← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 173

Sashe 14

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ _Bismillahirrahmanirrahim_ -Coincedence A daskare na tsaya chak kamar wacce akayi freezing dan ko iya juyowa banyi ba. and y are u in my room?Ya sake fada muryan sa emotionless Wani runtse ido nayi for the moment ina sauraran bugun zuciya ta..ohhh ya ilahi"...his voice... shi kadai ma ya isa yi ma zuciyan mai sauraro hisabi.. kakkauran sautin muryan shin ya daki tsakar kwalkwar ta har yasa na saki siririn nunfashi, ji nake tamkar kirjina zai fado kasa tsaban tsanan ta bugu,..not withstanding sai na daure na amsa cikin sanyin murya nace... um..umm dama damm..a ..nice mai aikin ka,mai kulawa dakai.. Wani Shiru naji yayi bai amsa ni ba Banji mamakin hakan ba sabida yadda nayi maganan kasa kasa cikin tsoro da fargaba nasan ba lallai bane yaji. Shud i just turn around and look at him?na tambaye kaina anma sai naga nakasa yin hakan... ayau ko da ace ban fara mallakar hankalin kaina ba dole ne na fahimci cewa wannan gayen ba kalar masu maimaita magana bane.dan haka Bani da wata mafita face na maimaita ansar tambayar shi A take na kuma taro confidence na dan bude baki nace"nice mai aikin ka mai kulawa da kai. Still naji yamin shiru, Nace im ur personal house help sir....sai nadan daga murya na kadan tunani hala baiya ji nane ashe ba haka bane. Hasali ma juya kanshi yayi yana tsime akan pillown sa yayi banza da maganan kamar da icce nake tare ba da mutum ba,"hmm ashe gwara ma da ban juyo na kalle shi ba sai na cigaba da tsayuwa ta.. Chan dai dana ga abun nasa so i started panicking, Gashi kafa na har zafi ya soma min tsaban tsayuwa waje guda nakai minti 10 ina maimaita abu guda azuciya ta,da kalmomi iri iri na ansa shi ko zanji yace wani abu Still yana shiru. "can nima nayi tsit still dai ban juyo na kalle shi ba,cikin tunani na nace Oh Allah,ko kashe ni zaiyi ne kam! Maybe is time to walk away...halan ranshi ne ya baci... Sai nayi yunkuri fast foward zan fita sai dai Ko daga kafata banyi ba naji ya daka min wata dakakkiyar tsawa wanda dirinta ta nane min kafata ta kuma daskarar da gangan jiki na, waje daya na tsaya sanda kunne na ya jiyo tambayar na daban dayayi min again' Meya kawo ki daki na? Lokacin da baki na ya furta tea tea tea dink...a na zo ajiyewa banma sani ba..My tongue was seriously sluttering har kalmomi suna neman kasa haduwa abaki na. Dan shiru yayi cahn naji yace did you know who i am?...!yana gama rufe bakin sa Immidietly na girgiza masa kai alaman ah'a Words!!! Yace yan mai daka min wata fusatacciyar tsawa Lokacin da baki na da kanshi ya furta amsar"ah'a,ban ma sani ba. Gaba daya sai naji na tsorata sai na rasa meyasa yake min masifa to ni menayi masa?ba shayi kawai na kawo ba? Ji nayi yace aikin ki ne kizo ki dame ni ina bacci? Na girgiza kai da sauri nakuma cewa ah'a da sanyin murya.. Yace kinzo kin tashe ni ina bacci baki ji ne ko baki gani?...kirji na dada bugu na girgiza kai na gefe da gefe na kuma cewa ayi hakuri. Tsimewa yayi,Bai kulani ba cikin makokwaransa yayi kwafa yace both i quess...toh daga yau kar na sake ganin mai kama dake a dakin nan dont you ever come into my room. Ever!!! ya dada jaddada min. Kaina akasa na amsa shi A tsorace ina kan jiran next action. Get lost!!! Comanding voice dinsa yayi wisphering chan kasan wuya kamar bada ni yake ba,aiko da uban sauri na fice adakin na koma kitchen rike da kirjina ina haki. A gurguje na shiga hada abubuwan dana shirya Koda na fito na aje masa breakfast din sa sai naga bai ko sauko ba ma bare yasa lokacin yaci. Haka naci tsayuwa akan abincin har nagaji,so i tot ko dan na bata masa rai ne bayason ma ya kalle fuska ta inayi ina dan komawa kitchen hoping to see him seated amma shiru har na kammala komai na dawo na dauki abincin na mayar kitchen. Ashe har yayi wanka ya shirya kansa ya fice ban ma lura ba. I was kind of pissed duk dama banda wani dalili,lokacin aikin na kaucewa na tattara komai a kitchen din na tsaftace shi tsaf kafin na fito ina sb tambaye tambaye har nagane ashe ma ya fita ne agidan baki daya. Yau a sace kamar wata munafuka na gyara mashi daki na wanke bayi,na kuma jera masa wankakkun kayan sa a closet... Ina kwance akan gado na,zuciya ta tana mugun sha'awar ganin ammuh adama amma kuma bansan ina zanje kai tsaye na same ta ba Ni kaina nasan ina muhallin da aka gina shi da dokoki da tsari Tsoro na kar naje na shiga inda bai dace ba nayi laifi. And I do not want to miss this chance,ko ba dan komai bama nakan tuno da mummunar rayuwar dana fito daga ciki dan sati biyu da suka shude Shin waye zai bani aiki awaje kamar haka?inacin mai kyau ina saka mai kyau ina bacci akan gado mai kyau..a rayuwa dai nasan na taimake mutane da dama amma babu wanda ya taba tunanin biyana ta wani fanni sai anan gidan. Speaking of secrifice,in na tuna da hakan kirji na ne ya kan buga,a take naji wani shauki mai karya zuciya ya shige ni ya min rawaya a kirji na Juyi nake faman yi ina juyayi cikin azaban radadin kewa da son in taurara zuciya ta Sam sam bana so na tuno da babbar aminiyata junnut bare ma na tuno da iyaye na wanda suka riga suka bar duniyan nan suka barni nikadai. Sai dai karban qaddara ga mumini ba kasawa ko gazawa wajen nuna soyayya bace,inka ganni wata rana zaka dauka bana tuna kowa aduniya nan,but deep inside me i know no one can eva replace my parents and my dear friend junnut. Wanda ayanzu na karbi qaddarar daya rabamu wanda kuma babu alaman zan iya ganin ko daya daga cikin su har abada,wannan shaukin ya sa sai na dena saka komai a raina ma game dasu ina dai fatan so na riki duniya ta fuskar da a duk inda suke bazan taba basu kunya. A Yau na yanke wa kaina hukuncin jajircewa wajen aiki na batare da na sa damuwar halin ogah na araina ba.. Tun safe da yamin maganan Ban sake ganin shi ba har sai da dare yayi a dinning dinshi wajen serving dinshi dinner. Riga da skirt royal orange mai tsafta da sanyin qamshi na saka dauri na simple babu hayaniya tsaye nayi a agefen shi na shiga serving dinshi in varieties Crispy fishrolls,offals pepper soup da tamarind juice dayan wamer din kuma tuwon shinkafa ne mai laushi da miyan eforiro yau ban jero abinci dayawa ba dan bana iya taba zubarwa kuma nagaji da neman masu cin ragowar. Ina serving dinshi tsaban fargaba jiki na har rawa yake amma duk da haka ban fasa gulman sa araina ba,hmmm yau naga abun mamaki So finally he decided to fully show me his face! kanshi ya dora akan chair din yadan jingine Babu karya gayen ya hadu,kai kalman haduwar ma is an understatement. Kamar yadda nayi harsashen kamannin dirin jikin sa da indian actor john Abraham Sai naga fuskan nasu kusan kwatance daya ne, aga nina ma yafi shi haduwa da hasken fata the guy is faultless and flawlesss. Sanye yake cikin wata kasaitaciyar collection na kananan kaya ta kamfanin dior hormes white shirt and a very soft black trosers. "Suman kanshi is silky black and shiny babu wani sanko ko cinkai,gashin sa acike take luff dai dai misali sannan babu maraban askin kansa dana world best foot baller wato cristiana ronaldo. Bakin shi dan dai dai,Daidaituwar shape din Karan hancin sa ya samo kyakywan diri ne daga Shatin kerarren Sajen sa wanda yabi cikakken giran shi masu dauke da dogayen eye lashes dinsa. Nasan hala bazan taba ganin murmushin shi ba sai dai Allah cikin ikon sa ya bayyana shatin lotsawar kyawawan twin dimples dake gefe da gefen kuncin sa, He loves keeping straight face ban taba ganin mutun mai son bata rai kamar wannan gayen ba Hannu na sai rawa yake a hankali amma bandamu ba haka na gama serving dinshi.! Ina gamawa nayi sauri zan Juya da niyyar basa waje sai naji yace na dawo na tsaya! Tun daga nan baice min uffan ba,ina kallon shi yana cin abincin a tsanake,well pampered yatsun Hannun shi da suka ji gyaran manicure su suka dauke min hankali he's goddam porschy sosai yaji wankan aji. Dan kadan yataba offal pepper soup yasha tamarind juice din ya aje spoon abunsa. Baice min uffan ba kuma bai tashi ba,wayar sa ya cigaba da latsawa yana kira ana kiran sa. Tsaban na gaji Baya na kamar zai karye amma hakan na daure na jira bai kuwa tashi barun wajen ba sai da ya wargaza min ka'idan lokacin aiki na. Da sauri na tattara dirty dishes din naje kitchen ina wankewa ina maganan zuci. This guy is kind of mean wallhy,wasu mutanen dai haka suke,shegen iya wulakanci da fi'ilin tsiya. '..Washe gari da safe hakan na tashi da niyyar cigaba da aiki na as usual abincin shi nafara dafawa duk dama nakasa motsawa sosai. Gaba daya tunanin Abubuwa dayawa sun cirke min zuciya,duba da yadda jiyan yace kar na sake shigar mai daki" Shin yanzu maganan wa zanbi? dokokin aikin da Jahan Aarah da ammu adama zan dauka na cigaba da aiki na koko na wannan mutumin da ko sunan shi ma ban sani ba? Wannan rudaddiyar muhawwara da zulumi yasa na dan ja lokaci banje dakin sa akan lokaci ba. Sai chan anjima dai na taro caurage na iso,Ko da nayi shahada na turo kofar sa a sadade na leka sai naga wayam babu shi akan gadon sa ...cikin mamaki na tsaya baki na abude. hmmm seriously I was surprise ai na dauka doka ne baya tashi akan gadon shi sai akan tsarin lokacin sa. I waited,haka nayi ta jiran tsammani dan naga ko zai shigo amma shiru har karfe
Chapter 14 · 0% Book details