← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 173

Sashe 110

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta furta,wani soyayya? Ya gwalo idanun sa dake kin buduwa da kansu Yace ahh baki son shi ne?nafa san kina son shi... Tace nidai bance ba,aifa shima cewa kawai yayi a aura masa ni bacewa yyi yana sona ba nima bance yamin ba.. Ya gwalo idun shi "So R u managing him?..tun kafin ta bada amsaa kaaamil ya fashe da dariya yana kallon ta...cikin salo ta tabe bakin ta kamar zata sake fuskan ta amma sai taki sam "ni dai wallhy bana jin wani soyayyar kawai dai an mana Aure..." Yace hey kifadena fada min haka..so nake kafin azo hidiman bikin nan naganki da little Aaban kina turowa.. Tayi saurin rufe fuska da tafin hannu, da dan zakin sautin murya tace mashi what?little who?tab di..ta turo baki Yana murmusawa Yace miye?..what is tab di..yanzu ke me kike so yamiki bayan kinsan ba laifin shi bane yayi fushin dake Ta sauke hannun da sauri ta harare shi.."...ba laifin shi ba?wato nice zan na yarda da shi nikuma bazai yarda dani ba kenan ko,he knows me more than anyone . ya rufe idanun shi daga yaji ance nayi abu sai ya fara min wulakanci... Ni wallhy na dena son nashi. ta langwame wuya a lalace tamkar daga zuciyar ta furucin ke fita tone din voice din ta cike da mita Dariya kawai kaaamil yakeyi yana mamakin ta, tsokanan ta ma ya shiga yi yana cewa karya kike wallhy kina son saood Ta bata ranta tana kawo masa reasons din ta bai dau abun serious ba,..duk dama yasan da gaske takeyi.. Ganin ta mike zata tafi ya tashi da sauri yace sister twinkle wai baki san wasa ba?To me kike so ayi masa dan ki huce..uwar gida, ran gida ina jinki sai yaya kenan? Tadan harare shi tace nidai kawai ka taimaka min na rama,ni wallhy sai na rama ..dan bana son yaga kamar bai cutar dani ba.. nima fa mutum ce ai inajin zafi araina. In ba huce ba bazan dena ganin shi da abun da yayi ta min ba Kaamil ya waro idanun shi yana kallon ta "Amma dai kinsan bada son ran shi bane ko? Tace eh..nima ai bada son raina bane Yace ok to me zan miki,tayi shiru can tace mashi ranar da mukaje abuja jahan tace mashi ya sake ni..but i know he wont..kawai dai zan nuna mashi bana son auren ne..so that he will learn how to value it.. And i want u to be my acomplice...ta dan kalle shi da gefen idanun ta silently ta furta hakan kamar wata munafuka Kaamil yaja cheeks din ta yana murmuushi yace ok..amma nidai kar amasa da tsauri ...kinsan bro akanki fa baida wani dauriya ...hararar sa tayi cos she dont realy belive that saood yanason ta..nidai kayi min alkwarin... yace promise duk abunda ake ciki ki gaya min.. Haka suka rabu ta koma site dinsu, junnut aranar gaba daya bata fito ba,tana kwance akan gadon ta bataci ba bata sha ba juyi take yi from one end to end tana jin tsananin kishi da zafin al'amarin. To bawanda ya sani har ta aike hilda wajen bokan su a india akan a duba mata kan maganan Inda halin raba auren a saukake tana bukatar ayi hakan da gaggawa Tuntuni take latsa wayar ta, kirar wayan hilda ta take amma bata dauka ba... Ayanzu ji take ko zata mutu ne bazata iya sharing saood da bahiyya ba,gashi tana son ta kam.. amma bata jin zata iya saukowa ta saurare ta akan sa'ood iya dannewa tayi amma zaman kishiya da kawartan har yanzu yaki kwanta mata arai. Wuraren 8:30 saood yatashi da kyar, ya shiga bayi yayi brush yayi wanka yayi alwala, yadau mai ya shafa sannan ya shirya cikin dogon black jeans da soft cotton t-shirt maroon bakaramin kyau kalar yamai ba,cikin nitsuwa ya shafa man gashin shi dake kara saka gashin kanshi kyalli sannan yadau turaren shi mai kama jiki ya fesa kafin yahau dadduma yay salla raka 'a biyu yana idarwa ya mike yana kallon agogo dan baida lokacin yin azkar din sosai, takalmin shi mai kyau ya zira sanan yadauwayar shi ya fito ya nufi inda ya shirya musu yin date din su A cahn sama ne a bene na karshe dake gidan,inda babu hayaniyar komai bare sautin maganan kowa. Bai bari kowa ya gansa ahakan ba,dan musamman sabida bahiyya yayi wannan shigar.. A sama chan inda ya shirya date din shiya fara isowa komai yayi ras dashi wajen shiru daga shi sai hasken watan Allah. ...Ya tura mata sakon text few minutes ta amsa da ok..shiru shiru bata zo ba kuma a kowani sako ya tura mata zatayi reply dan ma yasan ta gani,tun 9 yake Jiran ta shiru har 10.30 ya gauce bai ganta ba... Bai dai nuna wani alama na bacin rai a fuskansa ba still He called her,yayi ta kira har ya gaji bata daga ba.. Ya tashi ya tsaya yana waige waige chan ya sauke ajiyan zuciya cikin ransa Abun baimasa dadi ba.. ,cike da naci ya jira har 11oclk daya ga ya cika sai yaji baxai iya ba sai ya sauko yana ta jin haushin abun aransa,adaidai zai shige site din san suka gamu da mahaifiyar sa maids guda biyu suna binta da trays wanda baisan meye aciki ba.. Ya dan rusuna da sauri.. daga irin kallon data ke mashi ma kawai yasan ta yaba da kwalliyar nashi.. Yace fatan lpya naganki haka ? ta amsa mashi da ka Tana mai dan daga idanun ta akanshi,ita dai har ila yau tana fushi da shi akan auren hushe haushi dayayi da noor din ta.. sallamar bayin tayi kafin tace masa dama ina neman ka. Yace ko zamu je site dina ne tace ah'a... ba wani magana mai tsayi zan maka ba,tasani sarai yaji cewa za sake renewing auren nashi amma sai bata maimaita masa ba,aranta bawai bata son auren ya dawwama ba ne amma ita so take ta gasa shi sosai dan ko a mafarki bata so ya sake tunanin zai jefa rayuwar bahiyya a wani matsala tunda tasan nan gaba wani auren iyayen nasa zasu masa ...sai tace angel banji kace komai ba, kar kaga nayi maka shiru kadauka ko zaka rike min yata a kyauta..she is not a comodity da zaka aure ta yadda kake so...to me auren nan naka is invalid ...noor ai maza dayawa na nan zasu zo sunemi auren ta a mutunce .. As for u Is eida kaje kasakar min ita ko kajira na tambaye ta muddin tace min bata son auren nan Ba mahaifin ka da kakar ka ba koma waye yakenjin zaisa maka baki wallhy sai na warware shi.. Wani mugun mugun faduwar gaba yaji,a hargitse ya dago ya dube ta da fuskan magiya xaiyi magana ta tsare da da manyan idanun ta tace in kaje ka turo min ita da safe..gudnite Ya mike Muryansa har na rawa Yace ok ..1 secnd bata kara ba ta barshi awajen. Yayi luff Yana kwance rasa inda zaisa kanshi yayi gashi yau kwana uku kenan rabonsa da su hada daki daya da matar san ga haushin rashin zuwan ta date din nacin shi a wuya jiyake kamar zai shake shi.. Babu irin tunanin da baiyi ba..shi ayanzu tsorone yake neman shiga zuciyar sa game da al'amari.. Sam bai gane me suke nufi da shi ba Da safe yana idar da sallah plain black vest ne ajikin shi ta dan matse shi wandon sa itama na sport fari da vertical strips kanshi yayi rough kadan alaman bai combing ba ..gym ya wuce dan yayi warmin jikin shi,to tsaban tunanin yadda xai shawo kan bahiyya ta amsa tana son auren agaban jahan shi yake damun sa ayanzu Gashi yana fushin dishing dinsa d tayi taki zuwa date din wani abu aransa na bashi cewa dagan gan tayi..tsaki yaja ya aje karfen dayake juyawa,hannun shi ya mika ya zaro sweat towel fari yana goge zufan daya fetso ajikin sa . Fitowar sa ke da wuya yaji muryan ta na famar tashi tana ta dariya,abun da bai taba ji ba kenan Da sauri ya leka dagasaman benen sai ya ganta,normal ruga da skirt ne ajikin ta suna tagiya da kaaamil zasu bar site din Allah kadai hirar da sukeyi but dariya sukeyi sosai kamar basu san da shi ba Siririn Tsaki ya kufce masa baima san dalili ba,a gugurguje ya bita kan step ya shiga bin bayan su Kan ya shigo,har sun zauna maid tana serving dinsu hot coffe...wani racing game kaamil ya kunna musu suka fara bugawa .. Khal tsaban sun bashi mamaki bai karaso ciki ba sanda ya tsaya kare masu kallo Haushi yaji aransa dayaga kamar bata da wani dalilin da zata masa abunda tayi masa jiya and she looks ko ajikin ta kamar batasan tayi wani abu ba...,dan kadan yayi furzan iska cike da kasaita da taurin kai..ya zame ya bar wajen ko 3minu baiyi ba saiga maids ta shigo musu....ranki shi dade his higness khaldun yana neman ki da gaggawa...murmushi kaaamil ya sakr mata ,dan duk suna lura dashi amma suka dauke idanun su...yace cupcake zakije? ..tayi rau da idanun ta tace ah a..ni bazanje ba Tabe baki yayi Ya sallame maid,dacewan ace ma khal din tana zuwa.Share tashan sa sukayi suka cigaba da game dinsu har aunt murja ta zo ta same su,suka gaisa. After like 20minuts wajen ya kaure da surutu,game din ya mugun dauke musu hankali amma a zucuyar ta tana tunanin mijin nata Aikuwa sake aje nunfashin ta batayi ba sai gashi ya shigo babu ko sallama ransa a mugun bace..daya dake sanda dukann su suka juya suna kallon sa Kaamil ma gaishe sa baima amsa ba ..wani mugun harara ya watsa mata tayi saurin hade rai ta lau da kanta Get up...ya fada da shakurarren voice.. .aunt murja sai ta dan tsakure ta,nan ta mike a sadade ta isa bakin door din,wani finciko hannu ta yayi suka bace awajen bai sake ta ba sanda ya shige da ita dakin sa ya kulle kofar.. A masife take kallon shi"Hannun ta take kokarin fizgewa anashi amma kamar ma batayin komai dan karfin su ma baiyi kusan daya ba. Ni ka sake ni...pls let go Ina wasa dake ne? Ya dan daka mata tsawa ranshi
Chapter 110 · 0% Book details