← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 173

Sashe 84

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rasa shi da kishin sa shi yake saurin danneta Most times sai taga kamar ma babu amfanin soyayya ko auren da ke tsakanin ta da khaldun amma har yau ta kasa bari zuciyar ta ya cika furtawa mata hakan bare kuma ta kai maganan gaba Sosai sonshi yayi nisa acikin ranta har ya zame mata numfashi da abinci ma ruhin ta Washe garin yau bata jin daidai ajikin ta, amma sai ta daure ta fito dan su hadu da junnut din ta..hira kadan sukayi Junnut tace dana ga kwana biyu baki fito ba sai nayi tunanin na barki ki huta kawai Most time bahi sai dai tayi murmushi Dan inta kalle junnut bata iya daurewa ...sai taga ko magana mai tsayi bata cika son yi da ita,..gaba daya ta dawo wata shiru shiru komai tana yi ne tana dan jan baya akai ita kuwa junnut sai rawan kai take xuba mata surutai Ita kuwa bahiyya A duk zumudin sake haduwa da aminiyar ta datayi bata kawo cewa cikin sauki zataji komai ya fita mata akai har haka ba.. Domin kuwa iya daurewa da nazari tanayi amma har yanxu bata gane kan komai ba sai ma dada rudewa da tunanin su yake sa takeyi Bangaren khaldun kuwa duk yana sa idon sa akanta a boye amma bata san da haka ba Aranshi Yakanji ya takura ma rayuwar ta akan junnut tunda yaga kishi na damun ta sosai.. amma idan ya kalle yanayin tarin hadarin son data ke masa a kwayar idanun ta sai yaji gaba daya jikin shi yayi sanyi da al'amarin..game da subaya da sadat yasan tayi ma zuciyar shi laifi..but he stil respect that kowani dan adam yana da ra'ayin shi akan wanda zaiso da wanda bazai so ba Yana matukar kaunar ta yar hanzu....He hate those tears ...he feel that bazai iya cigaba da dauriyar ganin ta ahaka ba duk dama laifin datayi ma zuciyan san is still unforgivable. And Besides ya tsani raini,kuma Baijin zai iya cigaba da sai insa da ita bare ya gaya mata sirrin zuciyar sa Dan a kwana biyun ya lura yaga cewa gaba daya mood din ta ba adaida yake ba Hakan ya dada sawa yayi watsi da tsabgar ta bata ma ganin shi sosai a hidima gidan amma shi yana lura da ita sosai Kaamil da junnut din dai suke kokarin debe mata kewa duk dama kwata kwata yanzu mind din ta baya wajen su duka Ita ayanzu Tafi tunanin yadda zata fuskance al'amarin,shin zata daure ta gaya ma junnut komai ne koko zata nemi mafita ta wani wajen. Akan hakan ma ta kira dija yafi sau agirga amma ta kasa gaya mata asalin meke damun ta,gashi har yau subaya taki daukar wayar ta bare suyi magana,kuma duk sanda suka hadu da junut har ta kawo mata maganan khaldun din ta toh bata iya yin bacci mai dadi Wani bin ta dinga kuka kenan A Haka rayuwar ta kasance mata na har kusan sati biyu sannan ta fara jin sassauci aranta musamamman data gane cewa ayanzu bata da wani madogara face ta bar ma Allah komai. Idan tayi wani tunani sai taga kamar bazata iya zuba ido taga komai na tafiya a lullube ba,duk dama yanzu kam junnut ta cike mata brain da kare rayi akan soyayyar su da khal But tunda ta dan aje hankalin ta waje guda ta soma lura da banbancin lafuzan junnut da na kaamil akan abun sosai sai ta fara gane cewa kamar abun duk daya ne babu wani banbanci. . dada nitsuwar datayi sosai yasa ta gane cewa wasu zantukan junnut din duka karya ne Hakan ya fara bata karfin gwiwa har ta dena jin karfin cutarwan lafuzan ta a zuciyar ta kusan kowani lokaci Gashi ta gama lura ayanzu kamar rayuwar su ya dada banbanta,dan babu yadda batayi da junnut ta dena saka guntayen kaya tana yawo agidan ba amma haka sam taki.. Ita tunda khal ya sa tayi islamiya a london ta gane cewa ko wata mace a duniya kamar sarauniya ce,yaanzu ita dakanta ma bata son cika barin jikin ta abude haka kawai... Junnut Takan dai ce mata bahiyyya ke kam bazaki taba wayewa ba,tunda kika zo gidan kike lullebe kanki kamar wata kwai...bazaki sa kaya kisha iska ba?wasu designers din are terrible Design dinsu is alwys revealing amma dan dai tasan su din ta saka bata damuwa da yanayin tsarin su Shikuwa kaaamil yanayin bambancin tarbiyan su yana daya daga cikin abunda yake sa shi yake jin bahiyya na burge sa sosai. Ya lura duk iya surutun junnut da tsiyar d zatayi ma bahiyya,bahi taki sam ta biye mata akan irin sabbin tsarin rayuwar da ta debo makanta. Ana cikin haka washe gari da safe bahi ta farka da niyyar zata kai ziyara ma dija dan kuwa tunda ta karbe adress din bata bude ba sai yau Sanye take da hot pink nitie ta sake suman kanta duka sun zubo mata a baya ganin safiya yayi yawa ba lallai akawo mata abincin akan lokaci ba yasa ta shiga private kitchen dinshi ta shiga dora indomie Wani irin hadin alfarma takeyi ma indomie yana ta zuba qamshi an shake shi da ingredient kala kala tamkar ba ciki za'a kaishi ba Tanayi ne tana tunanin masoyin ta,musamman take so ace yaci ko da zata ji dadi aranta for once Dan haka Bayan ta kammala tayi serving a plate sai ta gangaro tabiyo ta kofar dakinsa,tafi minti biyar a kofar dakin batayi knocking ba kuma bata ce uffan ba.. Har Fargaba yasa taji ta juya kawai ta bar wajen,one step ta kara sai taji kyat an bude kofar dakin daga bayan ta Wani gafff taji kirjin ta ya amsa,a dan sadade ta juyo ta gama daukawa shi zata gani kawai sai suka hade ido da junnut,... Saurin dakewa tayi ta tsaya...She cant hide the remorseful look dan ko murmushi ta kasa mayar mata,ita kuwa junnut sanda ta gama kare mata kallo sannan tace bahi?me kike yi anan haka..tayi mata maganan ne tana kallon dresing din ta Irin kofar dakin husban to be dina ne kike zuwa mashi da hot nity? Junnut Batayi tsammani ba sai taji bahi ta mayar mata da irin tambayar,tana cewa ke me yakawo ki nan din,im suprised..naga baki tashi da sassafe sai 10 ko... Tace ohhhhh dear,bari kawai khal ne fa..kinga wai miji zaiyi tafiya shine nazo muyi ban kwana kinga ma har ya tafi ya barni a dakin ban sani ba... Wabi shiru Bahi tayi dan bata san sanda ta daure fuskan ta ba,tana jin duk surutun junnut din amma bata sake cewa uffan ba Imagining takeyi cewa ita da suke shashi daya tayi kwana biyu kenan bata ganin sa amma sai yau junnut ne zata gaya mata cewa yayi tafiya? And what is chocking her up bai wuce cewa da junnut tayi tazo wajen sa har cikin dakin nasa ba. Ita sam bata ji dadin haka ba,duk dama bata taba ganin junnut a site din ba yau kishi ya sataji kamar dama idan tana daki junnut din takan shigo wajen sa ma bata sani ba. Wucewa kawai tayi ta nemi waje ta zauna cikin danne zuciya ta bude abincin ta fara ci a tsanake kamar bata damu ba,but Tsaban bata jin dai dai ko tayin abincin bata mata junnut din ne tagaji ta sa hannu suka karasa ci tare.. Da ta dan kawo hirar iyayen sun ne ma bahi ta sake nata fuska ta sa baki,.junnut ke cewa ai abincin bahin har yau babu maraban shi da na mahaifiyar ta... Bayan sun gama cin indomien,wayar junnut tayi kara sai ta fita tayi excusing dinta Daga nan wanka ta fada ta yi alwala tayi karatun qurani haka kawai dan ta rage zafin kishib datake ji aranta game da kawar ta wanda bata san da shi ba Wani bin takan rasa gane dalilin daya sa ta kwallafa gayen da bai damu da ita ba .. Tasan dai Allah yana jin kukan ta Amma rashin samun sassauci akan son data ke mashi yasa ta dadajin ta bar ma Allah komai Dan kadan ta tattale fuskan ta da make up,ta shafa turare marar karfi Riga da skirt tasa na plain ember sai ta dora kakkauran bakar kimono jacket ta rufe sumar kanta gaba daya da veil shima baki... Fitowar ta ke da wiya suja hade da kaamil,waya yake yi amma daya ganta sai ya dakata ya iso har inda take yana yaba dresing dinta Takan ji kunyarshi sosai duk dama most times dan yasa ta magana yake damun ta he has a great sense of humor ..ya iya barkwanci da salon sace zuciyar mata Ita kam bata jin komai akansa,ta kan dauka dai khal shine nadaban acikin yan uwanshi,subaya da kaamil duk taga basu da daure fuska Sai da suka zauna Tace masa ina junnut take? Sai yace mata tana daki tana shiryawa kinsan kawarta zata kawo mata ziyara Tace hilda? Yace ehh...thank god kinsan ta ai dana baki labarin ta bata da maraba da kawar ki .. Sa tayi murmushi batace komai ba... Yana ta kallon ta...chan yace mata yaushe zamuje...tace ina? Yace waje...i want to take you out....ko kin fiso kita zama a gida..gwara mu muna ganin mutane am sure babu ko irin maids din nan a shashen bro..aint u bored? A hankali Ta girgiza masa kai tace no am ok....cikin gwalo ido ya taso zaiyi magana to karar takalmin junnut ya dakatar da su. Duka suka maida kallon su kanta sai langwasa takeyi tasha white dolce and gabana suit ya mata kyau bana wasa ba Ita kanta bahi bata san ko kallon kishi tayi mata kona jin takaicin irin wayewar junnut din ba ...right now she dosnt even look like a muslim girl. Tace me kuke fada baku jira ni ba? Kaaamil ya tabe baki.. .yace yawwa kizo kisa mun baki ko hajiya kawar ki zata amince muje mu sha iska. Zama junnut tayi tna kallon bahiyyar,cikin raha tace hajiya bahi... Bahi Tasan da lullubin ta take yi Sai sukayi Dariya...cikin shagwabben yanayi tace junnut ni fa ki kyale ni Wani dariya junnut din tayi tace nikam na shiga uku,kay kaga tun ban yi korafi ba harta gane me zance..kaga dai bahiiya sam taki ta dena shake jikin ta
Chapter 84 · 0% Book details