← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 173

Sashe 2

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ _In honour of my 2nd version,am not dead if ure in this world,my blood, my flesh. *ZAYNAB TEMI TOPE ADENIYI ABUBAKAR LAWAL.*._ _Bismillahirrahmanirrahim._ -The horn of Africa Misalin karfe 6 na safe ne,Juyi nake ina kikkiftawa salon kwace baccin gajiyar da har yanzu yake bibiyan idanu na. "Yau ma Daga inda nafi kwanciya a chan dungun daki na tattaro karfi na duka nayi mika don na watseke,da kyar na waro idanuna dan kuwa Bibbiyu nake gani har wani jiri ke deba na,hakan kuwa bai hana ni daddagewa na zauna tsam ina muzurai ba sai dai duk da haka idanuna sunyi dishi dishi kamar wata mai kallon gajimare. sanda na dauki mintuna uku da hannun dama na ina yarfe su kafin suka dawo min normal sai dai har yanzu Basu nuna min abbu na ba. 'Wani irin faduwar gaba ne ya taso min"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na furta acikin zuciya na.Wani mugun fargaba ne naji ya rufe ni atake,a hujajan na mike tsaye ina dube dube dan bansan sanda sanyin sautin murya na ya fidda sautin sunan sa ba'..cike da damuwa na fito ina cewa ABBUH...! ...jiya cikin dare Abbu ne akwance kusa dani kamar gawar da yaki kabarin sa. Dan Daga ni har shi bansan ya akayi safiyan yau ta riske mu ba. duba shi na shigayi sai dai ina dora kafata bakin dakin daya raba jingar karar dake tsakar gida sai na hango rayawar karan masara har an sakaye kofar bayi dashi alama nacewa da mutum aciki yana zagaye. 'Bayin nadan bi da ido na dan wani lokaci domin na tabbatar ko shine aciki,bayan kamar minti biyu nayi ajiyan zuciyan tare da sauke boyayyen nishi nan na juya na koma cikin dakin dana fito. "...Yagaggen Tabarman kajinjinin dabinon da muke kwana akai na dora hannu na akai na jawo shi batare da na nade ba na karkade duk kasan dake kai na fito dashi waje. A jikin dangar kara daya suturce mana asirin jimammiyar muhallin mu na tsaya,sanda na zare kararen da suka rage mana na hura wuta sannan na yarfa tabarman akai na juyo tsakar gida. Daga nan A Gaban wata dakilalliyar ramin murhu nayi tsugune,Hura wuta na shiga yi da gaske domin sanyin safiyar mu ta sha banban dana kowa a yankin mu. "Sunana Bahiyyah Ahmadu Alba. ni Bansan daga ina muka fito ba bare nace na san asalin mu amma yanzu haka a wata katafaren yankin jeji mai tsananin sanyi da duhun itacuwa muke zaune nida iyaye na da jinsin zuriar wasu fulani wanda su ba bakake ba kuma su ba farare ba. Nan din Yanki ne Daya tsaga tsinin kahon nahiyar africa,Kenan mu ba acikin wata kasa muke ba. A cikin kasashen afurka da suke zageye damu kuwa sun hada da ethiopia,somalia,djoubuti da cibiyar bahohin ruwa guda biyu wato quardafui da somalian sea,sai kasar kenya dake gudu maso gabas. Shiyasa ma idan anka duba yankin mu da kyau sai inaga kamar muna cikin wani tsauni ne a chan Cikin dajin daya ya raba gulf of eden da kuma bahar maliyar(red sea). Tsawon shekaru na a duniya na dauka acikin wannan yanki aka haife ni,Sai dai nasha mamaki sosai a lokacin da ammu wato mahaifiya ta tazo gaban ta na mutuwa. Anan ta take sanar da ni cewa ita cikakkiyar yar kasar somalia ce. A somalia jinsin yare biyu ne,ko ka kasance arab ko dan somali. Toh Ammu na balarabiya ce tar dan cemin tayi bata ma jin yaren su na somali a duk dama larabci da somalin suka dai ne yaren da ake yi a kasar.. Tace min Abbuh wato mahaifina kuma dan yankin ethopia ne gaba da baya,A wajen cin kasuwanci a boader chan mahadan su dake wajen kasar djibouti ta hadu dashi. soyayya mai tsananin karfi yayi sanadiyar auren su. Daga nan A takaice Iyaye na sukayi zaman aure a kasar ethiopia wato garin mahaifina sai dai Rayuwa na shudewa dangi suna ta mutuwa,kafin a hankara rayuwar iyaye na ta koma garin mogadishu wato state capital na kasar somalia nan inda aka haifeni. Anan ma Ko shekara guda banyi ba Koluluwar Yunwa Da jarabar tsiyan talauci irin na kasar somalia ya sa akayi wata karamar yakin daya rabamu da kowa da komai namu a duniya. Dan haka muka yi hijira muka bar somalia,dan tun ina Jaririya hijirar ya kawo mu wannan dajin inda muka hadu da jinsin zuriar fataken fulani mu kayi zaunen mu a cikin su muna rayuwa. Gashi har Yau shekara ta goma sha hudu bamu bar nan ba. A shekaran daya gabata ciwon daji yayi sanadiyar mutuwar Ammuh kuma tun mutuwar ammun Abbu ya kamo da mummun ciwon zuciya wanda nikaina na rasa gane wata irin tsaninin so da shakuwa ne ke tsakanin su,my dad cannot live without my mum shakuwar su tasha banban da irin shakuwar masoyan zamanin yanzu. A da chan,Allah ya bama abbu na baiwar magance cututtuka da sanin warakan ciwo ko da sanadiyar mutum ne koko na aljani. Abbu na yana da baiwar shiga jeji yayi farauta kuma ya tsinko ganyayyaki,itacuwa da saiwa kala kala,yana kuma iya sarrafa su ta yadda yake so domin a samu sauki,da waraka akan kusan ko wani irin cuta. Tsawon shekaru yana taimakawa amma yau Sai gashi har Abbu na yakasa gano itace ko wani ganyen da zai masa maganin Ciwon son ammu na dake damun zuciyar sa. Mutuwar Ammuh kamar faduwar wata danga ce agare mu gashi abbu yasa abun aransa sosai fiye ma dani. "Sai Gaba daya ya dena fita ko ina,tun lokacin ya tsayar da duk wani harkan sa ta siyar da magani gashi har ciwon zuciyar yayi tsanani ya kama shi ta inda bazai ma ji maganin gargajiya akan lokaci ba. A Yanzu Buri na na sami taikamakon da zai wadatar dani har na kaishi ganin likitar bature a chan yankin kasar egypts inda nake karatu dan naga suma suna shigowa kasuwanci a yankin mu kuma bamu da wani nisa sosai. Ko da nayi yunkuri sai naga Jikin abbu yaki sam,A kullum tsoro na kar abbu shima ya mutu ya barni dan bansan ina zanje ba. .......... A haka Ina zaune gaban murhun,idanuna sun yi lufu lufu da hayakin danyen karar dake ci Da kyar wutar murhun ta kama tana ci bal bal tashi nayi na jawo kwaryan dake gefe na,don kafin nan na dan tsaftace wajen danake zaune,sai kawai na dora sauran gasashen namar rago da muka ci jiya domin shima ya turara musamu na sawa a bakin salati. Asali dai Bamu cika cin abincin da ya shafi ganye ko itacuwa ba,,dani da iyaye na gaba daya We are not much of vegetarians. Dana zo daga baya ma na san asalin tarihin ammu sai na dena bata lokaci na wajen nazarin yanayin cin abincin mu. Ammuh tace min a chan somalia haka nan suka saba iyaye da kakanni,suna nomar turmeric wato(kurkurm) curry da kuma corriander,abincin su kuma daga namar rago, namar shanu kaza da tinkiya, Sai basmati rice. Hakan ya dada bayyana min tasirin halin talaucin da kasar somaliar take ciki,amma tunda muka dawo nan alhamdullhi zamu ce,duk dama munsaban amma Abbu wata rana yakan sa muci zallan yayan itacuwa ko ganyen alaihu,tufa,cerely,gurji,karas,ibini da dabino da kuma ganyen lettuce. Mukuma mukan bashi hadin kai ne A matsayin sa na masanin kariyar cuta sai muke biye mashi mafi akasarin lokuta muke sauya abinci. "Ina zaune gaban murhun,Daga baya na na Ji karar sautin takun sa,mikewa nayi na juyo ta inda zan ganshi da kyau as usuall tsaye yake cikin dakakkiyar rigar jumfa wacce take suluk babu shape,rigar ya dan tsuufa amma fari ne tass wandon kuma kalar kasa ne,he is looking neat babu lifo,don a duk dama ni karama ce bai hanani tsaftace abbu na ba. Tsaye yayi hannun sa rike da buta ya tsura min hasken fararen idanun shi yana kakalo murmushi kamar bashi bane mai sani kukan tausayin kaina ko wani dare. Domin son yaga nayi murmushi sai ya yabani da kalman larabci yana mai cewa Saiiqah...yah noori...! Nikuwa Yadda ya furta kalaman nan naga kuma yana kallo na yana murmushi sai ya sani naji wani tsananin kaunar sa da tausayin sa ya tsuma ni...a take na mike tsaye ina kallon shi Hannun shi naga ya ware duka biyu ya buda min,ni kaina Bansan sanda na taho kusa da shi na rungume sa ba..gam ya dada matso ni tamlar wanda zai maidani cikin sa"wani sanyin hawaye mai shiga rai shi ya kufce min ayayin dana kankame sa nima jiki na dik yayi weak a haka na furta ABBUH ban karasa ba....sai naji ya shafa kai na,A hankali na kuma furta ABBUH NA, HAMMAM dina, Wano Dada kankame ni yayi jikin sa sai rawa yake alaman shi kadai yasan meya keji ajikin nasa,a haka ya dago fuska ta zuwa nashi yana min murmushi mai taba zuciya da sa sanyin rai... Yace yata shin waya koya miki kalmar "hammam" bacin nasan ke baki iya larabci ba?..hakika kalman tayi min dadi...bayan matata zaynah,a duniya ke kadaice zaki iya gayamin wannan kalma mai dadi kuma naji dadin shi. Share guntun hawaye na nayi ina murmushi sai Na sunkuyar da kaina na seconds biyu.. Cikin farin cikin da bansan na meye bane na furta. "Abbu,ranar a kasuwar kofar gidan modibbo naji wani balabaren egypts yana fada ma sarki 'hammam" shikuma sarki yaji dadi sosai har ya masa kyautar azurfa. Shine Sai na tambaye shi ma'anan kalman shine yake cemin kalma ce ta girma kuma ba'a cewa kowa hammam sai mutumin da ya cika abun Alfahari,abun koyi,abun kauna kuma abun tinkaho.. Hannun shi na kama fiska ta na sake wasu irin disasshun murmushi: nace Abbbu..kai ne abun alfahari na Allah ya baka lpya abbu na. Dan Shiru abbu yayi,Sai Na lura tsaban farincikin abun da nace yanzun yasa abbu na baice komai ba. Nidai karamar ajiyan zuciya nayi Hannun shi dake famar sacewa da tsaninin sanyin dake busowa na riko cikin idonshi na furta ...wai shin yaushe zaka warke muje jeji ne,..?abbu na Ina so na raka ka deban magani kaga kwana biyu kudin mu duk sun kare..ko ka mance lokacin da kake dauko ni akafada muna tsintar ganyen mu?ko dan ammu ta barmu shikenan kai zaka dena
Chapter 2 · 0% Book details