← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 173

Sashe 50

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

din Yace Bahiyya.. Tana juyawa zata amsa sai yace i kept u waiting ko? sorry.. Ta dan kauda idanun ta,. .Babu komai....its ok ta sunkuyar da kai,wani direct look yake mata batare daya lura da komai ba,ita kuma kanta na kasa kamar wanda hankalin ta na kan book din ne.. Jawo book din yayi shima ya bude,five minutes scrolls ya dube ta ba yabo ba fallasa yace can you read stories?. Tace yes..cikin sanyin sautin jin kunyan shi.. Hawa gadon yayi mai gaba daya,ayayin data mike ta zauna sabida faduwan da gaban ta yake yi. Read it for me...ya mika mata book din yana gyara kwanciyar sa just beside her Babu musu itama ta karba Dan shiru ne ya ratsa wajen ta kafa book din har ido,sai ta rasa wanne labarin zata karanta mashi a halin yanzu da presence dinsa yake birkita ta Yana kwance agaban ta tana zaune agefen sa with the book still covering her face tasan duk dama ba kallon shi take ba amma da alaman jiran ta yake ta fara Which story will u like!..she manage to say in a very calm voice tana dan satan kallon shi ta kasan book din da wayo. A bazata ya sa hannu ya sauke book din sai ta runtse ido da sauri ayayin da ta sake mashi gaba daya cikin jin kunya sosai ,.murmushi kawai yayi yace "read story 7... bai bata book din ba ya rike,tasan jira yake ta karba a hannun sa dakanta Amma sai ta kasa Murya na dan Rawa ta langwame masa wuya so cute tace pls can i have it,...shagwaban ta sosai ya dauke masa hankali,sai ya dada gyara zaman pillown yadda zai fuskance ta da kyau idanun shi still kafin nan ya mika mata book din. Ba wani bata lokaci ta bude story 7,its a short love story wanda bai wuce rabin shafi ba,..sweet and slow ta fara karantawa wajen ya yanke shiru,tun tana kauce ma pircieng looks dinsa har ta dan basar ta saje kamar bata san yanayi ba. "Even after her death Sultan neva forgets his maid turn lover, asiyah". karshen labarin ya karashe da wannan kalman,a hankali ta furta....the end Wani ajiyan zuciyn Ya sauke kamar da gaske yaji duk abunda tace,menene sunan labarin ma? Tace"he is royalty. "Dan karamin kwafa yayi,yace and is that all?masoiyar sa ta mutu sai labari ya kare ko,a bazata tayi murmushi Ta dan girgiza kai sideways,tace ai ta mutu ne amma har yau suna tare....sai ya gyara zama ..ta dauki book din ta sake bude page seven,throug this writen poem soyayyar su yake numfashi . ..hannu yasa ya karba book din yace let me see the poem..sai ta bashi feeling more comfortable ta dada gyara zaman ta daf da kan pillown sa. Tsaff ya karance poem din aransa ,cikin zuciyar sa yana masa dadi dan ji yake kamar abubuwan dayake sha'awar furta mata kenan amma bazai taba iyawa ba,..after 10minutes of staring ya aje book din akan cinyar ta..'cikin basarwa yace read it for me ni bangane ba..ba wani tantama ta dauka ta fara bin words din.. Its actually from a song,amma dan author ya gyara labarin sa sai yace masoyan ne suka kirkiro remix din 2 stanzas.. Slowly ta fara from the moment that we met,any moment that i get,all i wanna do is dream about you....When you look into my eyes,i just hope u realised,i can neva live alone witout you..... Dayan layin kuma "i will neva forget you,u will always be by my side,from the day that i met you i know that i wll love you till the day i die,and i wll neva want much more,in my heart i will alwys be sure.. Jin yayi shiru sosai yana jin ta,sai kirjin ta ya shiga bugawa Sai ta danyi shiru itama,ko tunanin meyake oho,sai ya dan motsa jikin shi akasale ya wani lumshe ido yana lumar dakansa slowly cikin pillow..,da wani irin muryan mai kamar mai jin bacci yace 'banaji' is that all,ta dan girgiza kai adan rude da sauri ta maida kanta kan book din,ta karasa few words din daya rage da dan rawan murya Tana cewa ,i will neva forget,u wll alwys be by my sad till the day i die.. Finish....ta daure ta fada tana aje book din akan side drawer cikin sauke boyayyan ajiyan zuciya. Tana juyuwa taci karo da golden eyes dinsa dar akan nata,thank you,ya furta a kasale..sai ta sunkuyar dakai kasa bata ce komai ba,can i ask? Ya tambaye ta... cike da mamakin sa ta dago cikin sanyin murya tace yes sure.. Why must love die?.... I mean meyasa sultan zai bari maid turn lover dinsa ta mutu,What sort of love is that? Dan sauke ajiyan zuciya tayi,cikin sanyin nazari tace Ba bari yayi ba,"she is just scared.. Cikin dauriya ta kalli idanun shi tace... Scared of broken relationships.... Shima Sai ya danyi shiru,kamar mai nazari kasan makoshi ya furta but one must not secrifice love.. "Tayi murmushi, Awajen wanda yasan halacci amanan yan uwanta ka ba abu bane mai saukin karyawa, Asiya Tana son shi amma she choose peace and relationship Bai motsa ba dan Murmushin ma kufce masa yayi sai ya tabe baki yayi shiru for 2seconds so you do belive in that?u believe in secrifice? Ta gyada mashi kai tace yes..its a good thing. So "love is a bad thing".Ya furta yana dan kokarin kau da kansa Tace noo,ni bance haka ba. Bai dai amsa ta ba ya fara shirin sauka akan gadon mai gaba daya sai ta bishi da wani irin kallo. Misali,Idan ace kai ne sultan zaka ga laifin ta dan tayi haka?What wll you do? Data furta mashi hakan shikansa Ya dan sha mamakin courage din ta,sai ya dan yi kwafa yana dan kallon ta daga tsaye.. "I don't belive in relationships,sabida babu wani kwanciyar hankali da zaki samu duniyan nan,I wont kill myself for any secrifice. Mood din Daya furta hakan sanda taji kanta ya wani sara Bata iya cewa komai ba tayi murmushin karfin hali.... Ruwan gora ya juya ya dauko yadan kurba,gyara zaman ta tayi tace but ,The poem is actully nice"when it says from the day that i met you i know i will love till the day i die....ai kenan so bazai mutu ba. Wani makallen kallo ya bita da shi" yace hmmm ur tots.? abunda ya bata poem din shine"i will neva forget you" If only baisa wannan kalman ba i will accept ur own point of view,"those who secrifice only to die in love are loosers... go to bed now..yana kallon tan ya bata comand din haka... Sai tayi murmushi Babu bata lokaci ta haura kan gadon tayi lumui kamar wata kyanwa,... zama yayi yana shan ruwan for some minutes sannan ya tashi ya rage wutar dakin,akan cushion ya mike ya kwanta ya lumshe idanun sa. Almost 1hr suna shiru,kowa da abunda ke yawo aransa barin ma ita ta datake faman juye juye Dukan su idanun su biyu suna faman pretending da kyar tayi bacci,. Jim kadan Shima Wani shegen baccin ne yayi awon gaba da shi,kowani awa guda baiyi ba motsin ta ya daga shi,bude idanun sa kawai yayi bai taso ba amma duk yana jin ta She was seriously shivering,alaman wani mumunan mafarki takeyi.. sai ya kira sunan ta yaji shiru bata amsa ba,tashi yai ya iso kanta yana duban yanayin tan gashi dai idanun ta a kulle amma duk jikin ta rawa yake alaman tsorata ta akeyi Acikin kwakwalta tana ta kokuwar fincikewa ko zata dawo dai dai ta kira masa sunan sadaat,amma wani abu mai nauyi ya riga ya toshe mata baki,ga wani tsinannen bugu da ake yi ma kanta da sanda kwata kwata bata gane meke faruwa da ita ba... Agefen ta ya Zauna da sauri tare da dora hannun shi akan goshin ta da wuyan ta yana tattabawa,maimakon ta furta sadat din datake gani cikin wani irin firgitaccen yanayi ta furta ...Abbuhhh..Abbuh... Addua ya shiga tofa mata hakan ya dan dada hasassa kwalwanta dawowa sarari,jikin ta tuni yayi lagwas sam bata jin wani karfi,tanaji yadda heavy hands dinsa ya tattare ta zuwa kirjin sa Are you ok? Ya furta yana dora ta akan kafadun sa whith a very calm hug.. Gajiyayun ajiyan zuciya da Qamshin jikin sa dake toshe mata iska su suka tada ta daga baccin sosai har ta dawo cikin hankalin ta,tsaban tsoron daya rufe ta bata ma san sanda taji ta dada shigewa jikin sa ta dada kankame sa ba. Shima Riko ta yayi gam kamar wanda zaa kwace masa ita,Wani sasaanyar muryan lallashi yasa yana dan shafa suman kanta daya yarfu hannun sa kamar wanda ya samu baby girl "Shuhhhhh,...go to bed baby,sleep now.. Da taji yace mata babyn nan ma Wani sabon shaukin shagwaba da narkewa takeji amma tsoron rudadden mafarkin data yi yanzu ya hana ta sakat bata sake shi ba sanda ya mikar da ita kan pilow ya riko hannun ta zuwa nashi yana bin inuwar closed eyes dinta da kallin yana murza fingers dinta slow..wani siririn kukan shagwaba tafara masa mai sanyin shiga rai duk saida yaji ya rude,da kamar bazaice komai ba,amma ya daure,muryan sa cike da damuwa yace Bahiyya Whats going on..tun kafin ya dora kalma Cikin rudewar yanayi tana sauke ajiyan zuciya mai ban tausayi Tace,Abbu na.. im just an opharn ...Abbuh... i really miss himm.. Idon ta ta rife tayi tsamm kamar bat san metake furtawa ba Cike da damuwa Yace kinyi mafarkin sa ne? Bata wani amsa ba ta fashe masa da kuka jikin ta atake ya dau karkawa Dada jawota ta yayi jikin sa Haka kawai yaji ta daga masa sense sosai sai ya tallafota ya aje kanta akan cinyarsa ya shiga lallabata yana mata nasiha da sanyin muryan sa. '...Comon its just a dream kar ki daga hankalin ki,Addua zakiyi masa ba kuka ba,Everyone is an opharn too,a duniya ba a maraya sai rago,so stop putting up with all this kiyi abunda ke gaban ki. Are we clear... Cikin sheshhekan da bata san dashi ba ta gyada kai tana jin yadda hannun shi yake dan shafa suman kanta yana aikin lallabata.. A haka har sai da tayi shiru wani bacci mai dadi ne ya dauke ta akan kafarsan ma
Chapter 50 · 0% Book details