← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 173

Sashe 21

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jin me zanje agaba ba ta kalle gurds din cikin masifa tace what is the problem?meyasa yake neman ta..are you sure shiya aiko la Ko dai kunga kyakyawar mace zaku fara irin bazan halayen kun nan to wannan dai ba yar aiki bace. Kanshi a kasa Yace Kiyi hakuri Nanah A ba haka bane,Ai ta bar mopping duck ne abakin kofar dakin khaldun shi kuma yafito yana sauri zai fito ya karbe wani set din kayan sawa dayace na kawo ..tsantsi ya debe shi saura kadan ya zame kasa ya fadi.. A cewar gurds badon yayi saurin tare shi ba daya buga kansa akasa Salati nana A tayi tana toshe baki cikin mamaki tana kallo na,nikuwa duk na birkice ina taro hawaye masu ban tausauyi,vike da samuwa Tace ma gurds where is he now,baiji ciwo bako? Gurds yace yanzu dai yana daki dan har ya buga kafar sa he looks ok amma da alaman kafan tana masa zugi, he has cancel all meetings for today shine yace na kira ta. Ji nayi jini ya dauke a jiki na,A Kasa na sulale kamar mai shirin kurma ihu kirji na dukan tara tara.. Duk da na naga alaman tausayawa a fuskan nanah A amma bai hanata dakewa tayi min fada ba. Tace ai lin kyauta Toh Kije maza ki same shi..ta nuna min hanya ranta adan bace. A sadade na mike ina kuka ina tahowa site dinsa 10 minute ina knocking kafin ya bani izini na shigo Gaba daya jiki na yayi lagwas sai sum sum nakeyi,sai da na taho face to face dashi ma kfin nasake tsinkayo kamannin sa da soldiern. Yana zaune Ya juya kansa kafafun sa amike akan tebur yana tattabawa Daga nan Ban iya sake kallon sa ba kuma ko rusunawan ban samu karfin gwiwar yi ba na dai tsaya ina murde murde da yatsun hannu na. Wani shiru ne ya ratsa wajen. Yana sane da abunda nake amma ko kallo na baiyi ba,Sai chan dai yayi magana chan Kasan makoshi naji yanacewa i believe you know what you did.. Na sauke kaina a sanyaye A sulale na taho na yi kneeling kusa dashi, hawaye na bin kunci na dan Ban san dawani kalma zan fara bashi hakuri ba ga wani mummunn tsoron sa da ya shake min wuya. Hey Am talking to u..ya dan daka min tsawa A firgice na tashi na matsa baya,i mentally shouted my throat out tsaban kuka. Sai ya dauke kafan nasa daya aje kan tebur ya mayar kasa ya kalle ni yana mai daga min girar sa alaman jiran amsa wanda ahalin yanzu kwata kwata bani da shi abaki na. Da kyar na dago da mumunnan rawan murya nace Dan Allah kayi hakuri!!! Yace hakuri?? Kinsan me kikayi min kuwa? Are you mad, kashe ni zakiyi ko?... Nace Nooo nooo what the hell are you thinking. .., Kin san suwaye suke jirana?...and u just let me cancel a multi billion dolla meeting kuma kike cemin nayi hakuri? sorry Is all what you gat huhn? Abunda ya tsanan shi na ke iyayi wato girgiza masa kai,khaldun ya tsani yayi tambaya abashi amsa da gyada kai ko girgiza kai Dan haka nw ma ranshi ya dada baci dani Cikin wata birkitaccen tsawa yace Me kika dauki kanki..?u ruined my uniforms, did you know that Ko duka zuri'ar ku aka hada bazaku iya siyan kaya na da kika bata ba? Wai daga wani kauye aka dauko ki? I can see that Baki da manners Don't you have a mum,ko bata koya miki aikata komai a nitse ba tare da kin bata shi bane. She tot you how to ruing everything right? cikin bambami ya juya kansa baiko damu da kukan danakeyi ba Nikuwa Sabida sunan mahaifiyata daya kira cikin maganan nashi yasa radadin azaban kuka ya dadu a kirji na Silly brat,sai na koya miki hankali da kanki zaki ce kin sawwake aikin nan naki, ure just pestering me baki da wani amfanin komai.. idanun sa ya dada tsurawa akaina kamar zaice wani abu sani naji yace very Stupid girl and u better say thank you . Murya na rawa Thanks. Thanks what Na dade fashewa cikin kukan nace thank you sir. Share wannan banzan hawayen naki da ba amfana ta da komai zasuyi ba....right now,ko na miki da kaina. Da sauri na share ina kukan zuciya,jiki na duk rawa yake ban iya dago idanuna na kalle shi ba, don duk sanda mutum zai zage ni bana so ko acikin wasa ya hada da sunan iyaye na I know im just an orpharn amma nasan yadda iyaye na suka tarbiyantar dani Wayar sa ya dauka yayi kira inaji ya dada masife guards dinsa. Sai da ya gama tsaf sannan yace nayi waje na bashi waje kar ya tatttaka ni. Nayi sauri nafice masa adakin sa Bansan me xanyi ba kuma dan haka na shiga daki na fada akan gado na fashe da kukan tsoro hr bacci ya dauke ni Na tashi da murdawan ciki dan haka na fahimci cewa bana sallah amma dana je wanka sai naga jini bai sauko dayawa ba so ban saka wani pad ba Zama nayi naci abinci,tsoro nake ji sosai musaman ta inda zan fara sake zuwa dakin sa yin wani abu. Haka dai na daure na shiga kitchen da daddaren zan girka masa dinner. Nanah A ne ta shigo ta dan min fada ta kuma bani hakuri tana ce min komai zai wuce kuma zan saba dashi. Lura da ina dingishi yasa ta bani wani ointment akan idan nagama kafin nayi bacci sai na shafa. Ina jera mashi abinci sai ga nana tace a daki zaki kai mashi.. I am sure kafar san ne ke damun sa har yanzu Nima gashi ciki na sosai yake murdawa yana min kananun ciwo Da abincin a tray na isa kofar dakin sa nayi knocking just few minutes ya bani izini sai na shigo A tsaye na tarda shi Muna hada ido na sauke kaina kasa. Har na aje abincin baice min komai ba,sai ya juya ya shiga bathrum nikuma na rusuna na shiga serving din kowanne kalar abinci a plate Ko kaiwa hannu sau uku banyi ba jiki na ya hau rawa,serving poon dakansa ya sace ya fadi Wani mugun murdawan ciki take ya dunkule ni da kyar na mike na zauna akan lallausan farar kujeran sa ina juyayi Nishi nake saukewa slowly har na dan nitsu,daga nan cikin minti biyar naji saukowar dumi mai yawa ta cikin pants dina Abu kamar wasa na dan janye na duba,jinin period din ne ya fara zuba har gashi yayi staining masa kan cushion dinsa sosai. Wani mugun faduwar gaba naji,oh Allah na wannan mutumin zaice da shi na tashi yau,after runing his shirt da safe yanzu jini na ya zuba masa akan cushion? What shud i do now,sai na mike tsaye a rude,hasbiyallah its showing jinin ya nuna clearly,kafin na ce zan share har nayi waje Sai Kyat naji alaman bude kofar sa i have no choice dan haka da sauri na koma a zauna akan jini Ko kallo na sau biyu baiyi ba,amma daga yadda yake miko min harara nasan banyi dai dai ba dana zauna masa akan cushion. Nima cijewa nayi na basar,duk hnkali na baijiki na,zafin ciwon cikin ma na dena kulawa Tunanin yadda zan masa bayani nakeyi,duk na rikita kaina. . Yana daga plates din zai fara ci, na fara kuka...sai naga ya aje spoon dinsa ya kalle ni. Dan Allah kayi hakuri. Tsaban rawan da jiki na keyi sai abun ya bashi mamaki Ikon Allah What is this nonsense? Will you Get out..ya kafe ni da ido Sai na dena kukan Nayi masa shiru na rike ciki na Ina jin jinin na dada bulbula,hawaye na suka fara razana shi I think saboda hakan ne bai sake min magana ba ya tsaya dai yana lura da motsi na gashi na kime sam sam bana so na tashi bare yaga jini Cikin kankanin lokaci ya fahinci ciki na ne matsala Sai naga ya aje plates din ya tashi tsaye. Get up...dah inda yake ya furta Girgiza kai na nayi nace dan Allah kayi hakuri U can't get up? Na gyada kai cikin sabon kuka nace yes sir am soryy sir Ciki na kemin ciwo. Sai yayi shiruuu yana ta kallo na ina kuka,it took him a while kafin ya gane asalin abunda nake ciki Komawa bakin gadon sa yayi ya zauna ya na latsa waya. In not less than 10minutes muna zaune,sai mukaji knocking abakin door,toh da kansa Naga ya tashi ya bude nidai banga wanda yazo ba har ya juyo, Batare da ya kalle ni ba ya aje min wani park akusa dani,sai ya juya ya fita ya barni adakin nasa. Kallo kawai nabi closed door din kafin na daure na bude park din Wanda sanitary pad ne aciki da white cotton pants,har cikin raina naji kunyar hakan but i know have to do quick tun kafin ya dawo na shiga uku. Da kyar na tattara komai na goge wajen na shiga bathrum dinsa na wanke jiki na na saka sabun pant da pad din,bansan ya zanyi ba sai na daura towel dinsa akan kayan jiki na na fito'.. He is still not around bai dawo ba hakan ya bani dama na shige da gudu na koma daki na Kayan kawai na sauya na kwanta dan kuwa sosai ciki na ya balle da azababben ciwon har ji nake kamar mutuwa zanyi. After 1hr,idanuna sunyo luiii nayi lagwas kamar an tsoma akuya a ruwan sanyi Bansan anshigo ba ma bare na gane ko waye ne,ji nayi an dan taba goshi na alaman ana feeling tempureture na wni nishi na sake sai naji mutum ya zauna agefe dani! Its khaldun,i can feel his scent and warmth dan haka naki na bude ido na kalle shi da kyau Kallo na yake yi his face isnt showing any emotion. Bansan ko ya gane halin danake ciki bane ko bai gane ba all i know is har nayi bacci yana zaune awajen yana duba ni,bansan kuma yaushe ya fita ba. #follow SURAYYAHMS COMENTS And SHARE WITH OTHERS AHUMAGGAH _A nigerian historical fiction_ *WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
Chapter 21 · 0% Book details