← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 173

Sashe 54

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yunkurin tashi Har waje ya rakasa kafin ya dawo gidan zuciyan sa cike da sanyin samun wanda ya fahimce abun dake makele acikiin zuciyar sa musamman akan bahiyyah. Kaaamil cikin nazarin yadda zai taimaka ma dan uwansa yake tuki,...daf da zai bar anguwan ya daga wayar shi dialing number junnut yake amma sam bai shiga ba Where cud she be now?kawai sai ya sha kwana ya nufi apartmtnt din ta direct. Bangaren junnut kuwa tunda ta fita ta bar gidan khal da fushi bata iya komawa gidan ta ba ta tare wajen kawarta hilda She is living in one of the luxurious hotele asalin cikin las vegas,to anan junnuta ta sauke duk abunda ke damun zuciyar ta game da rayuwar ta da khaldun saood Kwata kwata alkwarin da akayi musu shekara guda ne a yanzu amma gaba daya khal ya cunkusa mata zuciya da bakin ciki. Ranar da tazo tayi ta kuka Har ya kaiga ta fada ma hilda dukan abunda ake ciki game da auren nasu Tace ma hilda,tana ganin kamar karya Dilshad khatun sukayi mata akan maganan kama zuciyar sa da sukayi gashi babu abunda take sha wajen sa sai wulkanci. Dan ita har yau bata ga abunda ya sauya ta fannin sa ba Ita ce ma take mamakin yadda zuciyar ta ya kasa bata daman daukan kwakaran mataki akansa. With all his wulakancin amma ahakan wutan kaunar sa ke dada bulbulowa a kirjin ta Jiyan Data kira kaaamil da sassafe ko zata ji ya dawo da yace ah'a hankalin ta ba karamin tashi yayi ba. ko abinci taki ci da kyar hilda ta zaunar da ita tayi mata masifa sosai. Anan take cewa ita data san haka samun kan khaldun yake da wuya da duk abunda aka ca tayi a india ranar da zagewa zatayi tayi But righr now she is even suspecting ko kuskuren ta ne ya jawo abubuwa basu kankama ba? Toh tun suna juya wannan magana awasa har hilda ta tursasa ta akan sukama hanya su nufi kasar india ko za suji meke faruwa Ya da safe Jirgin su na tashi daga gidan ta kuma masu aiko suna ma kaamil bayanin cewa Tun ranar bata dawo gida ba,he left very worried amma daya kira gida baiji ance ta kira ko nan taje ba sai ya yi suspecting tana tare da hilda ne Sukuwa isarsu india cikin dare,saida suka sa aka bi musu kafa aka binciko komai harda amount din kudiin da dilshad take biyan matsafi ta Its much kam amma haka suka hada karfi suka ruba kudin kashi biyu dan ya saueare su da gaggawa Da sassafen kuwa ya kira su,suka taho kamar bai gane ta ba kuwa sanda yasa ta masa bayanin kanta sosai Tace tana so ya duba mata matsalan ta batare daya fada a gidan su ba Ba laifi,ya tambaye ta meke tafe da ita Nan take gaya masa dukan nin matsalan ta harda abunda taki hadiye da suka bata anan din. Wasu tsubace tsubacen shi yayai ya mata hayaki daga bisani yake sanar da ita cewa Sihirin da sukayi yana tafiya daidai amma abunda yasa bazata gane ba shine asalin zuciyar sa'ood aka bata ta hadiye ranar,amma sai ta bari kyakymi yasa tayi jefa dashi kuma tace musu tayin Wannan maganan sosai ya taba zuciyar junnut,tace ashe zuciyar sa aka bani? Kasssshhh tafurta cikin yanayin rashin jin dadi. Cikin marairacewa tace ko zaa sake bani zuciyar nashi? More than anyone today she was so ready taci ko da kashi ne,aganin ta ko da meye aka hada tana ganin yau zata iya hadiyewa Matsafii ya gama buge bugen sa,daga bisani yace mata tayi jinkiri dan ya duba ya gani cewa khaldun din ya furta soyayya akan sunan wata wanda kuma ba ita bace. Dan haka kafin su sake dauko zuciyan sa su bada wata sai wancan yarinyar tafita.. Wani gum taji Tuni idanun Junnut sukayo ruwa, hankalin ta ya tashi sosai,so akwai wata kenan a zuciyar sa? Sai tace amma kwanan nan yafara ko?why not acire ta daga nan tun yanzu ai zaku iya ko? Mutumin yace,ai dama tana nan tun kafin ke,saidai da bai furta ba muka samu daman cire maki zuciyar sa,kedai kinyi wauta mai girma dakika watsar da damar ki Zuciyar sa kam bazai sake fita ba. Tsaban damuwan da ya bayyana kan fuskan ta gaba daya ta kasa maida magana hilda ce ta dawo amsa maganan tana tambayar sa me zasuyi? Yace maganan zuciyan shi kan kawai ta cire rai,amma zai taimaka mata da maganin da zai sassauta duk taurin kansa agaban ta. Nasha ne dana wanka Ba tawani so ba,amma bayadda ta iya haka ta karba Har suka dawo united state babu abunda junnut take sai bakin ciki da jimami.. Musamman cewa da akayi akwai wata ta daban Wanda ba ita bane a rayuwar sa. Har suka dawo gidan hilda bata gane kanta ba Wani baccin dole ta tursarsa kanta zuciyan ta cike da mummunan tsanan yarinyar da khaldun sa'ood yake so a zuciyar sa. Follow #SURAYYAHMS And vote. This shafi is for Maman bappa kawata Madinatul munawwara Nafzagie saffah Deeja ciroma Mom sayeed and noor Mrs mane shukura Durlings na Munerah novel grp Swhrts na taskar billy galadanci Lovers na Zauren littafai Princess nvl grp gidan gayyar mai gaba daya wato Ahumaggah coment grp da surayyhms novel grp And all my beautiful momies and drlings na gidan *Zinne smart* novel group ku na daban ne a zuciya aradu .... _Uhum uhum ashe ban fada wa whtsap cewa jiya wattpad fans sunce zasu siya min lamboghini dan ayi posting full week ba,wani suna da suke kira min wai mrs surry lambo pls kar abarshi ya biyoni kamar yadda official catty ya dawo min official tag "to ku whtsap me zaku siya min?leeme ques..sury ferrari have a lovely night .._ SHARE WITH FRIENDS. AHUMAGGAH _The love triangle_ _A nigerian historical fiction_ *WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
Chapter 54 · 0% Book details