← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 173

Sashe 46

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba. Cikin wannan yanayi tuni idanun ta suka sauya kala suka cicciko batare data san dalilin hakan ba. Ganin zata iya jawo Attention din mutane akansu da rawan da jikin ta ya shigayi yasa ya riko hannun ta da tray din ya tayata saukewa kan table din. Sit down".. ya furta mata kamar wanda baison kowa ya ji muryan sa ko ya gane shi. Tana zama tana dada duban sa Involuntarily sautin muryan ya furta...you .. yoouu ? Sai ya dada matsowa a hankali izuwa cute suprise face dinta yana binta da wani irin yasashiyar kallon bege mai shiga rai "shushhhhhhsss....yace yana sa yatsa akan half wet pink labbansa.. Wani idon ta tsura masa da alaman bata san tayi haka ba,..komawa yayi da baya kadan sai ya zare cap din ya bar suman kanshi tare da jingina kai yana kallon ta direct. . Har zatayi magana kenan sai taji yace "Serve! Tace ok,cike da sanyin kamala ta langwasa Kamar wata marainiya Ta shiga bude buden plates din tana aje murafen su agefe. Guda biyu ne that means nata da nashi yayi oder,haka ya sata suka fara cin abincin tare,sunayi suna kallon juna bawanda yace uffan duk dama da kyar zuciyan ta ya amince mata da cewa ba mafarki take yi ba Tana ganin su Yasmin suna lekowa amma ta dan kashe musu ido Alaman kar su damu da ita. Ruwa ta zuba a cup ta mika masa ya karba kamar wanda zaisha amma sai ya kawo setin bakin ta ya shiga bata ruwan slowly tana karba Sau biyu ta kurba ya sauke cup din ya bita da wani close look yana duban yanayin ta,how are you?..bakinsa ya furta ya kuma kure ta da sanyin kallo alaman yana mai sauraron ta Spoon din ta fara ajiyewa Ta danyi shiru ta sauke kanta kasa,zuciya tuni ya mule cikin tunanin duk abubuwan da suka same ta tun bayan rabuwar ta dashi har yau, cahn saiga hawaye suna zubowa dakan su... Bata san meyasa ba amma haka kawai take jin shaukin gaya masa duk wani halin data ke ciki,musamman akan sadat da subaya. Sai dai kuma shaidan yana ta kokarin dasa mata tsoro da fargaban halayen maza Gani take kamar ayanzu she have learn alot of halin dan adam a wajen sadat toh tayaya khaldun din ma zai fahimce ta. Shikuwa Ya dau lokaci yana kallon ta a hakan,daya lura da halin da take ciki tun kafin ta sauke boyayyen ajiyan zuciya ya mike tsaye baice komai ba ya tashi yafita ya barta, a hujajan sai ta mike ta shiga biyo sa abaya.. Tafiya suke kamar basu san juna ba har ya ja ta suka nufi wani waje wanda baida nisa da shop din sosai Irin bishiyoyin nan masu dauke da cool down chairs abakin wani pondpool ya zauna,..a kusa da shi tadan dofane cikin sanyi murya tace khaldun sir,ure here, ure welcome. Sai ya dan juyo ya hade rai ya harare ta....nifa lpya ta kalau...ta fada slowly tana neman sauke kan ta kasa Yace shine kike min kuka?Did you have any problem?Ko dodo kika ga ni?gani zan cinye ki ko...ya tabe baki yayi kwafa Wani sassanyar hawayen ne ya sake sauko mata ta dan girgiza kai...bata ce uffan ba sai ya juyo U dont want to read..makarantar ya ishe ki? Tace ah a ...am just Suprise? Tace ehmm... Dan ciza labba yayi ayangace ya mike tsaye " Ok...i am going zo muce chan rudaddun idanun ta dago tana binsa da kallo bugun kirjin ta na karuwa Ya mika mata hands,ba bata lokaci ta riko hannun san, tin kafin tayi wani magana ya shiga janta suna tafiya har suka kai gaban wata bakar mota da alaman nashi ne Zai shiga driver seat sai ya mata alaman ta bude seat din baya tana budewa taga manyan packages din daya taho dasu tun daga shoping mall yace take them out.. Batayi musu ba ta shiga fitarwa har ta gama,dasu a hannun ta karaso daidai ta inda yake ta jikin motar dan kadan ya sauke glasss yana kallon ta wani 3mint silence wajen ya dauka kafin yace to Ayi karatu lpya.. Sai Tayi masa shiru fuskan ta adan daure.. Dan share ta yayi ya kau da kai kamar baisan tanayi ba, Yana kuwa kunna car din ta fashe masa da wani kuka mai sanyi da rauni kamar wata mai jinnu sai ta juya zata tafi abunta. Kashe motar yayi atake ya Wani lumshe idon sa a bazata cikin saurin da baisan da shi ba ya sauko. Irin kukan da baka san dalilin san nan ba takeyi ta daura tafukan hannun ta duka akan fuskan ta har goshin ta yana shirin taro zufa. Sai ya dakata ya zuba hannayen sa a aljihu,yadda ya tsime yana kallon ta kallo daya ya ishe ka ka gane kukan nata na azabtar da shi har baisan ya zaiyi ba Ranshi adan bace ya mata nuni da hanya Just Go.. Kije aikin ki ni bana son shegen iyeyi Dan kadan ta turo baki a shagwabe ta dan kalle sa da grey watery eyes din ta batace mashi uffan ba,sai ta juya kamar zata bar mashi shoping parks din amma kuma sai ta dawo cikin sanyin jiki ta dauka tana dan share fuskanta da tafin hannun ta so innocent kamar karamar yarinya yar 4yrs,tuni yarintar ta ya matikar tafiya da imanin sa Yanayin nata na mugun kafa tarihi aransa Tana kara one step Bata hankara ba taji ya cakumo arm din ta cikin zafin nama,"where did u think ure going like this?..ya dan dage mata giran. ..Wai kukan me kikeyi?tell ne now,ya dan daga muryan sa kamar wanda dama sunyi alkawari ne bazata yi kuka ba har abada Ita kuwa tuni taji ta kara rudewa cikin waswasi,gaba daya bata san meyasa data gansa a hakan kukan yake zuwa mata dayawa ba Dan fincike hannu ta take kokarin yi batare da ta sani ba Sai taji Ya jawo ta jikin sa daf,not too close ya mata rumfa da kirjin sa ya dan saukar da kansa cikin idanun ta yasa nashi suna maida ma juna kallo mai saurin bayyana tsananin soyayya da tausayi .. "Wani ajiyan zuciya ne ya kufce mata yasa hannun sa ahankali yana share tears dake neman tare masa gani abunda ke idanun ta... "Sarkin karatu da Dafe dafe,toh ai Bani nace ki sa kanki schl ko kiyi aikin ba,.har kin gaji ne ko,did you want to go home? Ki fada min.. Ta girgiza kai tace ah'a. Baice uffan ba yana binta da Kallon nitsuwa a hankali ya sa finger daya ya lakato hawayen ta ya nuna mata, why tears? Mmmm Bata amsa ba,ya karkace lips dinsa da mafin sanyin sautin sa ya firta "i hate it. Wannan sautin murya nashi tasan yau datana da karfin sha'awa bazata iya cewa bata ji w ani abu ba! Wani Lumshe ido tayi a slow bata bude ba,Wani feeling din yarrr taji yabi jikin ta Sai data sauke boyayyen nishi kafin ta samu nitsuwa. Sai ta shagwabe fuska ta turo masa baki tana langwame masa wuya ta kasa cewa komai,yasan bazai iya jira yayi ta kallon ta haka ba duk dama yau yaga mugun kokarin sa akanta,,a hankali ya zare jikin sa anata batare da ya sake hade ido da ita ba ya sake ta, .. .yana juyawa zai koma motan nasa itama sai ta daure ta cije ta dauki kayan ta wuce gaba,sai kowa yayi hanyar sa batare da sun sake tanka ma juna ba Wani yanayi mai azabtarwa ke cin su arai dukan su, koda ya shiga motar shima zama kawai yayi ya kasa sa key bare ya tayar Ita kuwa Tafiya take da kayan a hannu kamar wanda ruwa ya kwaso ta tana sauke silent tears dan sosai Take jin kamar shine zai iya kawo mata karshen matsalan ta a rayuwa but she just dint know how and what to do to let him know all her problems. Dai dai wajen da suka zauna kan chair na gindin bishiyar ta kafe da ido da alamu khaldun din ne yake mata gizo,har ta isa wajen ta zauna shiru bata sani ba hankalin ta gaba daya kamar baya jikin ta,har ya iso ta bayan ta daff da ita bata ma sani ba. Wani uban tagumi ta rafka da duka hannyen ta biyu,within two secnds hawaye suka shiga saukowa This time bai wani jira ba,hannun sa ya sa yay tapping kafadan ta bai damu da yadda ta farga ta juyo arazane ba ya balla mata harara Zata kara sautin yace,nidai kimin shiru,bazan sake zuwa ba....i can see you hate seeing anyone Wasu tears din ne suka gangaro mata masu shegen yawa jikin ta har na neman daukar kyarrma,idon ta a rufe gam gam kuma cikin sautin kuka mai tada hankali tace... pls dont go...nidai kar ka tafi.. .i dont want you to go....dan Allah . Sai yyi shiruu Fuskan sa bai cika nuna yanayin da yake ciki ba amma gaba daya ya rasa yadda zaiyi da azaban kukan nata a kirjin sa deep inside him yake jin its hurts him badly..wani irin feelings mai karfi yake ji akanta.,ji yake kamar chan kasan zuciyan sa son ta ya shiga garari wajen nuna masa bakar tsana ma hawayen bahiyya. Mika hannu kawai yayi ya kwashe kayan da hannu daya ya kuma Jawo ta da dayan har gaban motar sa ya bude ya dura ta suka bar wajen.. Su biyu a motar kowa yayi shiru basu ko kallon juna Tafiya sukayi mai dan nisa,tun da suka kama hanya kanta akasa bata lura da isowar su ba sanda hannun shi ya sauka anata mistakely. Anan ta dago ahakan ma da sauri suka kau dakai shiya fara sauka sannan ya zago ya bude mata ta fito Its just past 10 na safe wajen is still cool iskan bishiyoyi na ratsa ko ina,wani karamin estate ne mai kama da lodge dan yawanci dama travellers ne da taurist suka fi booking wajen. Har cikin gidan ya mata jagora,yana tafiya tana binsa abaya kamar wacce bata da laka. Yanzu kukan da zafin dake damun zuciyar ta duk ya washe,yanzu kuma wani uban tsoro ne ya fara shigo mata Its seems like they are alone banda karnuka da mai gadi bata sake ganin kowa ba.
Chapter 46 · 0% Book details