← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 173

Sashe 52

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ _Bismillahirrahmanirrahim._ _Shafin masoya masu min coments grp grp,nagode sosai Allah ya bar zumunci.Pls idan mutum yamin magana a pc yaga nadan jima ban amsa ba yayi hakuri bancika hawa whatsp haka kawai bane sai zanyi posting,Sannan idan zaka min magana akan abune kaga ya dau lokaci ban duba ba pls go ahead n say evrything and leave it there wannan nasan ko a offline zan iya bi na amsa, thank you -errabund cikin baccin kanta yayi hitting ta gane cewa baccin ya dauke tane a bazata a gabansa a cikin wannan yanayin. A mugun firgice ta farka tareda sake kowakwar tare towel din dake kirjin ta ta matso sa dam dam kamar wanda ake shirin kwace mata. Wani rutse ido tayi tana mugun jin fargaba da bugun zuciya,duk dama bata ganshi ba but ranta ya bata cewa ya farka kuma ya kalle ta a hakan Sam bata ji dadi ba,tana mikewa direct ta shiga inda ta shanya rigar ta witou any waste of time tamaida dukan kayan jikin ta,nan ta kunna tap ta wanke ido da baki Tafito dai dai wayan ta na ringing. Daukawa tayi a gurguje bata ma lura da yadda book din ke kife akan bed din ba,ta sa wayar akunne ta shiga magana da dija. Its just 40minutes to lecture time Tace gani nan zuwa,a dan hanzarce ta rarumo side purse din ta har yanzu bata dena tunanin ina ya shiga ba. Duba da yadda take fama da kunyan sa aranta she is not sure ko tana bukatar ganin sa ayanzun sai ta fara tunanin ta bari ko sai anjima inta dawo Tunanin daya sha mata kai kenan ayayin da ta ke dan daga pillows din tana jan bed sheets tana kintsawa, Da murmushi ta dauki book din zata ajiye tanayi tana tuno da hirar su na jiya,har zata rufe kenan sai charaf idanun ta ya sauka akan bold handwriting dinsa. A nitse ta karance abun da ya rubuta "Wani Manne book din tayi da kirjin ta game da lumshe ido kwakwlata na aikin amincewa da sakon daya bar ma ta. "So he is gone,...wani numfashi taja kafin ta bude idanun ta.... haushin missing dinsa da murnan moments din da suka yi spending harda kunyar data keji duka suka hadu suka sauya mata yanayi. Just as she was about to drop the book wayan ta yayi kara kuma,tana dauka wani murya wanda bata sanda shi ba yace tafito a kaita school yana waje . Da wayan a kunnen ta ta matso har jikin window bata lokaci ta duba ta windown taga wani driver ne a tsaye jikin wata deep blue classic jeep wrangler.. Tasan bazai wuce Khaldun yasa shi ba,bataji wani dar dar ba ta taho ya bude mata ta shiga har cikin school ya ajiye ta yayi gaba abunsa. Ta danyi latti gashi tana bukatar sauya kaya,dan haka ta wuce hostel bata shiga class ba sai da ake je break aka dawo Toh bayan sun gama suka hade da su dija Da murna mai dauke da cunkusashen tsumayin missing dinsa dake damun ta ta rungume su Kowa na tambayar ta ina taje da wancen mutumin kuma waye shi Dariya kawai take,bata ce uffan ba sai ta shiga tambayar su nasu hidimon anan ta san cewa maman dijan ma ta tafi kasuwan ci ne acan kasar sudan maybe zata iya dawowa soon Wasa wasa bahiyya ta shiga wani yanayin mugun kewa da tunanin saood,daga jiya zuwa yau bata iya tabuka komai akan lokaci duk moment din da sukayi take ta famar maimaitawa a kwakwlta Dija ce ta gaji da ganin day dream din nata sai ta tsiye ta cikin wasa,da dare suna kwance shine take gaya musu sunan gayen khaldun sa'ood ,shine elder bro din big sis dinta amma takasa cewa itama bro din ta direct,tana tayi musu kwana har suka kamo kan tashan zancen Jasmine dake dariya sosai take teasing din ta da wasa cewar ta kaga masu bro din bigsis tare kuma kuka kwana?toh ai sai abamu details.. Tashi tayi agabn su kamar munafuka ta runtse ido tana murmushi.. Dariya suke yi Cikin wasa har suka Ci nasaran sata ta gaya musu asalin sirrin zuciyar ta akan sa. Tace tun ranan da tagansa taji ya kwanta mata arai sosai,acewar ta ba so bane kai tsaye burge ta daya ke yi ne ya cusa mata son shi... Dukan su sun shagala da yadda take suffan tashi so very real and natural Abun ya matukar kama zuciyar su Sai dai tce musu basu furta ma juna komai ba kuma bata san ko shima yana jin yadda take ji aranta ba Hakan ya sa su dija suka dan shiga nazari A tunanin dija tace mata bisa ga labarin data bayar ita taga alaman shima he feels the same Jasmine tace a'a,kar tayi gaggawan rike hakan Tace bahi...akan yi mistaking so sabida wata rana yakan yi kama da tausayi kuma yakanyi kama da abokantaka. hakan yasa tabata shawaran cewa ta kula da son shi aranta har sai nashin yafi haka bayyana mata sosai kafin ta yanke hukunci.. Bahiyya tahi dadin shawaran nasu Suma kuma Sunyi farincikin sanin cewa bahiyyar su is in love sabida dama kullum hidiman sadaat na mugun sanya musu tausayin ta aransu. Gashi yadda ta gwada saood cikin labarin ta tasa sukaji sun amince da shi kuma suke ta zumudin ganin sa Kamar yadda tace wata rana tasan zai sake zuwa. Haka hirar ta kare kowa ya cigaba da hidiman rayuwar sa Bangaren khaldun kuwa isar sa gidan sa ya samu babu kowa and his doors were half locked alaman kaamil bai tafi ba tun a jiyan Amma daya shiga baigansa ba sai yake tambayar gurds yaushe kaamil din ya bar gidan Sai gurd yace masa yau da safe..,daga nan dakin sa ya nufa ya fada bathrum ruwan shower mai sanyin gaske ya sake ma jikin shi yana kwalala ya nitsar da zuciyar sa waje guda tamkar wanda yake bada zuciyar hakurin kar ta tunzura shi ya aikata abun da baida niyya which is kiran bahiyya a waya.. Thats why he neva wanted to keep her contact gashi yanzu zuciyan sa har ta fara tunzira shi. He want to convince himself that she wll be ok.. Gani yake kamar in ta tashi bata gansa ba zatayi ta kuka A Yanzu Gaba daya fiskan tane yake masa guzo sai yaji baida filin jin sakat a rayuwar sa. Haka ya karaci sha'anin sa yana shafa cream yana tunanin ta He dint bother to even think of yadda ya tafi jiyan ya bar su kaamil anan din kosau daya Bayan yan shafe shafen da yayi ya dora jallabiya light brown a jikin sa Sallah kawai yayi ya cire kafin nan ya shiga duba abubuwan da zai duba 20minute yana danne danne nan ya fara tunin hada ma cikin sa simple coffe,white singlet da deep blue jean ya fito da shi ya kunne coffe maker ya shiga hadawa Shikuwa kaamil dama yace a sanar da shi dawowar khal gidan,so ana fada masa kuwa ya diro with immidiete effect Khal ganin sa kawai yayi a bazata Sallama sukayi exchnging,kaamil sai ya cije ya dan daure fuska yana nema makansa wajen zama,ba yabo ba fallasa yace So u back? Sai yayi kamar bai gane fushi yake ba Yace ehmm yana dada sipping coffe dinsa very camly ya lura da yadda kaamil ya hade rai cikin masifa sai ya dauke kansa Kasan makoshi yace Ashe baka tafi?im suprised.. "Ohhh bro pls..dama ka gudu ka barmu ne sabida mu tafi Sannan sai ka dawo?....Seriously kaamil yayi wannan tambayar Amma Cikin kasalallen yanayi khal ya amsa.. Yace kaaaaamil,mu kuma?kai ka cika shirme... i was talking about you just now sai kaga ma kazo.. Yace ohh khal cut the crap naki naji wannan boye boyen naka,kasan katafi ka barmu and its,me and junnut...ur fiance... Wai meyasa baka kira ka fada mana inda kakw ba,wallahy bata ji dadi kuma ni Akan ta nake magana Sa'ood Wani hade ransa yayi share sa Yace brother pls dan Allah ka dena azabtar da yar mutane dan ko ni na ji haushin abun She tot u left bcos of her,baka ganin yadda take kallon ka inka namin ne wllhy tasan ba haka kake ba. Karamar yarinya ce fa,tana bukatar kulawar ka Just little attention Wani banza da shi khal yayi yana ta shan coffen sa tamkar bada shi ake yi ba Kaamil shima bai fasa ba bambami yake yana ta surutu non stop Why isnt it like this She is your godamm wife to tun kan yace be din yaji ance.. Stop kaamil,ya ishe ka...Ta turo ka tazo ka buge ni ne? Kaamil zai sake magana yace not another word frm you I dint say i want any girl ..to name zan takura ma rayuwa ta akan ta? Baki a bude kaamil yace But Ure engaged. Khal yace ok...Engaged not my wife right?toh Ka kama hanya ka tafi in baka da abun da zaka fada min But brother ure wrong .,wallhy baka kyautawa ma junnut,pls dont act that way with her jiya da ka shanya mu ko bacci batayi ba She left this house very upset and depressd. Wani xaro ido uayo yace So?its my job then to make anyone happy.. Kaamil yace No,but she has that right! Ko?,dan kawai ance zan aure ta in future shine take da wani right akaina? Ai gwara ma kaje kayi mata fada ko zata gane cewa akwai banbanci abunda ya faru da abun da ake jira zai faru Kaamil yace Haka ne amma ai abunda zai faru shi ake shirya wa ba abunda ya faru ba.. Kaamil meye bai faru ba?..Isnt it enough that i have accept that marriage proposal Me kake so dani ne? Na rika jan karamar yarinya ajikina kowani lokaci kamar wani shasha sha?..why wont she just face her studies tunda ta amince zata zauna dani a auren alkwari i think bata da matsala akan dole sai mun saba In sabo dani take so sai tawarware alkwarin ta jira sai naganta nace ina son ta,but right now babu wanda zai takurani. Agurin ku ne auren alkawari awajena auren alfarma ne wani shiru kaamil yayi cikin sanyin ajiyan zuciya
Chapter 52 · 0% Book details