Sashe 5
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba Kokawar jawo ni Ma Ta shigayi cikin dauriya dukan mu muna ihun neman ceto Ahaka Har ta ci nasaran kwace ni a hannun sa muka fado kasa tare A hargitse muka mike ai tun kafin Ahumaggan yace zai zago na tura junnut kan hanya nikuma na kwaso maganin da muka debo a hannu na,..wani uban Gudu muke cikin jeji da dukan karfin da Allah ya bamu. Gudu yaki ci yaki karewa dan Bamu san munyi nisan kiwo ba sai da hakan ya faru damu tsaga ciyawa kawai mukeyi babu iyaka... Ayayin da shima Ahumaggahn ya haukace yana biye da mu aguje da dukan karfin sa ko kiran yan uwnsa baiyi ba.... Bana so mu rabu da junnut dan haka muka rike hannu muna falfalawa back to back.. Gashi Idon mu duk ya rufe da tsoro,sao A Chan bakin wani tsaunin itace daya fado kasa junnut bata lura ba tayi tuntube ta fadi gashi ta gaji sosai sai haki take..nayi kokarin janta amma wani Ihu tayi cikin radadin zafi wanda ya tabbatar min da cewa taji mumunnan ciwo a kafarta A tsorace na zube gaban ta nayi kokarin dagata don jin sautin tahowar Ahummagan ya gama jefamu cikin rudani. Agurguce dai na tallafo ta Da kyar na dago muka tsaya tana dingishi kafarta na dama har ya farke ya na zubar jini sosai. Munajin sautin iska alaman Ahumaggan na gaf da mu anan tsananin tsoro ya sa muka sake juna Ita Junnut tayi gabas ni kuma nayi arewa.. Gudu kawai muke yi har na samu na tsira sai na buya bayan bishiyar kuka ina ta haki ina neman dai daita hankali na. Anan Nakai wasu mintuna goma banga wullowar Ahumaggan ba haka ma banga junnut ba Atake naji Kirji na ya buga,kaina yayi mummunan sara,gashi ina so na kwalla ma junnut kira amma ina tsoron dada jefa mu cikin fitina. Nasan tabbas sauran Ahumaggan ma suna nan,kuma muddin suka ji muryan mace zasu fito dukan su kuma nasan bazamu taba tsira ba. Cikin jarumta na fito a sadade ina neman junnut ajejin. Tafiya nake ina duban gaba da baya,har na naci kusan rabin awa banganta ba,sai da nakai chan ciki wajen gonar masarar sarki modibbo kafin naji dafff an dafa ni. A hargitse na waiwayo dan tsoro sai kuwa muka hade ido da junnut tana tsaye kamar kungi hawaye taff kan fuskan ta. Wani irin daskararren Kallo muka tsaya yiwa juna cikin mu babu wanda ya iya furta komai Gaba daya Ji nayi Jiki na ya dau sanyi dan Yanayin da take kallo na sam bangane mashi ba... idanun ta sunyi jajir kuma ta riko rigarta ta cukuikuyo shi da dukan hannayen ta tana nuna alaman tsana ma yanayin da take ciki. Innalihhihi wa inna ilahi rajiun Murya na tsananin na rawa nace" Junnuut...jun.. Ai Bata bari na karasa ba tasake min Kukan ta mai dauke da tsumayi wanda ya dakatar da ni. Atake naji wasu mahaukatan hawayen sun bulbulo min Cikin firgici Nace meye ne? Nan ta riko ni tana mai dada fashewa da kuka Tana boye fuskanta ajiki na,kai kawai take girgizawa Anan Zuciya ta tuni ta bani cewa wani abu mummuna ya faru da ita dan haka nima nabu jira na fashe da azabbaben kuka mai fitar da sautin ciwon daya fi nata ciwon zafi Wani Kankkame juna mukayi cikin dajin muna kuka sosai da kuma dukan zuciyar mu,..batare da ta furta min ba Na gane cewa Ahumaggan nan ya cimma burin sa ne akan budurcin junnut. Da kyar muka rarrashe kanmu Mukayi zaman mu cikin tsakiyar gonan bamu damu da komai ba muna tsananin jimami. Cikin disashiyar sautin kuka Nace shikenan yau na shiga uku junnut,..maganganu nake yi cikin rudani da Har zan fara bada kaina laifin j awo ta cikin wannan matsala Sai naji tace"kar kice haka bahiyya,ai duk abunda zanyi akan Abbu tamkar nayi ma mahaifina na ne.. Ni Damuwata yanzu ummah surbajo da cikar buri na! Kinsan yadda nake so nayi rayuwata ko?wallhy Ina matukar son na Zama mace a duniyan nan bahiyya bazan iya jure duk wani abunda zai ranani da hakan ba! Yau idan akaji abunda ya same ni nasan ko ummah surbajo bazata kula ni ba bare adanka ni wajen dangin mahaifiya ta. Sai bata sake cewa komi ba dan Kuka mai ban tausayi junnut take yi cikin zafin rai da rikicewa Gashi ba karamin zafi jikin ta yake mata ba,nikaina kukan nake yi kuma nasan dauriya junnut take yi ayayin da take min maganan ayanzu. Damuwa sai ta mamaye zuciya ta,don Bayan tinanin hukunci da za'ayi ma junnut awajen sarki Babban fargaba shine burin ta na rayuwa da take sa shi a ran zai fara daga gobe. Sai naji kawai banyi mata adalci musanman da naji cikin kukan nata kamar tafi damuwa da Cewa za'a shafe ta a zuria ayi cursing dinta inda ko umma surbajo bazata so ta hada hanya da ita ba bare taje birni ta cimma burin tan. Dan a al'adan yace muddin aka shafe ka babu wanda zai sake so ya hada zuria dakai,don gani za'ayi kamar kaidin ba alheri bane kuma darajar ka ta gushe kenan har abada Tausayin ta sai ya kamani sosai Junnut tayi min hallaci sosai,yau ta dauki qaddarar biyo ni neman magani ma mahaifi na rayuwar ta kuma ya shiga matsalan da bansan mafitar sa ba. Tunani nakeyi sosai Dan haka kawai nake jin cewa dole nima nayi mata hallacin da zai dawo mata da martaban rayuwar ta cikin gaggawa. Nace junnut idan zaki iya kawai muje gida yanzu mu samu abbu mu fada masa nasan shi zai nema mana mafita ko?. Junnut Gyada kanta kawai tayi ta kwantar da kanta akan kafada ta cikin jimami dan kwata kwata rasa budurcin nata bai wani dara ta chan chan kamar tunanin cikar burin ta ba sai tace. Bahiyyah ki rufa min asiri mana kinji?... Sai na dan langwafo na kalle ta,dan ban fahimce ta ba ...mikewa tayi ta zauna tare da riko hannu na.. Tace Kinsan a duniya bani da kamar ki ko Bahiyya!Toh dan Allah Ki rufa min asiri mu binne maganan nan tsakani na dake bana so kowa yaji. Cikin mamaki na ware ido ,a marairaice tace Kinga tunda naji ciwo jini na bina ai ummah surbajo bazata gane abunda nake ciki ba har sai na bar garin nan gobe ko?.toj Dan Allah bahiyya kimin wannan Alfarman, hawaye na zubo mata sai ta marairaice min sosai gwanin tausayi Nikuwa Cike da zakuwa Nace zan yi miki komai a duniyan nan junnut ..ina dai baki so kowa yasani ne? Amma toh baki tsoro aljanu su tona mana asiri.. Ahumaggan nan zai fada ma aljanun su cewa yayi fyade ma budurwa,a gidan sarki kuma zasu jira mu har kwana uku idan bamu kai kanmu ba kinsan zaki iya mutuwa ko? Da sauri Tace eh..nasani Anma ai basu sanin ko wacece akayi ma fyaden ba har sai takai kanta ko? Ba tare da wani shakka ba Nace eh Wani ajiyan ziciya Junnut ta sauke cikin sanyin tace "bahiyyah,Shiyasa nake so ki taimakeni...sai kuma tayi shiru alaman kalman ya mata nauyi abaki Nace inajin ki junnut.. Nan ma sai ta kafe ni da ido tayi shiru abun ta Da kyar sanda na dinga takura ta da cewa dare na dada yi mana ajejin,gashi tashin hankali ya gama mamaye zuciyar mu kafin ta shirya furta min. Anan junnut ta nemi alfarma ta tana cewa "Domin cikar burin rayuwa na nake rokon ki da ki sadaukar min da darajar ki wajen sarki Cikin kukan da bansan dashi ba Ta dada ruko hannu na tace "Ina nufin kice masa kece akayi miki fyaden bani ba.. Zu je tare amma ke zaki dauki laifin Inyaso koda an wanzar da hukunci akanki sai mu hada hannu mu dauko abbu mu kaishi chan inda ummah surbajo zata koma kasar nigeria sai ayi jinyar sa da dukiyata. Cike da mamaki Nace junnut?kinsan me kike cewa kuwa Tsaye ta mike tana dingishi,dan tun kafin na kawo korafi na tace toh nidai wallahy zan kashe kaina,daga yau muyi bankwanan a duniya bahiyya...kinsani Idan bazan cika buri na ba gwara na mutu. Nima tashi nayi a rikice nakai mata dan karamin mari a fuska,a zuciye nace zaki kashe kanki baki da hankali ne... Cikin kukan bakim ciki ta sulale ta tsuguna gaba na tana mai tana kafafu na a kaskance tace bahiyya dan Allah ki taimake ni,wallhy nayi miki Alkawari zan dawo miki bazan rabu dake ba ...zamu yi rayuwar mu mai tsafta ni dake har abada..Alkawari ne. Wani irin Tausayin ta ne naji ya shige ni sosai domin Wani Kuka mai shiga rai takeyi ayayin da nima na fashe da kukan na tsuguna na rungumo ta jiki na muka dunkule munayo tare.. Cikin tsananin son naga na yaye mata damuwar ta nace mata na Amince zan dauki alhakin yin mata haka.. Sai dai sharadi na shine wannan maganan ya kasance wata babban SIRRI l mai girma a tsakanin mu wanda ko abbu bana son yasan dashi. Junnut ta dada rungume ni tana kuka tana min godiya Tare da min Alkwarin duk dukiyar ta na wajen ummah surbajo zai dawo na jinyar abbu na. Haka na dauka wannan kayan alkwarin makaina Ni sam Bandamu da wani curses din da za'ayi min gobe agidan sarki ba. Sannan a tunanina na yaranta na bana kawo cewa akwai abunda zai tsare ni wajen nema mahaifina gamsashen lapya,wani tsafi da aljanu duk gani nake sun yi kadan su kara da ikon Allah.. Iya kaci ne ace inhar da ummah surbajo zamu zauna a inda zata koma gobe a birni to zan iya rabuwa da abbu na. Toh Wannan shine kadai babban abun daya yake damu na yanzu.. Ta ya zan fara ma abbu bayanin haka?gashi Bantaba boye mishi komai ba sai yau da nake shirin zan boye mishi sirri na da kawata junnut.. Shin ko akwai abun da ya fi dadi a duniya kamar kasan kana da iyayen ka a raye koda kuwa baku tare?. Follow @surayyahms _toh Fans ina jiran amsa First page Dedicated to members of bwa TOH YA KUKA GANI?ACIGABA?LET UR COMENTS SPEAK OUT FOR NEXT POST. #SURAYYAHMS [9/29, 2:42 PM] 0mer Farouk: _* AHUMAGGAH _A nigerian historical fiction_ _*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_