci kuma duka masu girkin gidan zasu hada kai suyi girki dan haka aka hana abinci ako wani sashi akan bazamu koma normal duty ba har sai sun bar gidan. Tun daga ranar ayyuka suka ragu ma kowa cos komai a dunkule ake yinshi Kullum akan shirya food gathering a babban royal hall din gifan kamar wani feast kuma haka zasuyi ta hira da jahan ana shakatawa. Sai dai anata wannan shagali nr amma ban taba ganin gogan nawa ya fito ba . Iya kaci yazo ya gaishe su ba a sake ganin sa. Gashi jahan tace nabar aikin kar na dafa mashi komai ko dan yazo ya zauna acikin su Amma taurin kai yasa yaki ya kula su har yanzu. Daga haka Kusan kwana biyar ya dauka baya cin girkin gida,shiyasa ma kullum zaka ganshi a daki ranshi a bace On the 6th day daya gaji,sai ya fara aikawa ana kira na yana kuma tursasa ni ina dafa mashi kananan abinci kamar su couslow,noodles,salad da pancakes curstad etc Gaba daya abun nashi sai ya bi ya ishe shi,nikenan bazan dan huta ba duk dama kowa ya sami ragowar hutu? I was literaly upset with him inna ganshi ma haushi nake ji Wani bin sai yaga Anata abubuwa awaje masu sa nishadi zaisa a kirani na dafa masa abu,ko dan baya so kowa ya san yana sani aiki, kullum nakanyi kukuni sai yayi kamar baya jina Toh Yau Ina kallon fire works da yamma ne sai ga kiran sa daga site Ina tahowa naga kwanukan abincin jahan Aarah ta sa an kawo mashi dan dole wai yaci Tsawa ma yamin tsaban ranshi abace yace min" kwashe wayannan abun agabana.. Bance ufffan ba na kwashe zan tafi,yace get me some Noodles..kiyi min sauri. Da gafen idanuna na kalle shi,ina saita kaina zan dau hanya Bansan kukunin nawa ya fito sosai ba sai gashi na furta "Mutum Yana xaune waje daya kullum sai ciye ciye Yake kamar mace mai karamin ciki,Har da dan guntun tsaki na. Stop right there....Ji nayi yace me kika ce? Dan haka a firgice na juyo. Yadda ya zaro idanun shi ya kalle ni nagane komai.. The answer Was clear ...ashe da karfi Na fadI Hakan kuma yaji ni Shikenan yau na na mutu na lalace.!!! One time jiki na ya fara rawa. Da wani irin muryan fusata ya dube ni again yace just turn around. Nayi saurin juyi baki n dakan sa yace babu ko..muryana na rawa Ko da ban dago ido na ba nasan kallon fushi yake bina dashi. Sai na fara bashi hakuri. He remain quiet for some moment fuskan sa a matukar daure kuma nasan ba zai maimaita tambayar daya min bane bayanin abunda na fadan kawai yake jira wanda ahalin yanzu bani da ita. A hankali na dago kaina na dube shi,ban bari mun hade ido ba nayi saurin sauke kaina,karkarwa jiki na yake kamar wacca aka soka ta a kankara. Nasake furta Im..m soryy,dan Allah kayi hakuri..ni bada kai nake yi ba. Wuf ya mike tsaye kamar wanda zai gwada min mari,a tsorace na matsa gefe tun Kafin na gyara tsayuwa na fashe da kuka sai naji yana cewa Kin sanni kuwa?. Hawaye ne na suka fara saukowa kafin na girgiza kai. A hatsale yace words!!! Yana mai dada firgita ni da sautin Buga table din dinning din da tafin hannunsa daya yi gashi tsaban karfin daya sa saida dishes duka suka canza Ma zauna. I mentally killed myself dan haka a firgice na amsa shi da 'e",kuka na farayi mai ban tausayi shikuma baice uffan ba ya matso ta gaba na yana bina da wasu mugayen kallo. Sai da yyi bitting lips dinsa kafin nan Yace na far wasa dake ko? yarinya baki sanni ba I bet inkin sanni bazaki yi wasa dani ba. Nama kasa amsa shi"..don a lokacin hawaye sun gama wanke min fuska Tsoron yanayin sa tuni yasa sai na zuba gwiwa ta a gabansa kamar zan lashe kafar sa. Im sorryyyy...bana karawa Ke wace ce da zanyi tambaya bazaki amsa ni ba? Who the hell did you think u are. Ya daka min wata shafaffiyar tsawa mai tafe da aji A sukurkuce nace Im no one sir ....wallhy ni ba kowa bace kayi hakuri dan Allah. Ban taba jin yayi tsaki ba sai yau Ya dan dago kai kansa kasa ya dube ni yace Banga alaman kinsa me kike yi nai ba inda kuwa kin sani bakin ki bazai barki ki furta min wayancan kalaman akan fuskata ba. Ni dai kuka kawai nakeyi sabida fushin nasa gaba daya ya rudamin ciki da tsoro. Yace ure very dumb and stupid as well,and for that zan iya korar ki agidan nan kuma babu wani mahalukin da zai sanda ke har abada. Cikin kukan na dago ma kalle shi eye to eye,i know i cant loose this job so i guickly manage to say kayi hakuri... "What did you say...?anan Na daga murya dan a karo na farko da naji ya maimaita min tambaya kenan...ki maimaita abun da kika fada min.. Sai naga ya jawo dining chair ya zauna yana facing dina da wata irin bakar fuskan bacin rai. Tuni na dada zubewa kan kafarsa nace dan Allah kayi hakuri...kar ka kore ni. Yace hakuri ko?.. Im giving you 2scndz say it or u will leave forever. Yadda naga ya sha kunu nasan komai ma zai iya faruwa,.. Chak wajen ya dauki shiru bakajin sautin komai sai na shessheka ta. Tunowa da yace 2seconds,sai na lumshe ido na...dai dai zai mike tsaye kenan nayi saurin furta kalaman cewa' "Sai mutum yana zaune waje guda kullum sai ciye ciye kamar mata mai karamar ciki" Cikin matsanin cin kukan tsoro maganan ya fita abaki na,shikuwa baice ba ina ganin sa ya mike tsaye slightly yana duban agogon sa.. Tunanin abunda zai biyo baya ya hana zuciya ta sakat,i cursed the devil daya sa ni na furta wannan kalami... Toh yau inya koreni ina zanje? Gashi Na samu an dan rufa min asiri,ci sha sutura ga karatu.. sam bana son na rabu da wannan dama..kuka na cika gaba da mashi jikina duk
Chapter 22 · 0% Book details